Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sakon Gaisuwar Juma'a (Jūma'at-Mubarak)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

A Shari'ance Mene ne hukuncin Sakon Gaisuwar Juma'a, da ake yi wa Mutane ta Text ko Social Media??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ko shakka babu cewa Ranar-Jūma'a rana ce ta īdi a wajen Musulmai, kamar yadda ya zo a Hadīsi cewa Mαnzon Aʟʟaн (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:

​إن هذا يوم عيد جعله الله للمسلمين، فمن جاء إلي المسجد فليغتسل.......... (رواه إبن ماجه/1098)

​​MA'ANA​​: ​​Lallai wannan rana ce (Jūma'a) da Aʟʟaн () ya sanyata amatsayin īdi ga Musulmai, danhaka idan Mutum zaije Masallaci to ya yi wanka.

Danhaka kenan Musulmai sunada ranekun īdi ne guda uku kawai a Muslunci:

​​-Īdin-Ranar-Jūma'a:​​

​​-Īdin-Babbar-Sallah:​​

​​-Īdin-ƙaramar-Sallah:​​

Sai dai Īdin-Babbar-Sallah da Īdin-ƙaramar-Sallah sukan maimaitune aduk Shēkara, amma Īdin-Ranar-Jūma'a yakan maimaitune duk Sati-Sati,​​

Amma dangane da abin da yashafi hukuncin Sakonu-Gaisuwar-Jūma'a, da Mutane sukeyi a tsakaninsu, kamar irin su: ​​Jūma'at-Karīm, Jūma'at-Mufīdat,​​ ​​Jūma'at-Mubarak, Jūma'at-Ɗayyibat,​​ Dadai sauran makamansu, sai ariƙa aikawa 'Yan'uwa da abokan arziƙi ta hanyar Text-Message, ko kuma ta Social Network, Abin da yake a Shari'ance kamar yadda Malamai suka faɗa shi ne, Asali Muslunci ya yardane kawai da Gaisuwar Ranekun Īdin-ƙaramar-Sallah da Babbar-Sallah, sūma a bisa ga wasu lafuzza da Shari'a ta yarda a yi amfani dasu, amma gameda Gaisuwar-Jūma'a, babu inda Shari'a ta yi bayanin cewa ayi, danhaka da yawa daga cikin Malamai suka ce yin Gaisuwar-Jūma'a Bid'ace, musamman idan ya kasance masu yin hakan suna ƙudurta cewa akwai wani lada da za a samu ga duk wanda yayi, to ko Shakka babu cewa ya zama Bid'a, domin ba a samu hukuncin yin hakan a cikin wani Nassi ko aikin magabata ba.

Sai dai akwai Malaman da suke ganin cewa idan Mutum ya yi Gaisuwar-Jūma'a, tare da cewa yasan bata da asali a cikin addīni sannan kuma bai ƙudurta cewa yin hakan Sunna ba ne, ko kuma idan Mutum yayi zai samu wani lada akaiba, kawai suna yine amatsayin al'ada bawai da sunan addīniba, suka ce to babu wani laifi akansu dan sun yi, sai dai duk da haka suka ce barin yinsa ɗin shīne ya fi zama alkhairi, saboda gudu kada Jahilai su rūɗu da cewa hakan adiīnine, wanda kuma galibin masu aika Sakon-Gaisuwar-Jūma'a, awannan zamanin zaka samu cewa suna yīne danufin samun lada bawai suna yine amatsayin al'adaba, Aʟʟaн () dai Ya ganar damu gaskiya kuma yabamu īkon binta Amīn-Ya-Rabbi.

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:​​ ↓↓↓​​

"زاد المعاد" (1/380)

"الفتاوي الكبري" (2/228)

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαмυ

 ​​AMSAWA

 Mυѕтαρнα Uѕмαn

 08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam HUKUNCIN SAKON GAISUWAR JUMA'A (JŪMA'AT-MUBARAK)

Tambaya:

A shari’ance, mene ne hukuncin sakon gaisuwar Juma’a da ake yi wa mutane ta Text ko Social Media?

Amsa:

Ranar Juma’a rana ce mai daraja sosai a Musulunci, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:

النصّ بالعربي:

"إن هذا يوم عيد جعله الله للمسلمين، فمن جاء إلى المسجد فليغتسل..." (رواه ابن ماجه 1098)

Hausa:

Lallai wannan rana ce ta īdi da Allah ya sanya wa Musulmai, wanda ya zo masallaci to ya yi wanka...”

Musulmai sun san ranakun īdi guda uku ne kawai:

Īdin Babbar-Sallah

Īdin Ƙaramar-Sallah

Īdin Ranar Juma’a

Īdin Babbar-Sallah da Ƙaramar-Sallah sukan maimaitu shekara-shekara.

Īdin Ranar Juma’a yakan maimaitu duk sati-sati.

Hukuncin Sakon Gaisuwar Juma’a:

Sakon kamar “Juma’a Mubarak”, “Juma’a Kareem”, ko makamancinsu, ba shi da asali daga Al-Qur’ani ko Sunnah.

Masana sun ce yin hakan Bid’a ne idan mutum ya ƙudurta cewa yin sa yana da lada musamman.

Duk da haka, wasu masana sun ce idan mutum ya yi sakon yana ɗaukar shi kawai a matsayin al’ada, ba tare da ƙudurin samun lada ko nuna ibada ba, babu laifi a kansa.

Amma mafi kyau shi ne kar a zamar da wannan sako al’ada ta addini, domin mutane kada su ɗauka cewa ibada ce ko sunnah ce.

Kammalawa:

Sakon Juma’a ba daga sunnah ba ne.

Yin sa da nufin lada ko ibada yana zama Bid’a.

Yin sa kawai a matsayin gaisuwa da al’ada ba laifi, amma mafi alkhairi shi ne a bar shi.

A mayar da hankali kan karatun Qur’ani, sallar nafila, da zikiri a ranar Juma’a, wanda yake da asali a addini.

Mabooki:

زاد المعاد (1/380)

الفتاوي الكبري (2/228)

Allah Ya bamu ikon aikata abin da Ya yarda, Amin.

Post a Comment

0 Comments