Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Sudan Na Kwantagora Na Uku, Malam Ibrahim Umaru Nagwamatse

Jagora: Namiji kamam maza yakai

Jagora /Y/Amshi: Jikan Shehu na tsaye,

Namiji kamam maza yakai,

Jikan Shehu na tsaye

Jagora: Mai riƙon ɗakin duniyag ga

Jagora /Y/amshi: Baya sakewa da hwama,

Namiji kamam maza yakai,

Jikan Shehu na tsaye

Jagora: Namiji kamam maza yakai

Jagora /Y/amshi: Jikan Shehu na tsaye,

Namiji kamam maza yakai,

Jikan Shehu na tsaye

Jagora: Yai magana mun amsa,

Bana ga babbas sallah

Jagora /Y/amshi: Za mu layya da Sarkin makangara,

Namiji kamam maza yakai,

Jikan Shehu na tsaye

Jagora: Bajinin Bello yaci birnin Gwari,

Yaci birnin Kogo,

Yaci birnin Gwari,

Yaci birnin Kogo

Jagora /Y/amshi: Barbare duka bawan gidanku na,

Namiji kamam maza yakai,

Jikan Shehu na tsaye.

Haka dai ☝️☝️☝️☝️ Makaɗa Salihu Alasan ɗan Giye ɗan Tigari mai abin kiɗi na Rawayya ya ce suka faɗawa Sarkin Sudan na Kwantagora na 3, Malam Ibrahim Umaru Nagwamatse lokacin da shi Jankiɗi da mahaifinsa Alasan ke 'yan amshi a ƙungiyar Kiɗa ta kakansa wato Makaɗa Giye ɗan Tigari mai abin kiɗa.

Sarkin Sudan Na Kwantagora Na Uku, Malam Ibrahim Umaru Nagwamatse

Sarkin Sudan na Kwantagora Ibrahim ɗan Sarkin Sudan na Kwantagora na farko wato Malam Umaru Nagwamatse yayi sarauta har sau biyu. Lokaci na farko shi ne daga shekarar 1880 zuwa 1901 karo na biyu kuma daga 1903 zuwa rasuwarsa a shekarar 1929. Allah ya kyauta makwanci, amin.

To ya wannan lamari ya faru? Turawan mulkin mallaka na Ingila a ƙarƙashin jagorancin Frederick Lugard sun mamaye Kwantagora da yaƙi a ƙarshen watan Janairu na shekarar 1901 saboda abin da suka kira rashin amincewa da mulkinsu da shi Sarkin Sudan Ibrahim ɗan Umaru Nagwamatse da jama'arsa suka yi. Su kore su daga Kwantagora shi da jama'ar tasa ciki kuwa har da su Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya.

Suka zo har ƙasar Ƙaya ta masarautar Zazzau domin kaucewa wannan iftila'i inda daga bisani Turawan su ka kama Sarki Ibrahim suka kai shi Lokoja sai a shekarar 1903 suka sake dawowa dashi a Kwantagora ya ci gaba da mulkinsa har zuwa 1929 da Allah SWT ya karɓi abinsa.

Daga Ƙaya su Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya suka koma ƙasarsu ta asali inda ya ci gaba da rayuwa har zuwa rasuwarsa a shekarar 1973. Allah ya jaddada masa rahama, amin.

Ɗiyan wannan waƙa da muka yanko a sama suna tattare da tarihi matuƙa. Wanzuwar wannan tun a mulkin Sarki Ibrahim (1880-1901 da kuma 1903-1929) ya bayyana muna dogon zamani da Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya ya ja a rayuwarsa. A gabansa aka gwabza yaƙi da Kwantagorawa da Turawan Ingila ga kuma irin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa bayan wannan mamaya ta Turawa.

Sun kira Sarkin Sudan Ibrahim da "Namiji kamam maza yakai" domin su tunatar dashi irin famar kakanninsa ( su Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo da Malam Abdullahi Ɗanfodiyo da Muhammadu Bello da Abubakar Atiku) da kuma mahaifinsa Malam Umaru Nagwamatse suka yi wajen jaddada addinin musulunci wanda ya haifar da Daular Usmaniyya. Domin a ciki ya na cewa "Jikan Shehu na tsaye".

"Yai magana na Garba mun amsa" anan suna danganta Sarkin Sudan Ibrahim da yayansa/wansa Sarkin Sudan na Kwantagora na 2 wato Abubakar ɗan Modibbo.

Sai suka ci gaba da cewa "Bana ga babbas sallah, zamu layya da Sarkin makangara". Kenan duka Sarkin da ke da ƙasa musamman kusa da masarautar Kwantagora amma baya biyayya ga Sarki Ibrahim to ya kwana da kari.

Domin ƙara fitowa da ƙarfin mulki na Sarki Ibrahim sai suka ce masa "Bajinin Bello yaci birnin Gwari, yaci birnin Kogo" domin su nuna yadda Sarkin Sudan na farko , mahaifin Sarki Ibrahim wato Malam Umaru Nagwamatse ya yi fama tare dasu ya'yansa wajen kafa masarautar Kwantagora. Suka kuma ambace shi da "Bajinin Bello... Wane Bello kenan? Amirul muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo tunda yayan/wan kakansa Sarkin Musulmi Abubakar I /Atiku mai Katuru ne.

Sai suka ƙara da wasan barkwanci dake a tsakanin Fulani( jinsin zuriyar su Sarki Ibrahim) da Barebari/Kanuri mutanen daular Borno.

Mahaifin Sarki Ibrahim wato Malam Umaru Nagwamatse ne ya samar da masarautar Kwantagora.

Malam Umaru ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku mai Katuru ne da ya yi sarautar Sarkin Musulmi daga shekarar 1837- 1842.

An haifi Malam Umaru a wani ƙauye da ake kira Gwamatse dake cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Wamakko ta Jihar Sakkwato ta yau a dai dai lokacin da kakani da iyayensa ke gudanar da jihadi na jaddada addinin musulunci a farko farkon ƙarni na 19 (1800s miladiya).

Wasu masana kuma suka ce a'a haihuwar Malam Umaru ta faru ne a wani wuri da aka kira "Gwamatse" dake cikin masarautar Bakura a Jihar Zamfara ta yau a lokacin da masu jihadi ke zaman Ribaɗi (a halin yanzu babu wannan wuri sai dai ayi kirdado/hasashe). To ko ma dai ya batun yake Malam Umaru ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi ya samu alkunyarsa ta "Nagwamatse" daga wajen /wurin da aka haife shi.

Ya fito ya doshi kudu maso yammacin Sakkwato har sai da ya samar da masarautar Kwantagora da hedikwata a Kwantagora ta hanyar yaƙe - yaƙe. A shekarar 1859 yayansa /wansa Sarkin Musulmi Malam Ahmadu ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I / Atiku mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo (yayi sarauta daga shekarar 1859 - 1866 ya umurci Sarkin Gwandu Malam Haliru mai Kara - Kara (yayi sarauta daga shekarar 1850-1860) da yaje ya naɗa Malam Umaru Nagwamatse sarautar Kwantagora da laƙabin "Sarkin Sudan".

Malam Umaru Nagwamatse ya kasance Sarki har zuwa wafatinsa a shekarar 1876. Daga nan ne zuriyarsa suka ci gaba da mulki a wannan masarauta ya zuwa yau da mai martaba Sarki Muhammadu Bara'u Mu'azu ya kasance Sarki na 7.

Mai martaba Sarki Muhammadu ɗan Malam Bara'u ne, Malam Bara'u ɗan Sarkin Sudan na Kwantagora Mu'azu ne wato Sarki na 5 da yayi sarauta daga shekarar 1961-1974, shi kuma ɗan Sarki na 3 Ibrahim ne wanda yayi mulki har sau biyu 1880 - 1901 da kuma 1903-1929, shi kuma ɗan Sarkin Sudan na Kwantagora na farko ne wato Malam Umaru Nagwamatse da yayi sarauta daga shekarar 1859-1876, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Atiku mai Katuru ne wanda yayi sarautar Sarkin Musulmi daga 1837-1842, shi kuma ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ne.

A hoton dake tare da wannan sharhi mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. (Dr.) Muhammad Sa'ad Abubakar CFR Mni ne a gefen dama tare da mai martaba Sarkin Sudan na Kwantagora, Alh. Muhammad Bara'u Mu'azu. A ɗiyan waƙar da aka yi amfani dasu wajen gabatar da sharhinmu ana ambatar "Shehu da Bello" a ciki saboda bayyana alaƙar waɗannan gidaje guda biyu wato Sakkwato da Kwantagora.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. (Dr.) Muhammad Sa'ad Abubakar CFR Mni ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III, shi kuma Sarki Abubakar III(yayi sarauta daga 1938-1988) ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne wanda ya yi sarauta daga shekarar 1877-1881, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne wanda yayi mulki daga shekarar 1817-1837, shi kuma ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ne.

Kenan yaya /wa ne da ƙane daga kaka guda ɗaya, Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo.

Allah SWT ya jaddada rahamarsa zuwa ga dukkan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Daga Taskar:
Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.
11/08/2026

Post a Comment

0 Comments