Ticker

6/recent/ticker-posts

Hani A Kan Tawaye Wa Azzalumin Shugaba Ba Goyon Bayan Zalunci Ba


Hani A Kan Tawaye Wa Azzalumin Shugaba Ba Goyon Bayan Zalunci Ba

HANI A KAN TAWAYE WA AZZALUMIN SHUGABA BA YA NUNI A KAN GOYON BAYAN ZALUNCINSA

Ibnu Taimiyya (r) ya ce: 

إن الرسول أخبر بظلم الأمراء بعده وبغيهم ونهى عن قتالهم لأن ذلك غير مقدور؛ إذ مفسدته أعظم من مصلحته

مجموع الفتاوى (4/ 443)

"Lallai Manzon Allah ya ba da labarin shugabanni za su yi zalunci a bayansa, amma duk da haka ya hana yakarsu, saboda talakawa ba su da karfin yakarsa, kuma ko da suna da karfin barnar yakar tasa ta fi girma fiye da maslahar hakan".

Kuma ya ce:

كان مذهب أهل الحديث ترك الخروج بالقتال على الملوك البغاة والصبر على ظلمهم إلى أن يستريح بر أو يستراح من فاجر

مجموع الفتاوى (4/ 444)

"Barin tawaye ta hanyar yakar Azzaluman Shugabanni ya kasance shi ne Mazhabar Ahlul Hadis (Ahlus Sunna), da yin hakuri a kan zaluncinsu har zuwa lokacin da mutumin kirki zai huta ko a huta da mutumin banza".

* Ka lura da abin da ya faru a Misra. Sai kuma ka lura da abin da yake faruwa a Libya da Yemen da Syria, har yanzu sun rasa zaman lafiya, a kullum zubar da jini ake yi.

Allah ya kiyaye jinanen Musulmai.

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)


Post a Comment

0 Comments