Ticker

6/recent/ticker-posts

Wacce Irin Tahiyya Kake A Sallar Ka

TAMBAYA (160)

Pls tahiya: attahiyyatulillah wassalawatu waddaiyyibah assalamu alayka.....

Da kuma Attahiyyatulillah azzakiyatulillah  assalamu alayka ayyhannabiyyu......

Pls wanne ne daidai

AMSA

Tashahhud kala 6 ne kamar yanda ya tabbata daga Sunnah. Tahiyyah irinta

1️) Nana Aisha

2️) Abdullahi Ibn Abbas

3️) Abdullahi Ibn Umar

4️) Abdullahi Ibn Mas'ud

5️) Abu Musa al-Ash'ariy

6️) Umar Ibn al-Khattab

Wadda ka turo itace irin Tahiyyar Abdullahi Ibn Mas'ud da Abdullahi Ibn Umar da mahaifinsa da Kuma Abu Musa al-Ash'ari

Ta biyun Kuma mai lafazin "Azzakiyatulillah..." itace Tahiyyah irin wadda Annabin Rahama Sallallahu alaihi wasallam ya koyawa Uwar Muminai Sayyada Aisha

Allaah ya qara musu yarda baki dayansu

Muhallish shahid dai shine: Dukkansu sun tabbata daga Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam Kuma an so ka dinga kowacce cikin 6 din domin koyi da Sunnonin gaba daya

Duba: littafin Ibn Abi Shaybah (1/293), al-Saraj, al-Mukhillas, da Kuma Bayhaqi (2/144)

Tahiyyar da na fi yi, itace

اَلتَّحِيَّاتُ ِللهِ وَالصَّلَوَاتُ والطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ  أَيُّهَا النَّبِيُّ  وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُه .

"Attahiyyatu lillahi wassalawatu wattayyibat, assalamu alayka ayyuhan-nabiyyu warahmatul-lahi wabarakatuh, assalamu 'alayna wa'ala ibadil-lahis-saliheen. Ash-hadu an la ilaha illal-lah, wa-ashhadu anna Muhammadan 'abduhu warasooluh."

Ma'ana

Dukkan nau'in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.

Karin bayani Kuma zai zo filla filla a cikin karatun da muka Fara last week na littafin GYARAN SALLAH da sauransu

Mai buqatar shiga USMANNOOR ONLINE ACADEMY, sai yayi magana ta private don kada karatun da muka fara yayi maka nisa

Wallahu taala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments