Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Rantse Ba Zai Sake Nema Na Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mun samu saɓani da mijina, har ya rantse cewa ba zai ƙara nema na ba, sai idan ni ce na neme shi. Ni kuma yau shekaru biyu kenan ban je wurinsa don nemansa ba. To, ko ina da laifi a kan ƙin nemansa da na yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Ƙwarai kuwa kina da laifi a kan wannan matsayin da kika ɗauka, ko dayake a asali ba mace ce aka ɗora wa neman miji don biyan buƙata ba. A nan kin kayar da haƙƙinsa da Allaah Taaala ya ɗora a kanki ta fuska biyu:

1. Biya masa buƙatarsa na ya mace haƙƙinsa ne a kanki, wanda kuma shi ne babban maƙasudin ƙulla aure a tsakaninke da shi. Idan kuwa ba haka ba, to kin yarda kenan cewa: Ya je ya nemi wata a waje. Wannan kuwa ba ƙaramin laifi ba ne. Shiyasa ma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« إِذَا بَاتَتِ الْمَرْأَةُ هَاجِرَةً فِرَاشَ زَوْجِهَا لَعَنَتْهَا الْمَلاَئِكَةُ حَتَّى تُصْبِحَ ».

Idan mace ta kwana alhalin tana mai ƙaurace wa shimfiɗar mijinta, Mala’iku za su yi ta la’antar ta har zuwa asubah. (Sahih Muslim: 3611).

2. Sannan kuma haƙƙinsa ne a kan ki cewa: Ki kare shi daga yin kaffaran alwashi ko rantsuwarsa idan ya karya shi, a matsayinsa mijinki kuma musulmi, kamar yadda Sahabi Al-Baraau Bn Azib (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):

أَمَرَنَا بِاتِّبَاعِ الْجَنَائِزِ ، وَعِيَادَةِ الْمَرِيضِ ، وَإِجَابَةِ الدَّاعِى ، وَنَصْرِ الْمَظْلُومِ ، وَإِبْرَارِ الْقَسَمِ ، وَرَدِّ السَّلاَمِ ، وَتَشْمِيتِ الْعَاطِسِ .

Ya umurce mu da raka gawa, da dubo mara lafiya, da amsa gayyata, da taimakon wanda aka zalunta, da rayar da rantsuwa, da mayar da sallama, da gai da mai atishawa. (Sahih Al-Bukhaariy: 1239).

3. Amma shi ma mijinki bai halatta gare shi ya ɗauki irin wannan tsattsauran matakin ba tun farko. Domin ƙaidar da addini ya sanya ita ce: Duk lokacin da miji ya rantse cewa ba zai sadu da matarsa ba, to za a duba a gani: Idan lokacin da ya sa bai kai watanni huɗu ba, sai a bar shi har zuwa cikan lokacin. Amma idan kuwa lokacin ya wuce watanni huɗu, to idan watannin huɗun sun cika dole ne a tsayar da shi: Ko dai ya komo ya cigaba da saduwa da ita, ko kuma ya sake ta. (Surah Al-Baqarah: 226).

Don haka, wajibinku ne ku yi taka-tsantsan a kan al’amarin aurenku, ku riƙe shi da muhimmanci, kuma ku kusanci malamai domin ƙara samun ilimi da gogewa a cikin dokoki da hukunce-hukuncensa.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments