Ticker

6/recent/ticker-posts

Mazubin Kwarya a Cimakar Bahaushe Ta Gargajiya

Article Citation: Aliyu Muhammad Bunza (2019). Mazubin Ƙwarya a Cimakar Bahaushe ta Gargajiya. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 17, No. 2. ISSN 0794-9316

MAZUBIN ƘWARYA[1] A CIMAKAR BAHAUSHE TA GARGAJIYA

By

Aliyu Muhammadu Bunza

Tsakure

Tunanin mutanen duniyar Yau ba zai taɓa ci gaba ba daidai da na jiya. Lokaci ya yi na mu fara tunanin tsirran da muka keɓanta da su a duniyar mutane domin laluba tarihinmu. Tsiron ƙwarya na daga cikin tsirran da suka game duniya. Haka kuma yana daga cikin tsirran da ƙasar Hausa ke limancin bazuwarta a ƙasarta da kuma shugabancin sarrafa shi. Haka kuma a duniyar wannan ƙarni Kasuwar ƙwarya mafi girma a duniya ita ce Kasuwar ƙwarya ta Gummi a jihar Zamfara. Wannan bincike ya ba ni damar hango rawar da ƙwarya ta taka a mazubin Bahaushe. Takardar ta hango wurare ɗari da ƙwarya ta taka rawa a matsayin mazubin Bahaushe. Da wannan sakamako nake ganin anya! Ba a ƙasar Gummi Allah Ya halicci tsiron ƙwarya ba? Masanan Ingila sun tabbatar da cewa a Afirka ta fito. Amerikawa sun ce, ba ta fi shekara dubu goma da zuwa yankinsu ba. A dai ci gaba da gashi tuya sai ran salla.

Gabatarwa

Lokaci ya yi na a fara tunanin adana wasu kayayyakin daɗaɗɗun al’adunmu na gargajiya gabanin guguwar zamani ta salwantar da su. Hasashen Ali Mazrui[2] ga irin turnuƙun da al’adun mutanen Afirka ta duniyar baƙar fata suka shiga ya cancanci a dube shi da idon basira. Al’adunmu nagartattu da sukaratso zamunna masu tsawo, nagartarsu ta soma raunana. Da muka yi taho-mu-gama da baƙi masu saukakkun addinai (Larabawa da Turawa) al’adun suka sake shiga duhu, guguwar addini ta gama da wasu. Ana cikin jinya, huntu uabangijin mai riga (Bature) ya leƙo gadan-gadan da mulkin mallaka aka shiga zaman bawa da mai gida, al’adun masu gida suka murƙushe na bayi. Ba a ko gama jinya ba, cigaban kimiyya da fasahar ƙere-ƙere ya kutso kai, aka sake watsar da wasu al’adunmu, wai sun zaman ƙauyanci. Duk waɗannan zamuna da aka ratsa da ƙwarya aka ratse su, kuma har yanzu tana nan ana yi da ita. Ban ce ba a raunanata ba, amma ta jure wa guguwar juyin-juya hali da ta cigaba da tawaye a gargajiyance. Maƙasudin wannan bincike kakkaɓan gara ga tarihin gwagwarmayar ƙwarya a cimakar gargajiyar Bahaushe.

Iyakokin Nazari

Wannan bincike bai keɓe lokaci ko zamani da zai fara da tuƙewa ba. Dalili kuwa shi ne, binciken ya hankalta kawai ga irin gurbin da mazubin ƙwarya yake da ga cimakar Bahaushe. Binciken zai kalli mazubin ƙwarya kawai wato ƙwaryar da za a zuba wani abu ciki ko ɗaukar wani abu ciki da sunan zuba shi aka yi, ko kwaso shi aka yi a ciki. Haka kuma, binciken ya taƙaita ga abin da ya shafi cimaka kawai. Duk wani abu da bai shafi cimakar Bahaushe ba, ba za a ba shi muhimmin bagire a binciken ba. Duk abin da aka ce cimaka ne (abinci) ga Bahaushe za a kalli rawar da mazubin ƙwarya ya taka wajen kyautata hulɗa da shi ta hanyar sarrafa shi ne, cin sa, kyautata shi ko cin moriyarsa.

Fashin Baƙin Matashiya

Matashiyar wannan bincike tana ɗauke da fitilun kalmomi biyar da ke buƙatar a waiwaye su domin su buɗe hanyar shiga fashin baƙi gadan-gadan. Zakaran farko daga cikin kalmomin shi ne ‘Mazubi’. A fassarar Ƙamusun Hausa da ya zo bayanin ƙwarya, kalmar mazubi ya fara gabatarwa.[3] Mazubi shi ne abin zuba wani abu, ko abin ɗebo abin da aka zuba cikin wani abu, domin a zuba cikin wani abu. A gargajiyar Bahaushe, akwai mazubai daban-daban, kamar:

1.            Taiki: mazubin tsaba da nau’o’in abinci (da fata ake yin sa)

2.            Salka: mazubin ruwa ga fatake (da fata ake yin sa)

3.            Kwando: mazubin taki da abinci, wake ko kifi (itace ƙanana)

4.            Mangala: mazubin taki, ƙasa ko abinci (kaba)

5.            Tandu: mazubin mai (fata)

6.            Tandu ƙarami: mazubin kwalli (fata)

7.            Randa: mazubin ruwa (yumɓu)

8.            Tukunya: mazubin ruwa (yumɓu)

9.            Kantu: mazubin gishiri (kaba)

10.        Rariya: matatar abinci/ƙullu (kaba)

11.        Akushi: mazubin abinci (itace)

12.        Baakaa: mazubin daddawa da shanya abinci (akwai na itace da kaba)

13.        Burgami: mazubin abinci (fata)

14.        Zabira: mazubin asaken wanzamai (fata)

15.        Gafaka: mazubin Alƙur’ani da littattafai (fata)

16.        Alabai/fartamani: mazubin kuɗi da madubi (fata)

17.        Jaka: ma’ajin kayayyaki na sutura da wasu (fata)

18.        Waagaa: mazubin kayayyaki daban-daban (itace)

19.        Faifai: mazubin alewa da ƙananan kaya a yi talla (kaba)

20.        Malfa: mazubin ƙananan abinci; rogo, nama, waina da sauransu (kaba)

Bahaushe da ya ji an ambaci mazubi waɗannan abubuwa ashirin za su iya zuwa a ransa gami da “ƙwarya”. To, wannan bincike “ƙwarya” kaɗai zai duba a matsayin mazubi, ko ita kuwa ga abin da ya shafi abinci mai rai ko matacce.[4]

ƙwarya ita ce kalma ta biyu, a nan, ba duma ake son a nazarci tsironta da nomanta ba. Abin da ƙwarya za ta kamo sun haɗa da duk nau’o’in ƙwarya da ake amfani da su a hidimar abinci. Cimaka, abincin Bahaushe na gargajiya wanda ya ƙunshi tsaba, da ruwa-ruwa, da mabunƙura ƙasa, da na gashi da dahuwa, da sauran ƙwalama. Daga cikin waɗannan da waninsu wanda aka tabbatar da cewa Bahaushe ke da abinsa kuma na gargajiyarsa ne, wato ya gaji abin kaka da kakanni shi za a yi nazari a wannan ɗan bincike.

Dabarun Bincike

A koyaushe mu ɗaliban nazarin al’adun mazauna duniyar baƙar fata, musamman Hausawa kukan da muke shi ne, ba a yi nagartattun bincike a kan wasu muhimman al’adunmu ba. Rashin samun muhimman ayyuka shi ke sa a koyaushe za a ga a fagagen bincike da yawa sabon harsashin bincike za a kafa. Tabbas, za a kalato ‘yan ayyukan da suka samu da aka yi kan ƙwarya na al’adun Hausawa. Babban abin da aka ba ƙarfi shi ne yawon rangandi ga wuraren da ake noma ƙwarya da sana’arta. Haka kuma, an shiga tattaunawa da ma’abota ƙwarya a ƙauyuka da ‘yan gutsattsarin adabin baka da ake iya tsinta a bakunansu da suka shafi ƙwarya. Kai- da- kawo cikin ƙamusoshin Hausa dole ne domin a ga yadda fashin baƙin wasu daga cikin kayan bincike yake. Wannan bincike ya bai wa duniyar intanet muhimmanci domin ƙyallaro duniyar da ƙwarya ta shiga da rawarta a bagiren cimaka. Domin samun ingantattun hujjoji, ya zama dole rangadin bincike ya kasance ƙasar Gummi ta jihar Zamfara da ƙauyukanta wuraren da noman ƙwarya ya yanke cibi. A ganin wannan bincike, ziyartar Kasuwar ƙwarya ta Gummi tilas ne, domin ita ce kasuwar ƙwarya mafi girma a duniyar zamaninmu ta ƙarni na ashirin da ɗaya.[5]

Ra’ayin Bincike

A tunanin wannan bincike, guguwar zamani da juyin-juya halin rayuwa bai razana ƙwarya ba. A tarihance, ƙwarya ba ta taɓa tagomashi da shiga duniyar mutane ba kamar wannan ƙarni, ƙarni na ashirin da ɗaya. Barazanar da ta samu na kishiyoyi ba su ƙirguwa, amma duk da haka ƙwarya ba ta kasance cikin al’adu masu haɗari ba.[6] A kan ƙudurina na ganin an taskace ƙwarya a fagen cimakar Bahaushe tun zamani bai gama da ita ba, na ɗora bincike a kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Da rashin kira, karen bebe ka ɓata”.[7] Duk wata kishiya da zamani ya yi wa ƙwarya a fagen girki da cimakar Bahaushe daga ƙwarya aka tsince shi aka sarrafa shi a zamanance. In haka ne kuwa, matuƙar ba a daina waiwaya ba, ba a rasa hango abin da aka manta a baya ba. Ashe ke nan, komai nisan da bebe ya yi ga karensa, da yana da bakin kiransa, ba su ɓace wa juna ba, muddin ba mu yi watsi da bincike ba, hikimomin ƙwarya da hidimominta ba za su salwanta a al’adunmu na gargajiya ba.

Mazubin Ƙwarya A Cimakar Hausawa

Aikin mazubin ƙwarya a cimakarmu ya fara tun daga lokacin da muka ɗebo irin shuka a ƙwarya muka shuka, da lokacin da muka girbe shi muka fara sarrafa shi zuwa adana shi, da gyaransa, da cin sa. A warwarar ƙunshiyar wannan bincike, za mu shifiɗa shi a faifan nazari kamar haka:

v    Mazubi a duniyar Bahaushe

v    Mazubi a shukar Bahaushe da gyara shi

v    Mazubin ƙwarya a matsayin abinci

v    ƙwarya mazubin awon abinci

v    Mazubi a tuwo da miya

v    Mazubi a ruwa-ruwan abincin Bahaushe

v    Mazubi a abincin ƙwalama

v    Dangantakar mazubin ƙwarya da rayuwar Bahaushe

v    Mazubin ƙwarya da sauran mazubin zamaninsa

v    Tasirin mazubin ƙwarya da na ƙarninmu

v    Mazubin ƙwarya a yau

Mazubi A Duniyar Bahaushe

Duniyar da Bahaushe ya rayu cikinta ta ratso zamunna na cigaban ɗan Adam, da wayewar kansa, da bunƙasar ababen rayuwarsa daban-daban. A tarihin duniyar mutane, an yi zamanin ƙanƙarewar duniya wanda ba a zaton wani tsiro ko halitta ya rayu a ciki.[8]An yi ruwan ɗufana da ya rage ‘yan iri na mutane da sauran halittu.[9] Da yake akwai mutane a lokacin, dole da abubuwan da suke mazubi da shi da cin abincinsu da abin shansu. Zamunna biyu da duniya ta shiga ciki na sarrafa duwatsu (tsohon yayi da sabon yayi), watau “Old Stone Age” da “New Stone Age”, babu alamar an sarrafa duwatsu zuwa wani mazubi na abinci ko adana wani abu.[10] Haka kuma, ba a ruwaito an yi amfani da dutsen wajen sassaƙa ba, bale a ce akwai yiyuwar samun akushi da makamantansu. A Zamanin Cin Tama/Samuwar ƙarfe kamar yadda masana suka kira shi (watau, Iron Age a Ingilishi), to ba mamaki a ce a lokacin aka fara samun “ƙwaryar maƙera” ta jibge kayan aikin cin tama.[11] Ba abin mamaki ba ne a ce, lokacin aka fara samun sassaƙa da mazubin abinci na itace. A tarihance, bayan ƙanƙarewar duniya an samu sarari aka samu manyan tekuna da gulabe da tabkuna da suka ba ƙasa damar fitar da tsirrai da muke da su. A nawa tunanin, bayan ƙanƙarewar duniya, ko Ruwan ɗufana, abin da ya biyo baya shi ne tsibiri a saman tuddai jefi-jefi da tsirrai za su samu damar fita.[12] A cikin wannan yanayi ne aka samu tsiron duma (ƙwarya). ƙwaryar ita ce hanya ta farko da ɗan Adam ya fara samun mazubi mai sauƙi domin shan ruwa da hidimomin abinci. Za mu iya cewa, ga alama, da ƙwarya mutanen farko suka fara amfani.

Mazubi A Shukar Bahaushe Da Gyara Shi

Bayan da Buwayayyen Sarki ya ƙago ɗan Adam a tunanin Musulmai abinci aka fara gitta masa gabanin komai.[13] Ga namu hasashe na ɗaliban al’ada, ruwa ne farkon abinci. Duk yadda za a sha ruwa, in yi na kare, in a ɗebo da hannu, tunanin mazubi zai biyo bayansa, domin sauƙaƙa al’amari. Ban yi kuskure ba idan na ce, ruwa ne mazubin farko da ya shiga ƙwaryar Bahaushe. Galibin abincin ɗan Adam da ruwa ake sarrafa shi.[14]

Babu shakka, tsirrai da ake morewa da su a matsayin abinci, ba ɗan Adam ya ƙago su ba, taras da su ya yi an ƙago masa su. Yayin da ya fara wayewa, ya samu dabarar shuka abinsa, ƙwarya ya fara sawa gaba. Idan aka samu jinkirin saukar damina, Bahaushe kan ce; “Har yanzu tsabarmu (irinmu) na ƙwarya”, wanda ya nuna da ita ake shuka a matsayin mazubin irin. Irin ƙwaryar da ake shuka da ita, ita ake cewa ‘kwacciya’, wasu su ce ‘ƙoƙo’. Wannan shi ne asalin salon maganar da ke cewa; “ɗan ƙoƙo cike da tsaba batsa-batsa.”[15] Idan aka girbe abinci aka yanke aka ɗaure, da ƙwarya za a yi roron wanda ya kaririye, haka ma dangin gyaɗa da wake, da ƙwarya ake roronsu da kwasarsu. Kasancewar ƙwarya mazubi na abin da ake roro ya haifar da zancen hikima da ke cewa: “Gaba-gaba ƙwaryar roro.” A cikin wasannin raha na Hausa an ce, wai ɗankama ya je shukar hatsi da ƙwaryarsa ta shuka. Da aka zuba masa iri cikin ƙwarya, in ya ɗebo irin da hannu zai saka tausa (ramin shuka) sai ya ce: “ɗammaha!” In ya ɗebo ya saka a bakinsa sai ya ce: “dahir!” Hujjar kula a nan ita ce, cikin ƙwarya ɗankama ya saka irinsa.

Idan an gama hidimar shuka abinci za a sa wa ido har sai ranar da ya nuna a je a girbo a kawo gida don a more masa. Cikin gwagwarmayar mayar da tsaba/hatsi mataccen abinci, idan an gama sussuka da daka shi, akwai ‘surfa’ da za a yi da ƙwaryar ruwa gefeta yayyafa wa tsabar. Akwai ‘shiƙa’ wanda ba ya yiyuwa sai da ƙwarya biyu, ɗaya na zuba wa ɗaya ana ɗaga ta sama. Akwai ‘bakace’ da za a yi bayan surfa wanda da ƙwarya ake yi, a fitar da dusa waje ɗaya, ƙwayar hatsi waje ɗaya. Bayan bakace, akwai ‘rairaya’ na fitar da tsakuwa a tsaba tun ba a surfa ba. Akwai kuma rairayar da ake ce wa ‘riigaa’ wadda za a fitar da tsaki da gari daban-daban. Daga shuka zuwa haɗa mataccen abincin da Bahaushe za ci, ƙwarya ita ce mazubi ga tsabar iri ta shuka, da roron abincin da ya faɗi ƙasa; ita ce mazubin tsabar da aka sussuke; da ita za a yi shiƙa; ita ke rairaya; ita ke bakacen fitar da ƙwaya da kono; da ita ake gyaran gari a wajen yin tankaɗe da rairaya, ko bayan an kashe abincin akwai buƙatarta. ƙwarya babbar maganaɗiso ce daga shuka abinci zuwa cire shi.

Mazubin Ƙwarya A Matsayin Abinci

Mamaye duk wani mazubin abinci da ƙwarya ta yi a wajen Bahaushe ya sa, ba a jin amon kowane irin mazubi in ba itaba. Kai tsaye, ƙwarya na wakiltar abinci idan Bahaushe ya ce:

  1. “Muna ƙwarya” ko
  2. ƙwarya gabanmu” ko
  3. “A gwamatso ƙwarya” ko
  4. “A sa ƙwarya gaba” ko
  5. “Bai taɓa mayar da ƙwaryarsa ba” ko
  6. ƙwarya ta bi ƙwarya” ko kuma
  7. ƙwarya ta gamu da masu jira”

A cikin dukkan waɗannan kalamai, ‘ƙwarya’ abinci take wakilta, don me? Domin Bahaushe bai san wani mazubin abinci ba face ƙwarya. A cikin fitattun karin magana, ƙwarya ita ce mazubin mataccen tuwon da ke jiran ma’aikata. Sa natsuwa ka dubi waɗannan:

  1. Hannu baka hannu ƙwarya/akushi
  2. Cin tuwon maza zube ban ƙwarya

Asalin karin maganan farko, “Hannu baka hannu a ƙwarya”, bayan da fasahar sassaƙa ta samu aka sauya shi zuwa “Hannu baka hannu akushi”.[16] Akushi da baya ya zo, ƙwarya ta fi shi tarihi. “cin tuwon maza zube ban ƙwarya” nuni ne zuwa ga matsayin ƙwarya na mazubin tuwo ga Bahaushe. “Zube ban ƙwarya” fassara biyu yake ɗauka; (a) A yi abu ratata kara zube ba tsayi ba tsaitsayawa. (b) A cinye abinci irin cin kwaɗayi, cin takaici, kamar dai zubewa kawai akai yi aka mayar da ƙwaryar tuwo ga wanda ya zo da ita (wannan bayani shi ake son a tabbatar a wannan bincike). A halin yanzu, cikin ƙwarya ake samun igushi da ƙuli, kuma a yi wa dabbobi abinci daga cikinta. ƙwarya dai ta zama komai da ruwanki.

Ƙwarya Mazubin Awon Abinci

Rayayyen abinci da mazubin ƙwarya ake awonsa. Bayyanar ƙwarya a ƙasar Hausa Mahdi mai dogon zamani. Idan ana Bahaushen lissafi, gomiyya goma suna biyu take da su, walau goma sau goma, ana ce da ita ɗari ko ƙwarya ɗaya. Faɗan ƙwarya a matsayin ɗari (100), Bahaushe a can da yana da ‘yan ƙananan ƙore da yake awo da su wanda guda goma sau goma su ba da babbar ƙwarya ɗaya. Ko su ba da adadin ƙwarya ɗaya a mazubin da ake buƙata.[17] Ga dukkan alama, wajen ‘yan fataken goro aka samu adadin ɗari (100) a matsayin ƙwarya ɗaya. Can Gwanja da goro ke zuwa ƙasar Hausa ba su da ƙwarya sai dai su sako goro cikin ganyayyakinsa ko ganyayyakin wasu itace a ƙunso shi ƙunshi-ƙunshi, a ɗaɗɗaure da igiya.[18]ƙaramin huhun yakan ɗauki ƙwara ɗari da ‘yan kai, idan aka juye su ga ƙaramar ƙwarya su cika ta. Haka kuma, ƙaramar ƙwarya biyar ke masakin gero, dawa, shinkafa, maiwa, ɗaya. Da ƙwarya da masaki da su ake awon abincin da zai cika buhu, taiki, mangala da kwando. Duk wurin awon abinci dangin hatsi da ake sayarwa idan ya shiga kasuwa a “ma’auna” ake kai shi. Ma’auna ita ce wurin awo, kuma suna ne na masu aikin, su kuwa da ƙwarya suke awon kowane rayayyen abinci na tsaba irin su gero, dawa, malle, acca, maiwa, shinkafa, wake, da sababbi irin su alkama da masara. A awo, akwai kwacciya, ƙwarya, da masaki. Da ƙwarya da hatsin da Bahaushe ke ci tare suka yi zamani, mai binciken tarihin Bahaushe da al’adunsa dole ya kula da wannan.

Mazubin Ƙwarya A Tuwo Da Miya

Ƙwarya a fagen tuwon Bahaushe ita ce jakadiya. Duk da sanin cewa, ba da ita yake dafa tuwonsa ba, amma tuwo ba zai kasance tuwo ba sai da ita. Bahaushe na tuwo da dawa da malle da acca da masara da shinkafa. Waɗannan su ne jagoran tuwon dare ga Bahaushe. Ta fuskar mabunƙara ƙasa, akwai rogo da dankali da gwaza da doya da mankani, waɗannan ana iya dafa su gaya ko a tanada musu miya ko a yi kwaragwado. Wake ya kasance mai fuska biyu, ana sarrafa ɗanyensa da busasshensa. Duk na saka waɗannan ƙarƙashin tuwo, domin in dare ya yi duk abin da aka kawo wa Bahaushe sunansa “kalaci”. To a kalacin Bahaushe, kumbu ne jagora domin cikinsa ake sa tuwo da miya ko kuma duk wani abu da aka tanada na kalaci. Idan aka tuƙa tuwon ko kalacin, da ƙwarya za a kwashe shi. Yadda yake shi ne, da gutsuren ƙwarya mai suna “maaraa” za a ciro tuwo a saka ga “ƙoƙo” mai sunan “ƙoƙon malmala” a mulmule shi sosai a saka cikin ƙwarya a jira ya huce a dinga ciransa ɗaya bayan ɗaya ana saka wa a kumbu ana raba wa masu ci. Wanda ba a cinye ba, za a adana shi cikin ƙwarya, a jira safiya ta waye a zazafa shi a ci. Da kwasar garin tuwo, da kwalfe tuwo, da yin marar tuwo, da cin tuwo, da adana ragowar tuwo har gobe a ci zazahe/ɗumame, da kuyafar da ake sa miya, da ƙoƙon da ake saka ruwa a cikin idan ana kwashe tuwo ana taɓa su don gyara muciya da bakin tukunya, duk ƙwarya ce ke aiki.

Sauye-sauyen abinci da gyare-gyarensa da ake da su na yayin zamani da cigabansa ya shafi kowace al’umma. Abincin da ake ce wa “tuwo” ya keɓanta ga Bahaushe, kuma da hatsi ake sarrafa shi. Irin muhallin da ƙwarya ke da shi cikin hidimomin tuwon Bahaushe wata babbar taskar bincike ce. Na farko, wannan ya tabbatar da cewa, duk wani mazubin da ke ga Bahaushe ƙwarya ce kan gaba. A fagen tuwo, ba ta wa sai dai ƙannai. A tarihi, in dai a ce ta riga hatsi shiga hannun Bahaushe, in ko a ce, tare suka zo ƙasar Hausa.

Mazubin ƘwaryaA Ruwa-Ruwan Abincin Bahaushe

A tsarin sanwar Bahaushe, abinci iri biyu yake da su, daga tuwo sai ruwa-ruwa. Ruwa-ruwa sun haɗa da kunu, fura, maɗi da tunkuɗi. Duk wani dangin abinci ruwa-ruwa shi ne wanda ruwa suka rinjaya ya zamo kashi saba’in (70%) nasa ruwa ne. Ire-irensu duka da ƙwarya ake tanadinsu. Mu fara da kuna na shan gida, da na mai jego, da na sayarwa, idan aka haɗa ruwan zafi cikin ƙwarya ake yinsa. Da ƙwaryar da ake cewa “ƙololo” ake ɗebo ruwan zafi ana zubawa a garin da aka tanada a babbar ƙwarya ana motsawa har sai ya haɗu. Idan ya haɗu da ludayin ƙwarya za a ɗebo shi a saka a ƙaramar kwacciya a sha shi da ludayin ƙwarya. Idan za a yi guzurinsa cikin gorar da ake ce wa “gyanɗama” ake saka shi a rataya a kafaɗa zuwa gona ko jeji/daji ko zango. Fura da tukkuɗi duk a ƙwarya ake tsara su, a ciki ake dama su da ludayi ake shansu. Maɗi da ake haɗawa da ɗunya ko rake a cikin tukunya ake haɗa shi, amma a ƙwarya ake adana shi da shan sa. Bahaushe ba ya da tarihin shan abin shansa ruwa-ruwa da bakinsa irin na dabba ko da hannu irin na biri. Wayewar kansa ta shan abin shansa da ƙwarya da malolo da kwacciya da ludayi da abinsa aka gan shi.

Idan muka ɗan waiwayi tarihin mazaunin ƙwarya ko wuraren da ake samun ta, za mu ga duk a wuraren fadama ne. Wannan ya nuna matsayin ruwa na abincin farko na Bahaushe, a nan aka yi masa alfarmar sama masa abin da zai sha ruwa da ruwa-ruwan abincinsa, watau ƙwarya, wayewar kan amfani da ƙwarya daidai yake da wayewar samun ludayi da ƙananan kwacciya na sauƙaƙa shan ruwa da duk wani abinci madangancinsa. Wannan ma ya isa ya sa mu sake tunanin bitar waɗanne irin wurare ne Hausawan farko suka fara zama? Wane abinci Hausawan farko suka fara sarrafawa? Da waɗanne kayayyaki suka fara sarrafa abincin da tadaninsa da adana shi, da cin sa?

Mazubin Ƙwarya a Abincin Ƙwalama

Mafi yawan abincin ɗan Adam da jarrabe-jarrabe aka samo shi. A wajen Bahaushe, duk wani abincin da ba ya da lokacin cin dole, ba za a yi zaune a yi masa cin tuwo ba, ko a yi masa shan fura ko kunu ba, to, ya zama ƙwalama. Da sassafe karin kumallo ake, da rana lomi in ana gona, in ana gida ƙwalama, da dare kalaci. A wajen Bahaushe ‘yan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe da ake na rana na kowane iri, su ake ce wa ƙwalama. A gidan Bahaushe, an fi cin dambu da rana da ƙosai da waina da rogo da dankali da sauran ‘yan toye-toye. A can da, duk cikin ƙwarya ake sayar da su. Kayan tanɗe-tanɗe irin su maɗi da zuma da alewa da maye-maye[19] da waina duk a ƙwarya ake sayar da su. Zuma da ƙwarya ake yin ganin ta da ƙwarya ake sayar da ita. Soyayyar gyaɗa, da dafaffa, ɗan wake, da akuri, da tsire dafau da gasasshe, duk cikin ƙwarya ake yawo da su a matsayin ƙwalaman rana ga mabuƙata.

Kasancewar ƙwarya mazubin ƙwalamar Bahaushe ya sa muke da ƙwaryar maɗi, ƙwaryar zuma, ƙwaryar dambu, ƙwaryar waina, ƙwaryar ɗan wake, da dai makamantansu.[20] Abubakar Imam ya ƙara tabbatar da wannan batu a cikin wani fitaccen labarin da ya bayar a littafinsa mai take: “Bakatsine Mai Kan ƙwarya”, wani ɗan Alewa ne ya je Caranci cin kasuwa bayan an yi masa dama sai ya jawo “ƙwaryar alewarsa” ya ɗan ɗora kansa ya huta. Cikin haka barci ya sace shi kansa ya nutse cikin alewa, da ya farka ya taso da ƙwaryar gaba ɗaya. Da ƙyar aka agaje shi yara na ta kuwwa, eho! Eho! Ga mai “kan ƙwarya”.[21] Bayyanar ƙwarya a abincin ƙwalama shi ne babban muradina a nan.

A rayuwar Bahaushe ta gargajiya, duk wani abincin ƙwalama da na marmari, ƙwarya ce mazubinsu. Idan wanda ake dafawa ne, dahuwa kaɗai ce ba za a yi da ƙwarya ba, amma da fitar sa tukunya ƙwarya za ta yi masa maraba. Abin lura a nan shi ne, wasu daga cikin kayan ƙwalama ba haɗa su ake ba haka nan Bahaushe ya tarar da su, kamar zuma da ‘ya’yan itace, da ganye, amma duk ƙwarya ce mazubinsu. Babu tabbas na haƙiƙance da su da ƙwarya wa ya riga shiga hannun Bahaushe.

Dangantakar Mazubin Ƙwarya Da Rayuwar Bahaushe

Mazubin ƙwarya ya ratsa zamuna huɗu na rayuwar Bahaushe masu matuƙar muhimmanci ga al’adunsa da wayewar kansa. Zamunnan da ƙwarya ta ratsa su ne:

  1. Gargajiyar farko ta Maguzanci
  2. Zamanin saukakkin addinai Masihanci da Musulunci
  3. Zamanin mulkin mallaka na Turawan Faransi da Ingilishi
  4. Zamanin cigaban zamani da ƙere-ƙere da ƙaƙale-ƙaƙale

Tun gabanin Bahaushe ya sadu da kowace irin al’umma a duniyar mutane yana da harshensa da al’adu irin na lokacinsa kuma da ƙwarya aka taras da shi. Dubarun gyara ta, da kyautata ta a matsayin mazubinsa ga dukkanin nau’o’in abincinsa da su aka taras da shi ba ga wasu ya aro ba. Da saukakkin addinai na Masihanci suka riske shi ta hannun Larabawa da Buzaye da Gobirawa da Arawa da ƙwarya suka riske shi.[22]ɗawainiyar da Bahaushe ke yi da ƙwarya a hidimomin abincisa duk al’adun kyautata rayuwa ne ba su shafi wata fassara da Masihanci ko Musulunci ba, don haka ƙwarya ta zama gani nan, bari nan. Turawan mulkin mallaka ba su zo da wani mazubina abincinsu da zai wa ƙwarya barazana ba; su kuwa Turawa ba su ƙyamaci wani abu na ƙwarya ba, a kan wannan hasashe mulkin mallaka har ya wuce bai taɓi ƙwarya ba, bale ya raunana ta. Zamanin cigaba na ƙere-ƙere ya kasa kashe ƙwarya don haka Bahaushe bai saki ƙwarya ba. Duk waɗannan zamuna huɗu ba su girgiza dangantakar ƙwarya a rayuwar Bahaushe ta gargajiya ba, musamman a matsayin mazubin abincinsa. Zamunnan da ƙwarya ta ratsa a matsayin mazubin abincin Bahaushe ba su rage wa ƙwarya wata daraja ba a tanaje-tanajen sanwa da cin abincinsa ba. Haƙiƙa ƙwarya wani babban madubi ne daga cikin maduban ƙyallaro gargajiyar Bahaushe ta fuskar abincinsa. Dangantakar mazubin ƙwarya da rayuwar Bahaushe irin ta jini da tsoka ce, duk zamanin da mai rai ya ratsa, ba zai sauya wani abu daga cikin jininsa da tsokarsa ba. Haka dukkanin zamunnan da ƙwarya ta ratsaba su rage ta komai ba sai ƙara mata ado da kwalliya da tagomashi.

Mazubin Ƙwarya Da Sauran Mazubin Zamaninsa

Mazubin ƙwarya a wajen Bahaushe shi ne na farko, sauran mazubai da ya ƙago ba su kai ta fice da mamaye duniyar al’adarsa ba. Daga cikin daɗaɗɗun mazubai akwai “akushi” da ake sassaƙowa daga itace. ƙwarya ta riga sassaƙa samun bagire a mazubin Bahaushe, don haka akushi yaƙinsa ya tsaya tsakanin kumbun tuwo da kwatarni.[23] A farfajiyar ƙasar Hausa, yau ƙarni na ashirin da ɗaya, akushi sai labari. Kantu da ake yi da kaba da kwando da ake yi da itace, da mangala da malfa da rariya da baakaa duk da kaba ake yin su, su duka siffofin amfanonin ƙwarya aka kwaikwaya aka ƙago su. Taiki, salka, burgami, zabira, gafaka, fartamani da jaka da fata ake yin su bayan da Bahaushe ya samu fasahar sarrafa fata ta fuskar jima ya ƙago suturarsa ta walki da yaba suka biyo baya. Randa da tukwane da shantali sun samu bayan da manyan daulolinmu suka kafu da ƙafafunsu.

ƙwarya tsiro ce daga cikin tsirran ƙasar Hausa da tun farkon zamaninta ba noma ta ake yi ba riskarta kawai ake yi ta tsiro. Yadda Bahaushe ya tarar da tsirran hatsi da ‘ya’yan itace, haka ya tarar da ita. Ita ce farkon mazubi na ruwa da abincin Bahaushe, sai bayan da ta bayyana tunanin a kama dabba, a cire fata, a cinye nama, a kere fata, a yi sutura ta bayyana. Sarrafa ciyayi da kaba, a tanadi matsuguni, duk bayan an ci an ƙoshi ne, ƙwarya ta gama aikinta. Duk wani mazubi da Bahaushe ya ƙago daga yumɓu tasirin mazubin ƙwarya ne aka kwaikwaya aka yi. Labudda mu ce: “ƙwarya liman ce, wani ba ita ba, mamu.”

Tasirin Mazubin Ƙwarya Dauri Na Ƙarninmu (Ƙarni Na 21)

Shekara ɗari (100) su ne ƙarni, hatta da Amurka da suka tabbata ƙwarya baƙuwa ce sun ce ta yi shekara dubu goma/sha biyar a ƙasarsu. A nan kaɗai za mu ce ƙwarya ta ratso zamunnan cigaban duniya daban-daban, duk wani cigaba, da na haƙiƙa, da na mai ginan rijiya, ya tarar da ƙwarya hannun ɗan Adam. Wanann wata irin makaranta ce ta karatun yadda mazubin ƙwarya ya yi katutu a mazubin abincin mutanen duniya gaba ɗaya. ƙwarya babu duniyar da ba ta ratsaba, babu al’ummar da ba a santa ba, kuma babu wurin da ba ta taka rawa ta mazubi da ma’adani naabinci ba. Tukwanen da mutane ke yi na dafa abinci, sato fasahar suka yi daga ƙirar babbar duma ce irin wadda ake kiɗin duma da kurya da su. ƙananan kwanna na zinari da azurfa da ƙarafa da roba da katako ko yumɓu duk daga zatin ƙwarya aka sato fasahar aka ƙirƙiro su. Cokali na cin abinci na ƙarfe, da kuyafa ta itace, da ɗan wurin ajiye gishiri da kayan miya na zamani, an sato su daga ƙwarya na laudayi babba da ƙarami da ƙoƙon sa gishiri da marar tuwo da ake yi da sakaina. Fasahar bokiti, an aro ta daga ƙwaryar ragaya da ƙwaryar gugar ɗibar ruwa da jigon ban ruwa. Duk abin da wayayyen mutum na ƙarninmu ke amfani da shi wajen ɗawainiyar mazubin abincinsa, idan aka sa natsuwa da idon basira, za a ga tushen sifarsa ko amfaninsa ba zai rasa alaƙa da ƙwarya ba. A gai da ƙwarya, ke dai buwaya.

Mazubin Ƙwarya a Yau

ƙarninmu na yau na ashirin da ɗaya, muna kan matakin ƙoli ko na ƙarshe a cigaban zamani. Ban ce, ba za a yi zamanin da zai ɗara namu cigaba ba, sai dai da wuya. Abubuwan da suka bayyana a yau, ko tsafi da sihiri da siddabaru bai isa ya musanta su ba. Mazubin ƙwarya ya ratsi zamunnan gargajiya da addini da mulkin mallaka da zunzurutun ilmin kimiyyar zamani, tilas zamani ya sa wa ƙwarya ido ta yi yadda ta saba yi, sai dai abubuwan da suka yi mata tarnaƙi sun haɗa da:

  1. Ba ko’ina tsiron ke tsira a ƙasar Hausa ba, don haka ba za ta wadata a yi ɗawainiya da ita ba a ko’ina. Kwannan ƙarfe da na roba a nan suka mamaye ta.
  2. Sai da baya nomanta ya fara bayyana a ƙasar Hausa. Da tun lokacin da aka fara noma hatsi aka fara noman ta da ta mamaye duniyar mutane. Ina manoman ƙwarya za su gwada tsawo da manyan kamfunnan ƙarafa da roba?
  3. Sai da baya aka fara gano wasu amfanoninta na abincin ɗan Adam da dabbobi. Da an daɗe da gano haka, da ko wurin da ba noma ta, ana renon irinta a noma shi.
  4. Yawan mutanen duniya masu cin abinci sun rinjaye ta. A ƙasar Hausa kawai a yau 2019 muna da fiye da mutum miliyan ɗari da hamsin (150,000,000), ina za a noma ƙoren da za su yi muna hidimar abincinmu? To, kun ji wata ƙofa da ba mu da gambun rufe ta.
  5. Waɗanda suka yi imani da aiki da ƙwarya a kowace rana raguwa suke yi. Masana sarrafa ƙwarya da gyara ta, su ma haka. Masu girmama ta, da adana ta zamani ya ƙauyantar da su, ala tilas lokaci ya yi mata barazana. Ya kamata masana al’ada da manazarta Hausa su gaya wa duniya ko bayan tiya akwai wata caca.

Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya himmatu kawai ga mazubin ƙwarya a cimakar Bahaushe. A ɗan ƙwarya-ƙwaryan nazari da aka yi an gano cewa:

  1. Tsiron ƙwarya Mahdi ne mai dogon zamani, da shi , da Bahaushe, ba a san wanda ya riga wani ƙasar Hausa ba.
  2. Tun Bahaushe bai sadu da kowace al’aumma ba a duniya yake tare da ƙwarya, don haka ƙwarya Bahausa ce ga suna da ayyukanta. Ba ni musun kasancewarta Bazamfara.
  3. A rayuwar ɗan Adam, babu abin da ya kai ƙwarya zama kusa da shi domin kasancewarta mazubin abincinsa ta farko a bayan ƙasa. Daga cikin albarkatun tsirran ƙasar Hausa, ƙwarya ta fi kowane kusa ga Bahaushe.
  4. Guguwar zamani na cigaban gaske da na mai ginan rijiya, ta kasa kawar da ƙwarya a kundin tarihin cimakar Bahaushe, domin babu wani nau’in ƙwarya da za a ce ya salwanta gaba ɗaya.
  5. Babu wani mazubi na jiya ko yau da ya kai ƙwarya ɗaukaka a wajen Bahaushe, dalili kuwa shi ne, duk da cigaban zamani na samun kishiyoyin ƙwarya na ƙarfe da roba kai har da zinare da tagulla babu ɗaya daga ciki da ya yi amo cikin adabin baka har yanzu.[24]ƙwarya ce ta mamaye adabin baka; karin magana da zantukan azanci. Hatta da kwalba da ta so ta yi wa gyanɗama barazana, Bahaushe ya kushe ta a karin maganarsa mai cewa: “Bilkiri tusa cikin kwalba”[25]
  6. Garin da duk Hausawa suka sara, ƙwarya ke tabbatar da kasancewarsa Bahaushen gari, matuƙar ba ta samu ba, ba su suka kafa shi ba, masauki aka yi musu da kyakkyawar maraba. Anya! Hausawan asali ba ƙasar Zamfara Allah ya fara ƙago abinsa ba? Ku tambayi ƙwarya.

Shawarwari

  1. Ina ba da shawarar a darussan Hausa, a fito da wasu darussa na karatun tsirrai da itace na abinci da alfarma. Wannan zai taimaka wajen fayyace tsirrai da itacen ƙasar Hausa da amfanoninsu ga rayuwar Bahaushe. Haka kuma, za a ƙara fayyace itace da tsirrai na asali a ƙasarmu baki ɗaya.
  2. Ya zuwa yau, 10/10/2019, ban ci karo da wani aiki da masana Hausa, ko ɗaliban Hausa, ko manazarta Hausa suka yi a kan ƙwarya ba, a gargajinyace. Ina kira ga ɗaliban al’ada, da a samu wani ya yi nagartaccen bincike a matakin MA ko PhD a kan ƙwarya a ƙasar Hausa.
  3. A fara tunanin taskace ayyukan ƙwarya da manomanta a hukumance domin gudun salwantarsu tare da salwantar masu hidima da su. A keɓe wa manoma ƙwarya gawurtaccen tallafin hukuma za a ga mamaki.
  4. Cikin shirye-shiryen da ake yi a gidajen rediyo da talabijin da jaridun Hausa, a samu ɗan lokacin da za a keɓe wa noman ƙwarya ko sana’ar ƙwarya ko masu bincike kan ƙwarya. Yin haka, wani haske ne da zai hana dushewar hasken ƙwarya. Anya! ‘Yan jaridar duniya sun san da kasuwar duniya ta ƙwarya tana garin Gummi?

Naɗewa

Al’ada na salwanta gwargwadon salwantar masu aikata ta suna bugun gaba da gadonta. Ga alamu, bayan bayyanar ƙwarya a duniya, da ta ratsi zamuna da yawa ta ɗan yi rauni musamman zamanin mulkin mallaka, saboda Bature ba ya son ya ga wani abu na hikimar magabata a farfajiyar da yace, ya mallake. Bayan ɗan masassaran da ƙwarya ta yi, Gumawa sun farfaɗo da ita ta fuskar mayar da nomanta sana’a, kuma ta haifar da sana’o’i daban-daban da ko ta suma sukan yayyafa mata ruwa ta ƙara farfaɗowa. A ko’ina Bahaushe yake tare da cimakarsa yake cikin ƙwaryarsa. A irin dogon tarihin da ƙwarya ta ratso a duniyar mutane; a ko’ina aka fi noma ta, da sarrafa ta a ɗawainiya, nan za a nemi tushen tarihinta. Ra’in wannan bincike shi ne, “Da rashin kira karen bebe ya ɓata.” Me zai hana mu je Zamfara mu kira Gumawa (mutanen Gummi) suba mu labarin karenmu wanda ya game karkararsu da haushi kowa ya ji? Muddin ba a je Gummi binciken asalin ƙwarya ba, ba a yi wa binciken ƙwarya na ilmi adalci ba.

Manazarta

Alhassan, H. da wasu (1982) Zaman Hausawa. Lagos. Islamic Publication Bureau, Mushin.

Amiru, M. (1992) “Tasirin Zuwan Turawa a kan Sana’o’in Gargajiya.” Kundin BA, Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bagudo, F. M. (2009) “In Ba Ku Ba ƙasa: Gudummuwar Mata Ga BunƙasaSana’o’i A Sakkwato”. Kundin digiri na biyu.Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato:Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Babagana, A (No Date) “ Calabash Complte.

Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa ɓocabulary. Zaria: NNPC.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nig. Ltd.

Bunza, A. M. (2019) “Muhallin Ƙwarya A Ɗawainiyar Al’adun Gargajiya” Takardar bincike da aka kammala 6/10/2019

Bunza, A. M. (2019) “Ƙwarya A Farfajiyar Adabi Da Al’adun Hausa” Takardar bincike da aka kammala 2/10/2019

CNHN, (1981) Rayuwar Hausawa. Lagos. Thomas Nelson Nigeria, Ltd.

CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Dalijan,B. M.(2012) “Noma da Ginuwar Tattalin Arzikin Hausawa na Gargajiya”.Kundin digiri na biyu.Sakkwato: Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Delziel, J. (1916) Hausa Botanical Vocabulary. London: T. Fisher Unwin

Delziel, J. (1937) The Useful Plants in West Tropical Africa. London: Crown Agent for Overseas Goɓernment and Administration.

Garba, C. Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a ƙasar Hausa. Ibadan: Spectrum Books.

Ibrahim, U.(2011) “Tasirin Haye a Sana’o’in Hausawa na Gargajiya”.Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.

Mann, A., Muhammad, G. and Abubakar, N. U. (2003) Medicinal and Economic Plants of Nupe land. Bida: JUBE-EVANS Books

Mika’il, A. M. (2017) “Kayayyakin aiwatar da sana’ar noma da ƙira da fawa a gargajiyance”. Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.

Muhammadu, Y. (1990) “Sana’ar Aikin Kaba: Amfaninta da Yadda ake Gudanar da Ita a ƙasar Hausa”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.

Muzrui (1986). The Africans: A Triple Heritage. Canad: Little Brown

Rambo, R. A. (2018) “Nazarin Ayyukan Sana’ar Sassaƙa da Fasalolinsu a Rayuwar Hausawa”, kundin PhD, Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa.

Rodney, W. (1982) How Europe Underdeveloped Africa. London: Bogle

Sambo, J. (2016) “Tasirin Zamani a kan Sana’ar Sassaƙa a Garin Sakkwato”, Kundin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo.

Sanda, F. U. (2011) “Gudunmuwar Turawa a kan Wasu Sana’o’in Gargajiya na Matan Hausawa”. Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.

Sani, D. (1986) “Sassaƙa a ƙasar Hausa”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.

Sharifai, B. I. (1990) “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa”. Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.

Tukur, A. (1999) “Kowace ƙwarya da Abokiyar ɓurminta: Wasannin Barkwanci, Ma’anarsa da Asalinsa da Sigoginsa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Al’ummar”. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Turaki, H. (1987) “Sana’ar Ginin Tukane a ƙasar Hausa”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.

Zakirai, A. S. (1986) “Saƙa da Sana’ar Sarrafa Auduga”, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.

(Ba shekara) Gubbaru Kammalallen Tarihin Gobirawa.



[1] Mazubin ƙwarya suna ne da naci karo da shi daga ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Da suka kawo “ƙwarya”suka ce “mazubi”wato sun aro daga ƙamusun Bagery da ya kira shi “Calabash basin”. Abin da nake so in ce a nan, matsayin ƙwarya na mazubin abubuwa daban-daban na abinci da waninsa. A wanann takarda ga “abinci”kawai za a tsaya.

[2]Mazrui (1986). The Africans: A Triple Heritage. Canada: Little Brown & Company.

[3] Abin nufi ana “mazubi” shi ne amfanin ƙwarya na farkon amfanoninta gaba xaya suna rakiyar “zubi” babu wanda ya zarce shi.

[4]Abinci mai rai shi ne abincin da ba a sarrafa zuwa daidai a ci shi ba. Tsabar dawa, maiwa, shinkafa, acca, gero wake duk abinci mai rai ne. Idan aka gyara su aka sarrafa zuwa tuwo ko babu miya sunansa mataccen abinci domin da an ci da ba a ci ba duk an gama da shi sai dai lalacewa.

[5]A ɗan binciken da muka gabatar 2019 a cikin duniyar da muke ciki yau, babu nahiyar da ta kai Zamfara Arewacin Nijeriya noma ƙwarya. Babu ƙasar da ke da kasuwar ƙwarya ita kaxai sai Gummi. ƙoren da ake samu ƙasashen Afirka fatakensu daga Gummi suke samun ƙwarya.

[6]Al’adu wadanda ke cikin hatsari/haxari su ne waxanda ake ganin alamar salwantar su da sassauyawar zamunna. To, ƙwarya ta tsere daga kowane irin haxari domin har yanzu kowace irin ƙwarya ana samu a ƙasar Gummi.

[7]Duk abin da ake tafiya ana waiwayarsa ba za a manta da shi, ba zai ɓata ba.

[8]A lokacinsu ne duniya ta ƙanƙare ta zama ƙanƙara a yanayin ƙanƙara babu wani tsiro ko halitta da za ta rayu.

[9]Suratul Hudu, sura ta 11 aya ta 40.

[10]Zamunna duwatsu duk suna bayani ne kan cigaban da xan Adam ya samu ta hanyar amfani da dutse yakare rayuwarsa, ya farauto abincinsa, ya tanadi wurin da zai shiga.

[11]Akwai ƙwaryar maƙera wadda ake jibge kayan ƙira a ciki. ƙamusoshin Hausa sun bayyana haka.

[12]Jirgin Annabi Nuhu a “Juduwwi”ya tsaya, wurin kuwa tsibiri ne waxanda aka kwaso suka sauka. Bayan da Allah ya jaye ruwa, babu wani lungu na duniyar mutane da ba a samu tsibiri ba, ai shi ne hikimar Bahaushe ta cewa; “Ko Kwara tana da tsibiri.”

[13]Da faxan masana da aka halicci Adam da abincin Aljanna ake ciyar da su, sai da aka ƙaddare su da abin da aka ƙaddara suka baro ta suka zo duniya. Da suka zo duniya da yunwa aka fara jarrabarsu aka gaya musu yadda za su samu abinci.

[14]Bahaushe na cewa, duk abincin da bai gamu da ruwa ba wurin yin sa, dole a tanada masa ruwa wurin cin sa. Mai musun wannan ya tambayi dambu da rogo da dankali.

[15]A yaƙin Basasar Nijeriya da wannan kalami ake amfani wajen rarrabe Bahaushe da wanda ba shi ba. Za a ce, kace: “Dan ƙoƙo cike da tsaba batsatsa.” Da yace; “Dan” ko “Koko” ko “Saba” an gano shi.

[16] Sarrafa itace ana jin lokacinzamunnan ƙarafa ne, wato (Iron Age). ƙwarya kuwa tun gabanin zamunnan duwatsu (Stone Age) take.

[17]Ga tarihi, da hannu aka fara yin mazubi. A ga abin da tafin hannu ɗaya ya ɗiba da wanda tafi biyu idan aka haxe su za su ɗiba. Da haka aka fara gabanin ƙwarya ta zo. To, ba mamaki da tafin hannu aka fara jarraba mazubin ƙwarya har aka gano (100) ne ƙwarya.

[18]Irin ɗaurin da ake yi wa goro na ba Bahaushe mamaki da sha’awa har ya ƙago zancen hikima da ke cewa: “Ya ɗauru kamar huhun goro” ko “In ka kai goro xauruwa…

[19]Maye-maye idan an yi ɓarzon gero a haxa da rama shi ne maye-maye. A Gobirana ce da shi runbace/runɓaye.

[20]Duk abincin ruwa-ruwa cikin ƙwarya ake adana shi. Da an ce “ƙwaryar zuma” kowa ya san abin nufi a Hausa.

[21]A dubi littafin

[22]Gabanin addinin Musulunci, akwai addinin Masihi ingantacce a ƙasar Hausa. An ce Arawa da Gobirawa suka zo da shi. A masarautar Gobir akwai Sarkin Gobir Muhammadu Mai Gicci shi ne Sarkin Gobir na

[23]Akushi harya ƙare zamani bai kore kumbu ba a mazubin tuwon Bahaushe. Kwatarni da ƙasa ake yin sa. Ana yi wa dabbobi wurin shan ruwa da shi.

[24]Da za a ce wa Bahaushe ya kawo karin magana ko kirari ko tatsuniya goma da aka ambaci zinari ko tagulla a ciki da wuya ya kawo goma cikin kwana biyu. Jarraba kace a kawo na ƙwarya ka gani, har da wanda ba a shuka ƙwarya garinsu zai kawo su kai tsaye.

[25]Na tuna da xaya, “Bakin kwalba ka riga ciki xaukar mai.” Ga alama dai yadda Bahaushe ya ƙi Bature, haka nan ya ƙi ‘yan tarkacen da ya zo da su. Duk abin da aka haɗa da tusa akwai alamun ba a son sa.

Degel Journal

The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

Post a Comment

0 Comments