Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Sunan Aisha Humaira

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam na haihu na sami ɗiya mace an sanya mata suna AISHA to sunan mahaifiyata ne shi ne na ce zan kira ta da HUMAIRA to mutane dayawa sun ce min HUMAIRA yana nufin jaririn jaki dan Allah malam hakane ina son karin bayani dan nasami sunan kiranta yau kwananta 11

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Toh HUMAIRA ma'anarta shi ne 'Yar Ja, wanda asali daga Hamra'u ne, wato Ja, se aka yi tasgirinsa ake cewa HUMAIRA, wannan kuma wani salo ne na larabawa idan sunaso su ƙanƙanta abu, ga babba ga ƙarami ga kuma ɗan ƙarami toh wannan ɗan ƙaramin shi ne suke tsamo sunanshi daga jikin sunan babban, misali UMAR, idan kanaso kace ɗan ƙaramin UMAR sekace UMAIR. USMAN idan kanaso kace ɗan ƙaramin USMAN sekace USAIMIN, SALAHA idan kanaso kace 'yar ƙaramar SALAHA sai kace SULAIHAT. ZALIHA kuma ZULAIHAT, toh itama HUMAIRA asali daga Hamra'u ne wato Ja, idan kanaso kace 'yar Ja wato ƙaramar Ja shi ne sai kace HUMAIRA, kuma wannan sunan babu laifi acikinshi domin ko acikin hausawa akwai wacce ake cemata 'yar ja kuma tana amsawa, toh ma'anar wannan 'yar ja ɗin shi ne HUMAIRA.

Amma AISHA tasamu laƙabin HUMAIRA ne daga Bakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam lokacinda AISHA tatare a gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam to 'yarsa FATEEMA ta girmi AISHA, ita kuma AISHA tana ganin kanta matsayin matar uba gakuma ƙuruciyarda take kansu a wannan lokacin se suka riƙa ɗan samun saɓani tsakaninsu toh shikuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ko kaɗan ba ya so a taɓa masa FATEEMA duk da cewa tafi ƙarfin AISHA amma sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake gayamata ke 'yar ja (HUMAIRA) ki kiyayi FATEEMA, toh daga bakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam aka samo wannan laƙabin na HUMAIRA kuma matarsa AISHA yake gayama haka kasantuwarta Ja ce kuma yarinya ƙarama a wancan lokacin, to daga nan aka samo kiran duk wata me suna AISHA da wannan laƙabi na HUMAIRA, kuma babu Yadda Za a yi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya sanyawa matarsa laƙabi wanda ba me kyauba, dan haka babu wani laifi dan ancewa AISHA HUMAIRA In sha Allahu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

MA’ANAR SUNAN “HUMAIRA” DA ASALINSA (A’ISHA HUMAIRA’U)

Tambaya:

“An haifa min diya mace, an sanya mata suna Aisha. Na yi niyyar kiranta da Humaira. Amma wasu sun ce Humaira na nufin jaririn jaki. Shin haka ne?”

Amsa:

Wa’alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A’a, ba gaskiya ba ne cewa “Humaira” yana nufin jaririn jaki. Wannan zance rashim asali ne kuma ba daga Larabci ba.

Asalin Kalmar “Humaira” daga Larabci

“Humaira” (ٱلْحُمَيْرَاء) kalma ce ta Larabci daga tushen:

amrā’ (حمراء) → ja mace

Ana rage shi ta hanyar tasghir (ƙananan suna) a Larabci, sai ya koma

Humaira (حُمَيْرَاء) → ‘yar ja ko ƙaramar ja’.

Tasghir a Larabci yana nufin rage suna domin nuna:

ƙanƙanta,

ƙauna,

laushi,

ko ladabi.

Misalan tasghir:

Umar → Umair

Uthman → Uthaimin

Salaha → Sulaihah

Zaliha → Zulaihat

Saboda haka:

Hamra’u → Humaira (‘yar ja)

Wannan ba suna ne mai mugun ma’ana ba. Suna ne mai kyau, kuma na yabo.

ME YA SA AKE KIRAN A’ISHA “HUMAIRA”?

Matar Annabi , Aisha bint Abu Bakr (RA) ta samu lakabin “Humaira” daga Annabi saboda ta kasance:

tana da fatar da ta yi ja-kaɗan,

yarinya ce ƙarama lokacin da ta shiga gidan Annabi .

Akwai ruwayoyi da dama da suka nuna Annabi yana kiranta:

Yā Humairā’...”

Ke ‘yar ja...”

Lakabi ne na ƙauna, ladabi, da soyayya ta halal — ba shi da wata ma’ana mara kyau.

Saboda haka, ba zai yiwu Annabi ya kira matarsa da wani suna marar mutunci ba.

SHIN YA HALATTA A KIRA YARINYAR AI’SHA DA “HUMAIRA”?

Eh, babu laifi ko matsala ko kuskure a hakan.

Domin:

Lakabi ne mai kyau.

Asalinsa daga Larabci ne.

Annabi ne ya kira Aisha da shi.

Ba shi da ma’ana mara kyau.

Babu wata shaida da ta nuna yana nufin jaririn dabba.

A maimakon haka, lakabi ne na ɗaukaka.

KAMMALAWA

Humaira → ‘yar ja / ƙarama ja, ba jaririn jaki ba.

Lakabi ne da Annabi ya yi amfani da shi ga Aisha (RA).

Halal ne kuma babu wani abin damuwa a amfani da shi.

Za ki iya kiranta da Aisha ko Humaira, duka suna masu kyau ne.

وَاللّٰهُ أَعْلَمُ 

Post a Comment

0 Comments