Ticker

6/recent/ticker-posts

Gaskiya Da Fa'ida a Tsakanin Akidu

Akwai wata ka’ida da ya kamata mabiya Salaf Ahlus Sunnati wal Jama’a su sani; a lamarin Addini, babu wata kungiya ta Bidi’a da za ta kadaita da wata gaskiyan da babu ita a wajen Ahlus Sunna. Duk wani alheri a Addini da yake wajen wata kungiya ta Bidi’a, to akwai shi a wajen Ahlus Sunna.

Kamar yadda babu wata gaskiya ko alheri da yake wajen Yahudawa da Nasara face akwai shi a wajen Musulmai, to haka babu wata gaskiya ko alherin da yake wajen wata kungiyar Bidi’a face akwai shi a wajen Ahlus Sunna. Don haka duk abin da wata kungiyar Bidi’a ta kadaita da shi a Addini to ba gaskiya ba ne.

Wannar Ka’ida Ibnu Taimiyya ya karrara ta a wurare daban daban. Daga ciki ya ce:

((وكل من سوى أهل السنة والحديث من الفرق فلا ينفرد عن أئمة الحديث بقول صحيح)).

منهاج السنة النبوية (5/ 167)

((Duk wata kungiya wacce ba Ahlus Sunna da Hadisi ba, ba sa kadaituwa da wani ingantaccen ra’ayi, a ce babu shi a wajen Malaman Hadisi)).

A wani wajen kuma ya ce:

((إن كل طائفة سوى أهل السنة والحديث المتبعين آثار رسول الله - صلى الله عليه وسلم - فلا ينفردون عن سائر طوائف الأمة إلا بقول فاسد، لا ينفردون قط بقول صحيح)).

منهاج السنة النبوية (5/ 172 - 173)

((Lallai kowace kungiya wacce ba Ahlus Sunna da Hadisi masu bin Hadisan Annabi (saw) ba, ba za su taba kadaita daga sauran al’umma da wani ra’ayi ba face bataccen ra’ayi ne, kwata-kwata ba za su kadaita da ingantaccen ra’ayi ba)).

A gaba ma ya ce:

((إن كل طائفة سوى أهل السنة والحديث المتبعين لآثار النبي - صلى الله عليه وسلم - لا ينفردون عن سائر الطوائف بحق)).

منهاج السنة النبوية (5/ 177)

((Lallai kowace kungiya wacce ba Ahlus Sunna da Hadisi masu bin Hadisan Annabi (saw) ba, ba za su taba kadaita da gaskiya daga sauran kungiyoyi ba)).

Ma’ana: Ahlus Sunna ne kadai za su iya kadaita da gaskiya daga sauran kungiyoyi, ba dai a samu wata kungiyar Bidi’a tana da gaskiyar da babu ita a cikin Ahlus Sunna ba.

Saboda haka babu yadda za a yi a ce akwai wata gaskiya ko wani alheri a Addini a wajen wata kungiya ta Bidi’a alhali a ce babu shi a wajen Ahlus Sunna.

Irin Rayuwar da Muke yi a Wannan Zamani

Muna wani zamani da aka rikita abubuwa a cikinsa. An mai da Shirka ta zama Tauhidi.

An mai da Bidi'a ta zama Sunna.

An mai da wulakanta Annabi (saw) ya zama nuna son Annabi (saw).

An mai da sabon Allah ya zama kayan ado.

An mai da riko da Addini da da'a ma Allah ya zama kyauyanci.

An mai da haram ya zama halal.

Fasikan mutane fajirai azzalumai an mai da su manyan mutane masu daraja.

An mai da karya ta zama gaskiya.

An mai da zalunci ya zama adalci.

An mai da jahilci ya zama ilimi.

An mai da barna ta zama gyara.

A wannan halin muke rayuwa a yau. Duka an juya lamura saboda jahilci da son zuciya.

Mutum da sunan malumta zai fito ya fadi jahilci amma a fito ana kambama shi, wai magana ta ilimi ya fadi.

Mutum zai yi zalunci amma a daure masa gindi.

Mutum zai yi barna a bayan kasa, ya haifar da fitina a cikin al'umma amma a fito ana masa jinjina. In hukuma ta kama shi a fito ana kare shi.

Mutum zai gama barna a Gomnati, ya kwashe dukiyar kasa, amma sai ka ji ana kiraye - kirayen ya fito takaran shugaban kasa.

Kamar yadda zalunci yake cikin shugabanni haka yake cikin talakawa. Azzalumin shugaba jarabawa ne da azabar Allah ga talakawa, ko za su hankalta su koma ga Allah.

Saboda haka gaba daya rayuwar karya muke yi.

Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments