𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum warahmatullah. Da fatan malam yana nan lafiya? Ubangiji ya karba mana ibadun mu! Malam shin akwai laya wanda ya halasta a yi amfani da shi? Misali, mutum yana tsananin rashin lafiya sai aka ba shi magani ya dafa ya sha, amma cikin ruwan maganin akwai abu mai kamar laya, shin ya hukuncin wannan magani? Shin amfani da shi shirka ne, idan shirka ne wani iri? Ubangiji ya saka da mafificin alkhayri!
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu
ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Laya mai sunan laya wacce
muka sani, babu wata laya da ta halatta musulmi ya rataya ko ya yi amfani da
ita wajen neman jawo alkhairi gare shi, ko kuma kare kan shi daga wani sharri.
Wannan ita ce maganar da ke da hujja a shari'a. Laya ko ta Alƙur'ani ce, baya halatta musulmi yai
amfani da ita don neman wata biyan buƙata,
wannan shi ne mafi ingancin zance da rinjaye, saboda hadisin Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam inda Ya ce:
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: ((إِنَّ الرُّقَى وَالتَّمَائِمَ وَالتِّوَلَةَ شِرْكٌ)).
Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam bai keɓance wani abu daga cikin
ukun nan, sai ruƙya
wacce babu shirka, amma sauran biyun ma'ana kowace irin laya (ta Alƙur'ani da wanin ta) da tiwala, shirka
ne, abin da hadisin ke ishara kenan. Duk wanda ya cire layar da aka yi da Alƙur'ani, ya ce ana iya amfani da ita, sai
ya kawo hujja inda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya cire ta kamar yadda ya
cire ruƙya shar'iyya kamar yadda yake a ƙasa:
عَنْ جَابِرٍ قَالَ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الرُّقَى فَجَاءَ آلُ عَمْرِو بْنِ حَزْمٍ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّهُ كَانَتْ عِنْدَنَا رُقْيَةٌ نَرْقِي بِهَا مِنَ الْعَقْرَبِ وَإِنَّكَ نَهَيْتَ عَنِ الرُّقَى. قَالَ فَعَرَضُوهَا عَلَيْهِ. فَقَالَ: ((مَا أَرَى بَأْسًا مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمْ أَنْ يَنْفَعَ أَخَاهُ فَلْيَنْفَعْهُ)).
عَنْ عَوْفِ بْنِ مَالِكٍ الأَشْجَعِيِّ قَالَ كُنَّا نَرْقِي فِي الْجَاهِلِيَّةِ فَقُلْنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ كَيْفَ تَرَى فِي ذَلِكَ فَقَالَ: ((اعْرِضُوا عَلَيَّ رُقَاكُمْ لاَ بَأْسَ بِالرُّقَى مَا لَمْ يَكُنْ فِيهِ شِرْكٌ)).
Don haka, idan har laya ce
kamar yadda kika ambata, toh baya halatta a nemi waraka da ita. Hukuncin ta ya
baiyana ƙarara cewa shirka ce, daga hadisin da
muka koro a sama, don haka amfani da wannan magani bai halatta ba, Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce, duk wanda ya rataya laya haƙiƙa ya
yi shirka, hadisin
6394 - «من علق تميمة فقد أشرك».
(صحيح) [حم ك] عن عقبة بن عامر. الصحيحة
492.
Bayan haka a cikin lamarin
amfani da laya, akwai ratayar da zuciya ga wannan laya da maras lafiya zai yi,
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce duk wanda ya rataya wani abu, an
dogarar da shi zuwa gare shi, ma'ana, addu'a ce, abin ya zamo abin dogaron sa
ke nan, na'uzhu billah
دخَلتُ علَى عبدِ اللَّهِ بنِ حُكَيْمٍ وبِهِ حُمرةٌ، فقلت: ألا تعلِّقُ تَميمةً ؟ فقالَ:: نعوذُ باللَّهِ مِن ذلِكَ وفي روايةٍ الموتُ أقرَبُ من ذلِكَ، قالَ رسولُ اللَّهِ مَن علَّقَ شيئًا وُكِلَ إليهِ
Amma ya halatta ta cire
layar ta sha maganin idan shi ma ba a yi shi da najasa ko sina dari da Allah ya
haramta.
Mallamai na kasa nau'ukan
shirka gida uku ne, sune:
1. Shirkul Akbar
2. Shirkul Asghar
3. Shirkul Khafiyy
A nan mutum ya yi Shirkul
Akbar ne mai fitarwa daga musulunci. Sannan Mallamai suna rarrabe shirkul akbar
zuwa gida huɗu, sune:
1.Shirku Adda'awah
2. Alƙasdi wanniyah
3. Almahabbah
4. Shirku Aɗɗa'ah.
Wallahu ta'aala a'lam.
Amsawa: Malam Aliyu Abubakar Masanawa
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa Da Tunatarwa a Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.