Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Musulmai Za Su Ga Allah Idan Sun Shiga Aljanna

DALIBI:

Malam Allah ya kai mu aljannah wlh malam ina son aljannah

Malam wato aljannah waii ka san mene ne sirin cikin gidan aljannah hmm saboda akwaii manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam

SHIN MUSULMAI ZA SU GA ALLAAH IDAN AN SHIGA ALJANNAH

USMANNOOR ASSALAFY

Dan uwa - ina kyautata zaton ba ka karanta littafin: "Hadil Arwah ila biladil Afrah" ba wallafar Imam Ibn al - Ƙayyum al - Jauziyya da kuma littafin: "Paradise and Hell Fire" wallafar Imam al - Ƙurtubi da kuma littafin: "Albidaya wan Nihaya" na Ibn Khathir (Allaah ya jikansu da rahama baki daya)

Da a ce ka karanta su kuma ka fahimce su to da tabbas za ka gasgata cewar da akwai sirrin da ya fi ganin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)

Wato ganin wanda ya halicci Manzon Allaah (Sallallahu alaihi wasallam)

Wato Allaah Azzawajallah

Hujja:

 (وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ )

القيامة (22) Al-Ƙiyaama

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

 (إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ )

القيامة (23) Al-Ƙiyaama

Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

Da kuma

 (لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا الْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلَا ذِلَّةٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )

يونس (26) Yunus

Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.

Wannan ayar ni da kaina na ga mu'ujizarta, shekaru 3 baya lokacin da muna zaune da abokaina da damina an hado hadari, ina karanta daidai inda Allaah ya ce: "Wata kura ba ta rufe fuskokonsi a Aljannah"

Sai kawai kura ta rufe mana fuskokinmu, sai kowa ya fara rufe fuskarsa, masu furzar da kasa na yi - mai Subhanallah na yi, anan take na nunawa abokaina cewar a daidai lokacin da nake karanta wannan ayar kuma a daidai kokacin da kurar duniya ta rufe mana fuskokinmu. Kowa ya cika da mamaki, muna firta Allaahu Akbar.

Ibn al - Ƙayyum ya ce: "Babbar ni'imar da za a bawa yan Aljannah ita ce ganin fuskar Allaah"

Shi kansa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba abin da ya fi so sama da Allaah ya lullube shi da rahamarSa ya saka shi a Aljannah, wannan ne ma yasa yake yawaita karanta adduar son ganin fuskar Allaah Azzawajallah:

 اللَّهُمَّ إنِّي أسألكَ لذَّةَ النَّظرِ إلى وجْهِكَ والشَّوقَ إلى لقائِكَ في غيرِ ضرَّاءَ مُضِرَّةٍ، ولا فتنةٍ مُضِلَّةٍ، اللَّهُمَّ زيِّنَّا بزينةِ الإيمانِ، واجعلنا هداةً مهتدينَ

— (An rawaito shi daga Nasa’i da Ahmad, Albani ya inganta shi).

“Ya Allah! Ina roƙonka niiman kallon FuskarKa, da ƙaunar saduwa da Kai, ba tare da wata cutarwa ba, kuma ba tare da wata fitina ta bata ba. Ya Allah! Ka ƙawata mu da kayan ado na imani, ka sanya mu shuwagabanni masu shiryarwa.

Duk da waɗannan ayoyin da sahihan hadisan amman fa akwai wadansu mutanen da ba su yarda cewar za a ga Allaah ba. Majority dinsu yan Ƙur'aniyyun ne.

Last week, da na halarci Daurah Ilimiyya a Bayero Umiversity Kano musamman na yiwa Shaikh Dr. Magaji Fadlu Zarewa (Hafizahullah) tambaya akan makomar irin waɗannan mutanen idan suka mutu ba su yarda za a ga Allaah ba a Aljannah, har na kawo misalin wani dan Ƙuraniyyun a anguwanmu da mukaita tafka muƙabala da shi akan hakan

Ya ce idan misunderstanding din hujjoji daga ayoyi da hadisai sukai to ana musu uzuri amman indai take sanin sukai to anan suna karyata ayar Allaah ne wanda hakan kafirci ne

Muna rokon kamar yanda muka hadu a wannan zaure na gyaran suratul fatiha, Allaah ya sa mu ga mahiliccinmu a Aljannah baki daya😅🤲

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments