Ticker

6/recent/ticker-posts

Goro, Amfaninsa Da Kuma Sunayen Da Ake Kiran Sa Da Shi

 A cewar binciken da aka yi, "goro" da ake magana a kai a yawancin lokuta yana nufin goron gargajiya (kola nut), ko da yake akwai wani nau'in da ake kira "namijin goro" wanda ya bambanta da shi. Goro na gargajiya shi ne wanda aka fi sani da amfaninsa ga lafiya da kuma rawar da yake takawa a al'adu.

Goro

An bayyana amfanin goro na gargajiya ga lafiya kamar haka:

· Magance ciwon kai musamman nau'in migrain

· Magance gajiya

· Rage kiba

· Kara kuzari saboda yana da sinadarin caffeine

· Hana amai da kawar da jiri

· Magance mura da sauran cututtukan da suka shafi hanci da makogwaro

· Kara karfin garkuwar jiki na jiki

Akwai kuma wani itace da ake kira "namijin goro". Ko da yake suna kama da goro na gargajiya, amfaninsa na lafiya ya bambanta. Ana amfani da shi a magungunan gargajiya don magance kumburin jiki, amma bincike ya nuna cewa bai dawo da karfin maza ba a lokacin mu'amalar aure, kuma yin amfani da shi ba daidai ba ne a nan fannin, yana iya rage yawan maniyyi.

Hanyoyin Amfani Da Goro

Mutane suna amfani da goro ta hanyoyi daban-daban domin amfanin lafiyarsa:

· Ana iya cinsa kawai ko a hade shi da tom-tom ko dabino ta hanyar niƙa su tare.·

. Don shan magani, ana iya daura ruwa a wuta sannan a daka namijin goro a zuba a ciki. Goro yana da sunaye daban-daban da ake kiran sa da shi.

WASU SUNAYE NA GORO

1. Ashaliya

2. Fari

3. Jan Fari

4. Ja

5. Tsanwa

6. Daushe

7. Dan Ankara

8. Dan Marake

9. Goron biri

10. Farsa

11. Cambe

12. Tsinta

13. Tiryasi

14. Menu

15. Marsa

16. Kurma

17. Na Gini

18. Dan Abuja

19. Kwar uku

20. Hannun ruwa

21. Goron matar Baushi

22. Goriya (namijin goro)

23. Lallen shamuwa

24. Kwaru-kwaru

25. Kwantakwaloso

26. Amangwaro

27. Saran Waga

28. Kwali

29. Sabon goro

30. Dan Ujili

31. Dan Mariri

32. Kitsen damo

33. Mai hula

34. Zuma

KIRARIN  GORO

Goro dan itaciya mai daraja.

Goro sha ruwa sha dauri.

Goro dan Ilesha dan Shagamu.

Goro bakon garin Kano dan Kurmi.

Goro daure mai daure ka ko don dole.

A birni ya ci gida, a kauye ya ci gonar gado.

Sana,ar goro ta fi aikin soja.

Tallar goro ta fi noma wahala.

In kuma anyi gardama a fara a gani.

Kowa ya ga uwar goro ya yi nisa da gida.

Post a Comment

0 Comments