Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Madigo

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam fatan an wuni lafiya malam inada tambaya malam akwai wata kawata da take cikin wani hali malam tace Dan Allah mene ne makomarta ta aikata san zuciyarta ne ta je wurin wata hajiya ta yi amfani da ita mace da mace Wanda amma daga wannan Rana ta yi nadama ba kuma tasakeyi ba ta ji tsoron Allah yashigeta shi ne tace shin Allah zai karbi tuban ta na gode

HUKUNCIN MAƊIGO

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

A shari'ar Musulunci, madigo wanda ake kiran SIHAQ babban zunubi ne kuma laifi ne dake tattare da sauraran hukunce-hukunce na TA'AZEER (hukuncin da alkali ya yanke domin hana saɓo), domin babu takamaiman hukuncin Haddi da ya zo a Nassoshi kai tsaye kamar na zina.

Saduwa tsakanin namiji da namiji (luwadi) ko saduwa tsakanin mace da mace (madigo) ko ta wani ɓangare saduwar ta kasance suka aikata ta gaba ne ko baya, shi ne mafi munin zunubi wanda saboda tsananin munanar sa har ALLAH ya hallaka al'umma akai, al'ummar Annabi luɗu (AS).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace'; ALLAH ya la'anci duk wanda ya aikata aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS) Wato luwadi, har sau uku Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana maimaita wa. Ahmad ya ruwaito.

Daga jabir Bin Abdillahi (RTA) Yace'; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Lallai mafi tsoron abunda nake jiye wa al'umma ta tsoro, aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS) ! Wato luwadi. [Ibnu majah albani ya inganta].

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace'; Duk wanda kuka tarar yana aikata aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS), to ku kashe wanda ke aikatawan da wanda ake aikatawa da shi ɗin.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Yace "Idan Mace Tazo Ma Mace (Wato Sukayi Madigo) To Su Biyun Mazinata Ne".

Madigo yana ɗaya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya kyamata, sai dai shari’ah bata bada ainihin wani hukuncin da za’ayi wa masu madigo ba. Sai dai mafi yawan malamai suna ganin za’ayi masu hukunci dai-dai da na yan luwadi. wato kashe duk wanda ke aikatawan da wanda ake aikatawa da shi.

Masana ilimin fiqihu sun tafi a kan cewa malami ko alkali yana da ikon yanke wa mai aikata madigo hukuncin bulala mai zafi, daurin kurkuku, ko kuma wulaƙantarwa domin ya azabtar da ita ta yadda za ta hana wani ko ita sake aikatawa.

To ya zama wajibi gareta ta tuba kuma ta yawaita istigifari tare da nadama bisa abinda ta aikata, kuma ta nisanci duk wata kawarta ko wata hanyar da za ta mayar da ita ga wannan dabi'a. Allah mai gafara ne mai jin qai. Yana karɓar tuban bayinsa aduk sanda suka tuba zuwa gareshi. Mutukar sunyi irin tuban da yake so.

Ta yawaita ayyukan alkhairi tare da rokon gafarar Ubangiji mutukar tana raye aduniya. Domin bata da tabbacin shin Allah ya karɓi tubanta ne ko bai karɓa ba!!!. Don haka kada ta ɗauki abun kamar Qaramin abu.

Anan nake jan hankalin 'yan uwa Mata cewa duk matar da tasan acikin Qawayenta akwai mazinata da 'yan madigo cewa ta nisancesu ta dena Qawance dasu. Domin Allah ya kawomu wani irin zamani wanda mutane basu ganin girman kowanne irin saɓon Allah mutukar zasu samu biyan bukata.

Wajabi ne ga duk masu irin wannan dabi’ar ta madigo da suji tsoron Allah su nisantar da kan su ga barin yinsa. Su tuna ko wane lokaci za su iya riskar mahaliccin su bayan suna aika wannan mummunar aikin.

Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da ka kiyaye mu da fadawa cikin wannan halin, ka shiryar da masu yi, ka gafarta mana ka kuma anshi tuban mu. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments