𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualekum mallam ya matasayin mace wadda take yin TIKTOK?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam
warahmatullahi wabarakatuh.
Yin TikTok ba haramun ba ne
kai tsaye, amma hukuncinsa yana dogara da abinda mace take yi da yadda take
bayyana kanta. Idan tana yin abubuwa masu amfani, kamar koyarwa, nasiha ko yaɗa
alkhairi kamar karatuttukan malamanmu na sunnah domin yan'uwa su karu, sannan
ba tare da nuna tsiraicinta ba, ko yin ado domin jan hankalin maza, magana ko
motsin da bai dace da Shari’a ba, ko yaɗa
abubuwan haram ba, to asali ya halatta.
Amma idan TikTok ɗin
ya ƙunshi nuna tsiraici ko siffar jiki,
rawa, kwaikwayo na batsa, jan hankalin maza da gangan, ko yaɗa
abinda Shari’a ta haramta, to wannan baya halatta.
Allah Maɗaukaki
Yace:
وَقُلْ
لِّـلۡمُؤۡمِنٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ اَبۡصَارِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوۡجَهُنَّ
وَلَا يُبۡدِيۡنَ زِيۡنَتَهُنَّ اِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَلۡيَـضۡرِبۡنَ
بِخُمُرِهِنَّ عَلٰى جُيُوۡبِهِنَّ وَلَا يُبۡدِيۡنَ زِيۡنَتَهُنَّ اِلَّا
لِبُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ اٰبَآٮِٕهِنَّ اَوۡ اٰبَآءِ بُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ
اَبۡنَآٮِٕهِنَّ اَوۡ اَبۡنَآءِ بُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ اِخۡوَانِهِنَّ اَوۡ
بَنِىۡۤ اِخۡوَانِهِنَّ اَوۡ بَنِىۡۤ اَخَوٰتِهِنَّ اَوۡ نِسَآٮِٕهِنَّ اَوۡ مَا
مَلَـكَتۡ اَيۡمَانُهُنَّ اَوِ التّٰبِعِيۡنَ غَيۡرِ اُولِى الۡاِرۡبَةِ مِنَ
الرِّجَالِ اَوِ الطِّفۡلِ الَّذِيۡنَ لَمۡ يَظۡهَرُوۡا عَلٰى عَوۡرٰتِ
النِّسَآءِ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِاَرۡجُلِهِنَّ لِيُـعۡلَمَ مَا يُخۡفِيۡنَ مِنۡ
زِيۡنَتِهِنَّ ؕ وَتُوۡبُوۡۤا اِلَى اللّٰهِ جَمِيۡعًا اَيُّهَ الۡمُؤۡمِنُوۡنَ
لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُوۡنَ
"Kuma ka ce wa muminai
mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu,
kuma kada su nuna ƙawarsu face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin
mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan
mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mata, ko matan
ƙungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya
wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai waɗanda.
ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da ƙafafunsu
domin a san abin da suke ɓoyẽwa daga ƙawarsu.
Kuma ku tuba
zuwa ga Allah gaba ɗaya,
ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo". (Surah: An-Noor, Ayat:
31).
Saboda haka, ba TikTok ɗin
kansa ne haram ba, sai dai abinda ake amfani dashi wajen yi ne yake sanya shi
ya zama halal ko haram. Idan mace za ta yi amfani da TikTok, ya kamata ta
kiyaye sa hijabi, mutunci, magana mai kyau, da nisantar duk wani abu da zai jawo
fitina ko lalata tarbiyya. Amma idan ta san cewa ba za ta iya kiyaye waɗannan
ƙa’idojin
ba, ko kuma amfani da TikTok ɗin zai kai ta ga fallasa
jikinta, yin abubuwan da basu dace da Musulunci ba, ko jawo mata fitina, to bai
halatta ta yi amfani dashi ta wannan hanyar ba. Musamman a wannan zamani da ake
samun yawaitar lalacewar tarbiyya, ya kamata mace ta ƙara taka-tsantsan wajen abinda take
kallo, abin da take wallafawa da kuma irin mutanen da take hulɗa da
su a kafafen sada zumunta (social media).
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.