𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam Su waye Ahlul-kitabi? Kuma shin akwai su a wannan Zamani? Kuma ya halatta aci yankansu ko a auri matansu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
Ahlul-Kitabi (Ma'abota
Littafi) su ne Yahudawa da Kiristoci. Su ne wadanda Allah Ya saukarwa da
littafi (kamar Attaura da Injila) a zamanin da, kodayake addinin na su ya shiga
sauye-sauye kafin zuwan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Shin Ahlul-Kitabi akwai su a
wannan zamani?Eh, suna nan har yanzu a wannan zamani. Kiristoci da Yahudawa da
muke gani a yau su ake nufi da Ahlul-Kitabi. Duk wata aya a cikin Alƙur'ani mai girma da ta yi magana kan
Ahlul-Kitabi, tana shafarsu ne a kowane zamani.
Ya halatta a ci yankan da
Ahlul-Kitabi suka yanka matukar dai sun yanka shi a kan tsarin da addininsu ya
tanada. Haka zalika, ya halatta a ci dukkan abincinsu (kamar kayan lambu da
sauransu) matukar ba a tabbatar da cewa sun hada da wani abu da Musulunci ya
haramta ba (kamar naman alade ko giya).
Cin yanke-yankensu yana
halatta, matukar dai ba a san da cewa an yanka dabbar ne ta hanyar da ba ta
dace da Shari'a ba, saboda asalin lamari shi ne halaccin cin sa, kamar dai
yankan musulmi, saboda faɗin Allah Maɗaukaki:
اَلۡيَوۡمَ
اُحِلَّ لَـكُمُ الطَّيِّبٰتُ ؕ وَطَعَامُ الَّذِيۡنَ اُوۡتُوۡا الۡكِتٰبَ حِلٌّ
لَّـکُمۡ وَطَعَامُكُمۡ حِلٌّ لَّهُمۡ وَالۡمُحۡصَنٰتُ مِنَ الۡمُؤۡمِنٰتِ
وَالۡمُحۡصَنٰتُ مِنَ الَّذِيۡنَ اُوۡتُوا الۡـكِتٰبَ مِنۡ قَبۡلِكُمۡ اِذَاۤ
اٰتَيۡتُمُوۡهُنَّ اُجُوۡرَهُنَّ مُحۡصِنِيۡنَ غَيۡرَ مُسَافِحِيۡنَ وَلَا
مُتَّخِذِىۡۤ اَخۡدَانٍؕ وَمَنۡ يَّكۡفُرۡ بِالۡاِيۡمَانِ فَقَدۡ حَبِطَ عَمَلُهٗ
وَهُوَ فِى الۡاٰخِرَةِ مِنَ الۡخٰسِرِيۡنَ
A yau an halatta muku
abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda
aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da
mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda
aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin
aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon
abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci,
kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra. (Surah: Al-Maaida, Ayat: 5)
Haƙiƙa
Shari'ar Muslunci ta halattawa Musulmi ya auri Mace Kirista ko Bayahudiya,
wannan ita ce Maganar mafi yawa daga cikin Malamai Ma'abota Ilimi, kuma
halaccin hakan ya samo Asaline daga cikin Alƙur'āni faɗin
Allah(ﷻ) kamar yadda Suratul Ma'idah aya ta 5 ta
tabbatar.
An samu wasu daga cikin
sahabai, sun aure Ahlul-kitabi kamar Usman ɗan
Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu ɗan
Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa masanin sirrin Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda.
Duba: Ahkamu-ahlizzimah 2\794.
Haka nan wannan Halacci ya
taƙaita ne kaɗai
akan Maza Musulmai, amma baya halatta ga Mace Musulma ta auri Kirista, ko kuma
dukkan wani wanda ba Musulmi ba.
Dan haka Malamai sukace idan
Ahlul-kitabi (Kirista ko Bayahudiya) ta kasance ta kame kanta bata aikata zina,
to ya halatta a aureta, duk da cewa suma Ahlul-Kitabi kafirai ne Mushrikai da
Nassin Alƙur'ani Mai girma, to
amma waccan aya ta keɓance su da wannan hukunci,
dan haka su kaɗai ne Allah(ﷻ)
ya halatta mana muci yankan su da abincin su kuma mu auri Matan su, shi ya sa wannan
halacci ya taƙaita ne kaɗai
akan Ahlul-kitabi (Yahudu da Nasara), amma sauran Kafirai da suke bautar waɗansu
abubuwa dabam-dabam kokuma waɗanda ma basu da wani abin
bauta (Majusawa) haramun ne a aure su, saboda faɗin
Allah(ﷻ):
وَلَا
تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن
مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ...
Kada ku auri Mata Mushrikai
(Kafirai), domin (ku auri) Baiwa Mumina shi yafi alkhairi akan ku auri Mushrika
koda kuwa kyawunta ya ƙayatar
daku…… (suratul Bakara aya 221)
Danhaka Malamai sukace idan
Musulmi ya aminta da cewa wannan Matar Kirista da zai aura ba zata iya
rinjayarsa ba yayi Ridda kokuma ta iya rinjayar 'ya'yansa zuwa ga addinin ta to
shikenan ya halatta ya aureta, danhaka ana buƙatar
Mutum ya kasance yana da Ƙarfin
imani dakuma ilimin addini atare dashi, sannan ya kasance niyyarsa ta yin auren
ita ce yayi ta ƙoƙarin nuna mata addinin Musulnci har ta
gane ta karɓa, to amma duk dahaka Malamai sukace
barin auren su ɗin shi ne yafi alkhairi,
Musamman ma a irin wannan zamanin da muke cikinsa wanda galibi idan an yi irin
wannan auren to Kallabi ne yake jan Rawani a madadin Rawani yaja Kallabi, abin
nufi da yawa mazan sukan yi ridda ne, kuma koda Mutum yana da ƙarfin imanin da ba zata iya rinjayar sa
ba, to abu ne mai sauƙi
awajenta ta iya rinjayar 'ya'yan da suka haifa tare dashi, shi ya sa Malamai
sukace barinsa ɗin zaifi sa Mutum yatsira da
imaninsa da kuma na 'ya'yansa, danhaka gara Mutum yaje ya nemi 'yar'uwar sa
Musulma ya aura.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.