Ticker

6/recent/ticker-posts

Kaffarar Rantsuwa

TAMBAYA:

Mece ce Kaffarar Rantsuwa kuma yaya ake yin ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kaffarar rantsuwa Allah ya bayyana ta a cikin fadinsa:

 لا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَكِنْ يُؤَاخِذُكُمْ بِمَا عَقَّدْتُمُ الأَيْمَانَ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلاثَةِ أَيَّامٍ ذَلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allah bazai kamaku da laifin rantsuwa da kuke yi a cikin Zancenku Na wasa, Zai kamaku da laifin rantsuwar da kuka ƙullah ne kaɗai, to irin wannan rantsuwar kaffararta shi ne: "Ciyar da Miskinai Abunci tsaka tsakiya wanda kuke ciyar da iyalanku, ko tufatar dasu, Ko 'yanta Baiwa," Wanda bai Samu ba kaffararsa shi ne Azumin kwana uku wannan shi ne kaffarar rantsuwarku idan kuka rantse ba ku cikaba, Ku kiyaye rantsuwarku kada kudinga yin rantsuwa barkatai, Haka Allah yake bayyana Muku ayoyinsa danku zama Masu godiya.

Mutum Yana da Zaɓi tsakanin Abubuwa Guda Uku:

1. Ciyarda miskinai goma, Tsaka tsakiyar Abin da mutum yake ciyarda iyalinsa, Kowanne miskini Abashi rabin sa'i na mafi rinjayen irin Abuncin da Mutanen garin suka fi ci, kamar shinkafa da sauransu, Idan kahada miskinai goma kaciyar dasu kashayar dasu ya wadatar.

2. Tufatar da Miskinai goma, kowanne miskini zakai masa tufar da zai iya sallah da ita (wadatacciyar tufa) namiji zakai Masa riga da wando, mace zakai mata Riga doguwa da kuma Hijabi.

3. 'Yanta Baiwa Mumina.

Wanda bai Samu wani Abu daka cikinsu ba, sai ya yi Azumin kwana uku Ajere..

Jamhurdin Malamai suntafi akan Bai halatta fitar da Kaffarar rantsuwa da kudi ba.

Ibun Ƙudama Allah yajikansa ya ce: Fitar da ƙimar Abunci ko tufafi da kuɗi baya isarwa ga mai kaffara, domin Allah abunci ya Ambata, kaffara ba ta samuwa sai idan da Abunci aka yita, saboda kuma Allah yabada Zaɓi tsakanin Abubuwa uku, daya halatta bayar da ƙimar ciyarwa ko tufatarwa dabai bayar da zaɓi cikin Abubuwa ukun nan ba. Al-Mugny (11/256)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments