𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Magidanci ne yake da matar aure mara sha’awa, yana shan wahala sosai wurin neman biyan buƙatarsa a wurinta. Takan tsara masa wasu abubuwan da sai ya cika su kafin ya samu biyan buƙatar, wasu lokutan ma sai ta gama lamarrunta kafin ta saurare shi. Abin har yakan kai shi ga bin wasu hanyoyi kamar kallon haram domin gamsar da buƙatarsa. Wai wace shawara za a ba shi?
YANA SHAN WAHALA
WURIN NEMAN BIYAN BUƘATA A WURIN MATARSA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh
Da farko dai wajibi
ne ma’aurata su san cewa biyan buƙatar juna ta hanyar
saduwa yana daga cikin manyan dalilai ko maƙasudan yin aure.
Haƙƙi ne mai girma a kan
mace ta zama a cikin shirin biya wa mijinta wannan buƙatar a duk lokacin da
ya yi buƙata, matuƙar dai ba tana cikin yanayi ko halin
da shari’a ta hana saduwa a cikinsa ba ne, kamar a
lokacin rashin lafiya ko haila ko nifasi. Har a waɗannan lokutan ma
malamai sun yarda cewa matar tana taimaka wa mijin wurin jin daɗi da duk inda ya so a
jikinta, ta hanyar shafa ko runguma ko sumba da makamantansu, in ban da saduwar
ta wurin da aka hana. Watau, bai halatta ya yi amfani da al’aurarsa a cikin
gabanta a lokacin haila ko nifasi ba, haka ma ta cikin duburarta, ko ta cikin
bakinta ba a kowane lokaci.
Amma a lokacin da
miji ya ga irin wannan matsalar a cikin matarsa, abu na farko da ya kamata ya
fara dubawa shi ne: Ta yaya aka samu hakan? Matsalar daga wurin ta ne, ko kuwa
daga wurin sa ne?
Abin nufi a nan shi
ne: Me yiwuwa matar tana da wata matsala ta damuwa ko rashin lafiya ne shiyasa
take gudun saduwar. Ko kuma ba ta da sha’awar saduwar da namiji ne, saboda ta
riga ta shiga ƙungiyar masu maɗigo da suke neman yawaita a wannan zamanin!
(Allaah ya kiyaye).
Ya kamata mijin ya
zaunar da matarsa cikin natsuwa da soyayya, ba tare da fushi ko zargi ba, don
jin dalilin da ya sa ba ta jin sha'awar. Wani lokaci matsalar ta kan samo asali
ne daga gajiya, damuwa, rashin lafiya, ko kuma kuskure a salon jima'in (foreplay).
Haka kuma matsalar
tana iya kasancewa saboda dalilin yadda shi ya fara mu’amalantarta a karon
farko ne, ko kuma yadda yake mu’amalantarta har a yanzu. Watau, me yiwuwa a
karon farko da ƙarfi ya yi mata, ba tare da kulawa da ƙoƙarin janyo hankalinta
ko motsar da sha’awarta ga buƙatar ba. Ko kuma me
yiwuwa ba ya damuwa da ko ita ta samu nata biyan buƙatar ko ba ta samu
ba. Shi dai kawai idan ya gama buƙatarsa shikenan, babu
ruwansa!
Shi dai mu’amalar
saduwa a tsakanin ma’aurata, kamar yadda masana suka yi bayani, ba abu ne da za
a ɗauke shi irin yadda
wasu sabbin angwaye da amare suke ɗaukarsa ba: A riƙa neman shi a kullum
da safe, da rana, da yamma, da daddare kamar ibadar Sallah da Salati! Abin da
babu wanda zai ƙwace maka, kuma babu ranar da zai ƙare har zuwa mutuwa,
menene na haɗama ko gaggawa a
kansa?
Shi ana zuwa masa ne
a lokacin da buƙatarsa ta taso kawai, kamar dai abinci. Amma sai ka ji
wasu a kan haka wai har magani suke sha, domin ya nuna mata shi namiji ne! Ko
wai ta nuna masa ita ba ƙaramar mace abar wasa ba ce! Irin wannan shi ke janyo
matsala a tsakanin ma’aurata idan ba a samu daidaito a tsakaninsu
ba.
Maganin wannan dai
ma’aurata su zauna, ko dai su kaɗai ko tare da wani amintaccen masani, domin
bayar da shawarwari masu amfani a kan wannan matsalar. Muhimmi dai su riƙa la’akari
da yanayi da halin buƙata ko rashinta daga juna a kowane lokaci, kafin neman
biyan buƙatar. Ita dai mace, kamar yadda na faɗa a baya, a kullum ta
zama a cikin shirin biya wa mijinta buƙatarsa.
Al-Imaam Muslim
(1403) da Al-Imaam Abu-Daawud (2151) da Al-Imaam At-Tirmiziy (1158) sun riwaito
hadisi sahihi daga Sahabi Jaabir _(Radiyal Laahu Anhu)_ cewa: Watarana Manzon
Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ga wata mace a waje, don
haka sai ya tafi gida wurin matarsa Zainab _(Radiyal Laahu Anhaa),_ ya same ta
tana aikin jeme wata fata. Sai ya biya buƙatarsa a wurinta,
sannan ya fito wurin Sahabbansa, ya ce:
« إِنَّ
الْمَرْأَةَ تُقْبِلُ فِى صُورَةِ شَيْطَانٍ ، وَتُدْبِرُ فِى صُورَةِ شَيْطَانٍ ،
فَإِذَا أَبْصَرَ أَحَدُكُمُ امْرَأَةً فَلْيَأْتِ أَهْلَهُ ، فَإِنَّ ذَلِكَ
يَرُدُّ مَا فِى نَفْسِهِ »
Ita mace tana
fuskantowa a cikin siffar shaiɗani ne, kuma tana juyawa a cikin siffar shaiɗani ne. To, idan ɗayanku ya ga wata
mace, sai ya koma gida ya sadu da matarsa. Wannan shi zai mayar da abin da ke a
cikin ransa.
Wannan ya nuna:
1. Mace a gidan mijinta tana zama a cikin
shirin biya masa buƙatarsa ta saduwa ce a duk lokacin da ya yi buƙatar hakan daga
wurinta.
2. Zama cikin wannan
shirin ba ya hana mace ta cigaba da wasu ayyukanta na yau da kullum a cikin
gidan, kamar yadda ya same ta tana gyara fata.
3. Ba daidai ba ne
mace ta zauna haka nan kawai, ba ta aikin komai sai latsa wayoyi da kallon
tashoshin nuna fitsara iri-iri.
4. Wannan shi ke
haifar da matsaloli a cikin gidajen auren zamunan yau, domin ma’aurata suna yin
watsi da haƙƙoƙin da suka zama
wajibai zuwa ga abubuwan da ba su da muhimmanci a rayuwarsu!
5. Bai halatta mace
ta tsara wa mijinta wasu abubuwan da wai sai ya gama yi mata su, sannan ne za
ta amince ta biya masa buƙatarsa ba.
6. Idan kuma ta tsaya
a kan yin hakan, to bayan zunubin hana shi haƙƙinsa, akwai kuma
taimakawa wurin buɗe ƙofar yin zina a wurin
mara tsoron Allaah, musamman ma a wannan zamanin.
7. Sannan yaya matsayin irin wannan matar zai
kasance a lokacin da mijin ya samu damar auro wata matar kirkin da ba ta yi
masa irin wannan?
Kallon tsiraici domin
wai samun biyan buƙata da kwantar da sha’awa shi ma matsala
ce. Domin bayan ya saɓa wa koyarwar Addini,
akwai kuma koyon munanan ɗabi’u da halaye a
cikinsa. Wani namijin kan iya ƙoƙarin kwatanta duk
abin da ya gani a cikin waɗannan hotunan ko video wanda kuma ba gaskiya ba ne, domin
tsara su ake yi a fim kawai. Wannan shi ke kai wani ga cutar da jikinsa, ko
kuma ma ga hallaka kansa. Kamar yadda wata macen ma kan kasa gamsuwa da
mijinta, saboda bai iya yi mata irin yadda ta ga ana yi a cikin irin waɗannan fima-fiman ba!
Abin da ya ke magani
dai shi ne, duk mu ji tsoron Allaah kawai a cikin zamantakewarmu a gidajen
aurenmu. Kar mu sake mu bi hanyoyin son-kai, ko cutar da abokin zamanmu ba da
haƙƙi
ba. Kar mu ɗauki al’amarin
saduwar aure ya zama kamar abincin da babu makawa a rayuwa sai an ci shi, mu riƙa yin haƙuri da juna, mu
nisanci shaye-shayen magungunan ƙarin ƙarfi, ko masu janyo ƙarin sha’awar
saduwa ba da wata larura ko umurnin masana ba.
Amma idan duk waɗannan hanyoyin da
makamantansu sun gaza kawo maslaha a tsakanin ma’aurata, to suna iya ɗaukar matakin rabuwa
da juna, ko dai ta saki ko kuma ta khul’i a ƙarƙashin koyarwar
Sunnah.
Da fatar Allaah ya
zaunar da gidajenmu lafiya, mu iya haƙurin tarbiyyar ’ya’yanmu
tarbiyyar musulunci sahihiya.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.