Citation: Ahmad, A. A. (2024). Nuta Cikin Tarihin Alƙalin Lardin Sakkwato Mallam Yahya Nawawi (1897-1979). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa,6-17. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.002.
Nuta
Cikin Tarihin Alƙalin Lardin Sakkwato Mallam
Yahya Nawawi (1897-1979)
Aliyah
Adamu Ahmad (Mrs)
08133314217, 08095059926, aliyaadamu@yahoo.com
Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Jihar Sakkwato
Tsakure: Tunanin shirya wani kundi wanda zai ƙunshi maƙalu na ilmi
domin ciyar da bincike gaba, musamman kan adabin Hausa ya taso ne a wani zaman
liyafar cin abinci da aka yi a harabar Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato ranar 15 ga Maris,` 2023 daga ƙarfe 7-10 na dare. Wannan liyafa an shirya ta ne domin karramawa ga
Farfesa Abdullahi Bayero Yahya. Shi kuma Farfesa Abdullahi Bayero ya cika
shekaru saba’in a wannan lokaci saboda haka ya rubuta takardar aje aikin jami’a
a matsayin mai ritaya. Wannan nasara ta cimma shekaru saba’in da yin ritaya,
ita ce dalilin shirya walima domin girmamawa da taya murna gare shi. Wannan
kuma ita ce damar da na samu na shiga sahun sauran ɗalibai wajen rubuta muƙala kamar
yadda hakan ta kasance.
Gabatarwa
Wannan muƙala
za ta yi tsokaci kan rayuwar Mallam Yahya Nawawi Alƙalin Lardin Sakkwato[1]. Ƙumshiyar muƙalar
za ta haɗa da nasabarsa wato asalin mahaifansa da kuma sharhi kan
gudummuwarsa ta ilmi da kuma ayyuka irin na hidima ga al’ummarsa a lokacin da
yana raye. Tambayar da za ta biyo baya ganin wannan take kan marigayi Alƙalin Lardi Yahya Nawawi ita ce, shin me zai hana a yi rubutu
kan Farfesa Abdullahi Bayero, ganin cewa shi ne ake shirya kundi domin karrama
shi, a maimakon mahaifinsa? Amsa a nan ita ce, da yawa za a yi rubutu kan
Farfesa Abdullahi Bayero, musamman kan gwarzontakarsa a fagen waƙa. Kuma wasu za su yi rubutu kan tarihin rayuwarsa da
ayyukansa ga jama’a da jiharsa. To ita wannan muƙala tana son ta tono dalilan shaharar Abdullahi Bayero
Yahya, domin Barewa ba ta yin gudu, ɗanta
ya yi rarrafe, sai dai shi ɗan ya zama mai
gudu irin uwarsa Barewa, har ma ya haɗa da
tumamaye (tsalle) wajen gudunsa. An nemi malaman da suka san Malam Yahya Nawawi
waɗanda suka rage a raye, aka tattauna da su domin samun
ingantattun bayanai a kansa. An kuma nemi iyalansa waɗanda suka haɗa da ‘ya’yansa, da
matarsa da ke raye, aka tattauna da su. Akwai kuma fayil-fayil waɗanda suka ƙunshi
bayanai kan rayuwarsa da ayyukansa da ke hannun iyalansa da kuma cibiyar adana
tarihi ta Waziri Junaidu History and Culture Bureau, waɗanda aka yi nazari a cikinsu. Da waɗannan bayanai da aka tattara kamar yadda aka ambata, aka duƙufa wajen rubuta wannan muƙalar.
Shehu Usmanu bn Fodiyo Uba ga Malam Yahya Nawawi
Haihuwa
Tabbas an haifi Malam Yahya Nawawi cikin ƙarni na goma sha tara (Ƙ.19). Sai dai, kamar ga mafi yawan mutanen ƙasar Hausa kafin zamanin da muke ciki, inda gizo ke saƙa shi ne sanin takamaiman kwanan watan da aka haifi wannan
bawan Allah. Bayanan da aka samo sun haɗa da
sheka ta 1897, da 1899 da 1886. Haka kuma ta la’akari da sanannun bayanan
ayyukan tarihi ana iya cewa ko da Turawa suka ci birnin Sakkwato a 1903 Malam
Yahya Nawawi yana duniya, kuma ya girmi wasu ‘yan’uwansa da aka haifa kamar
Waziri Junaidu (ƙanin mahaifinsa).
To amma shekarar da ɗaya daga manyan ‘ya’yansa, Alhaji Abbas Yahya, ya bayar kuma
Buhari (2014:689, 693) ya ruwaito, (1899) ba za ta fi kusa da daidai ba.
Dalilin cewa haka shi ne sanin cewa an haifi babban ɗan Yahya Nawawi, wato Usman Shehu Yahya Nawawi, a 1923[2].
Abin da aka sani ne kuwa cewa mafi rinjayen lokutan da aka fi yi wa ‘ya’ya maza
amre a ƙarni na 19 a nan ƙasar Sakkwato, har ma a farko-farkon ƙarni na 20, shi ne lokacin da matashi ya kai shekaru 20 zuwa
25 na haihuwa. Mai wannan muƙala
ta ɗauki 1897 saboda yin la’akari da lokacin da aka haifi babban
ɗan Nawawi, Usman Shehu, 1923 na nufin Malam Yahya yana da
shekaru 26 na haihuwa ya yi amre. Wannan ra’ayi yana ƙarfafa idan aka yi la’akari da al’adar da aka ambata ta yi
wa ‘ya’ya amren fari a zamaninsu. Da an samu kai ga hirar da gidan rediyon RIMA
ya yi da Yahya Nawawi da watakila duk wannan ka-ce-na-ce bai taso ba. To amma
kash!, Abdullahi Bayero Yahya ya shaida wa mai wannan muƙala cewa ya yi ƙoƙarin da zai samun
wannan hira daga RIMA Rediyo amma a lokacin bayan da aka yi gobara da shekaru
da yawa a kafar labaran ne, kuma kafar ta sanar da shi la’alla har da faifan da
aka naɗa hirar ne gobarar ta cinye. Allah ne Masani.
A dai garin Wurno ne aka haifi Malam Yahya Nawawi kamar
yadda ‘ya’yansa da littaffan tarihi suka bayyana. Iƙirarin da kan batun ke cewa, “Shehu Usmanu bn Fodiyo Uba ga
Malam Yahya Nawawi”, take ne zai jawo hankalin mai karatu kan yaya za a yi
Shaikh Usman bn Fodiyo ya zama uba ga Malam Yahaya Nawawi. Amsa a nan mai sauƙin fahimta ce, domin a fahimtar Bahaushe, kaka ga mahaifinka
shi ne uba na biyu gareka. Ƙarin
bayani kan hakan shi ne, idan mutum ya haifi ɗa
to ɗansa ne, idan ɗansa
ya haihu, to ya samu jika, ko aboki. Idan jikansa ya haihu, to ya samu wani ɗa, a wata Hausa ana cewa kama-kunne. Kama-kunne idan ya samu
ɗa, ana kiran wannan tattaɓa-kunne.
Idan kuwa tattaɓa-kunne ya haihu, an samu taka-kushewa! Hausa harshe ne mai
tarin kalmomi da ma’anonin da sai an fassara wa Gwari da bai iya gane abin da
ake nufi, duk da ko Alhaji Garba Gwandu (GG) ya ce,
Ga sauƙin koyo nan da nan
A cikin sati huɗu sai
ka san
Halshen Hausawa sai kaɗan
Ka ɓace maka ko an lafatan
Naki ko ƙunduƙushariya/!!
(ayar motsin rai ta mai muƙala ce)
(Alhaji Garba
Gwandu:Waƙar Ƙongiyar Hausa ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo)
Taswirar da ke biye ta tabbatar da wannan bayani kan tushen
Malam Yahya Nawawi. A lissafin da ya bayyana ta wannan taswirar da ke biye,
Yahya Nawawi hula huɗu ce tsakaninsa da Shehu Usmanu bn Fodiyo; hula uku
tsakaninsa da Nana Asma’u ‘yar Shehu Usmanu. Ahmadu ɗan Nana-Asma’u shi ne jikan Shehu Usman bn Fodiyo. Idan ana
son a waiwayi tushe na iyaye dangane da Mallam Yahya Nawawi daidai yake da
neman tarihin malaman Jihadi na daular Usmaniyya. Tarihin Malaman Jihadi bai taɓa samun surki ba. Tarihinsu ya sha ambato a hannun malamai
da marubuta tarihin daular Usmaniyya, kuma an yi ittifaƙi a kan tarihin. (Farfesa Sani Zaharaddin da Farfesa A.A.
Gwandu da Malam Muhammadu Isa Talata Mafara da Farfesa M.M. Gwadabe da Dr.
Usman Bugaje, kaɗan ne daga misalan manazarta).
Nasabar Yahya Nawawi Alƙalin
Lardi
Sharhi a kan Taswira
Malam Yahya Nawawi (Alƙalin Lardi) ɗa ne ga Waziri
Abdulƙadir Macciɗo, ɗan Waziri Buhari, ɗan Ɗangaladima Ahmadu, ɗan
Nana Asma’u[3]‘yar
Shehu Usman bn Fodiyo (Rahimahullahu amin). Taswirar ta sake tabbatar da
bayanan da suka gabata.
Dalilin Sunan Yahya Nawawi
Mahaifin Malam Yahya Nawawi shi ne Abdulƙadir Macciɗo. Sarakuna har
uku a Sakkwato ya yi wa wazirci. Ya yi wa Sarkin Musulumi Muhammadu Attahiru II
(1903-1915), da Muhammadu Maiturare (1915-1924) da kuma Muhammadu Tambari
(1924-1931). Haka kuma shi ne shugaban masu zaɓen
Sarki. A lokacin da Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare ya rasu, Turawan Mulkin
Mallaka sun tilasta wa wannan kwamiti na zaɓe da
Macciɗo ke jagoranta amincewa da Muhammadu Tambari (maimakon Hasan
ɗan Mu’azu da yake shi ne zaɓin
kwamitin) da ya kasance shi ne Sarkin Musulmi (1915-1924)[4].
Waziri Macciɗo masanin shari’ar
musulunci ne domin yana gabaci a hukunce-hukunce na shari’a tun ma ba duk wani
al’amari na rabon gado a yankin Sakkwato. Malam Abdulƙadir Macciɗo yana daga cikin
mashahuran malaman Hadisi daular Usmaniyya. Saboda soyuwarsa da nazari a cikin
litattafan Hadisi, ya ƙaunaci Shaikh
Sharifuddin marubucin littafin nan na Arba’una Hadisi. Ya shahara ne wajen
tattara Hadisai, ga shi kuma matashi mai ƙarancin shekaru. Cikakken sunan mawallafin littafin Hadisai
na Arba’una shi ne Abu Zakariyyah Yahya bn Sharaf Al-Nawawi (631-676 H). Shaikh
Nawawi mutumin Damaskas ne, sunan ƙauyensu Nawa[5].
Ya shahara wajen nemo ingantaccen Hadisi daga manyan sahabai da tabi’ai, ya
rubuce Isnadinsu domin adana tarihi.
Ya yi suna a duniya kan Hadisi, kuma ya bar duniyar yana ɗan shekaru Arba’in da biyar (45)[6].
Soyuwar Abdulƙadir Macciɗo ga Sharaf al- Nawawi, shi ya sa bayan an haifi Yahya,
lokacin da za a raɗa masa suna sai mahaifinsa ya riƙa kiran ɗansa da laƙabin Nawawi. Tun wannan lokacin aka riƙa kiran wannan ɗa na
Waziri Abdulƙadir Macciɗo da Yahya Nawawi, ko Nawawi kai tsaye ga manya da
sa’o’insa.[7]
Shi kansa yakan rubuta sunansa da ‘Yahya Nawawi’ a wasu rubuce-rubucensa.
Mahaifan Yahya Nawawi
Sunan Mahaifinsa Abdulƙadir Macciɗɗo[8]ɗan waziri Buhari ne. Uba malamin ɗansa ne, wato Buhari malamin Abdulƙadir ne. Kuma dukkaninsu sun zama mashahuran malamai kafin
wafatinsu. Malam Ahmadu mijin Faɗimatu
da Malam Abubakar Bube suna daga cikin malamansa, kuma su waɗannan malamai shahararsu ta karaɗe ƙasashen da ke ƙarƙashin daular
Usmaniyya ta yanzu saboda yawon neman ilmi da kuma yaɗa ilmin. Abin da wannan ke nuni shi ne kakan Yahya Nawawi
Malam Buhari Shaihi ne, kuma ‘ya’yansa kamar Waziri Abdulƙadir Macciɗo da Waziri
Junaidu sun gado shi, kusan dukkaninsu shaihunai ne waɗanda kuma Yahya Nawawi yana daga cikin jikokinsa. Sauran ɗiyan Abdulƙadir
Macciɗo akwai Malam Buhari Joɗi
wanda riƙaƙƙen mai tafsiri ne kuma mai kaifin ƙwaƙwalwa da har akan
ce tafsirin Jalalaini da Diya’ut Tawil fi ma’ani –l Tanzil ga kansa suke.
Sauran sun haɗa da Alƙali
Bello Giɗaɗawa (Ɗangaladiman
Waziri) kuma sanannen marubucin waƙa, shugaban Ƙungiyar
Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa na farko kuma mawallafin littafin da ake kira Bargon Hikima, da Alƙali Ahmadu Ɗantsoho,
da Malam Isa, da Lamiɗo Abdurrahman Sayuɗi, da
Muhammad Attahiru, da AlHassan, da Idirisu, da Abubakar, da Muhammadu da Malam
Halliru, da Malam Abubakar. Daga cikin ‘ya’yansa mata kuwa akwai Aminatu
(Kura), da Nana Asma’u (Dumukku) da Khadijatu, da Faɗimatu da Hafsatu (matar Sardauna Ahmadu Bello Firimiyan
Jihar Arewa ta Najeriya)[9],
da Aishatu (Giwa), da Maryamu (Daje)[10] Waɗannan su ne ‘ya’yan waziri Macciɗo har da Yahya Nawawi wanda yana daga cikin manyan
‘yan’yansa.
Mahaifiyar Yahya Nawawi ita ce Maryamu. Ta yi karatu a
hannun mijinta Waziri Abdulƙadir
Macciɗo. Ta yi litattafan addini masu yawa. Tana daga cikin
matansa waɗanda suke taimakawa wajen koyar da yara karatun allo a cikin
gida, a zamaninta. Malam Yahya ya samu horo mai kyau da tarbiya irin ta
makarantar allo tun a wajen mahaifiyarsa. Ana iya cewa mahaifansa biyu su ne
suka fara ba shi tarbiyya ta gari.
Malam Yahya Nawawi ya auri Khadijatu ‘yar Malam Basharu ɗan Wali Usman ɗan
Waziri Abdlƙadir ɗan Waziri Usman Goɗaɗo mijin Nana Asma’u ‘yar Shehu Usmanu ɗan Fodiyo. Har ila yau ita Khadijatu matar Malam Yahya
Nawawi ɗiyar Ramatu Hinnaye ce matar Malam Basharu kuma ɗiyar Waziri Buhari, kuma ƙaunar Abdulƙadir
Macciɗo mahaifin Malam Yahya Nawawi. Saboda haka da shi Nawawi da
Khadijatu kakansu guda, a yayin da kuma suka haɗa
kakanninsu suka dangana zuwa ga Waziri Usman Giɗaɗo mijin Nana Asma’u ɗiyar
Shehu ɗan Fodiyo. A taƙaice da Khadijatu da Nawawi auren zumunta ne suka yi. Su ne
suka haifi Abdullahi Bayero.[11]
Ƙuruciyar Yahaya Nawawi (1897-1927)
A ƙarƙashin wannan taken za a dubi shekarun farko kimanin talatin
(30) na rayuwarsa da yadda ya samu tarbiya ta rayuwa da ta ilmi daga wajen
mahaifansa da malamansa na karatun zaure.
Tarbiyyarsa
Tarbiyyar da Nawawi ya fara samu bayan reno na jarintaka ita
ce nuna masa muhimmancin Addinin Musulunci. Wannan kuwa iyayensa sun cusa masa
ita ta hanyoyin ganin iyaye suna aikata ibada, da koya masa salla da ganin da
yake yi mahaifansa suna karatu da karantarwa; mahaifiya tana karantar da
yayyensa da wasu yara; mahaifi ko yana karantar da yayyen Nawawi da kuma manyan
mutane idan suka zo nan gidansu.Haka kuma mahaifiyarsa, Maryam, da yannensa
sukan koya masa yadda ake salla; mahaifiya ita ce ta farko sannan yannensa idan
suka ga yana koyon yadda mahaifiyar ta koya masa, ko suka ga yana kwaikwayon
su. A wannan gefi sai Nawawi ya samu muhimman ɓangarorin
tarbiyyar Musulunci, wato da karatu da ibada. Baicin waɗannan akwai ladubba kamar girmama na gaba, da sanya sutura
da cin abinci da shan abin sha da makamantansu. Haka kuma da yake mahaifinsa,
basarake ne, wato waziri, ba zai rasa samun tarbiyyar hulɗa da jama’a ba, cikin gida da waje. A taƙaice Malam Yahya Nawawi ya buɗe
ido da ilmi domin gidansu na ilmi ne. Wannan kuwa haka aka sanar wa shiyyar Giɗaɗawa tun daga kakanninsa, Waziri Buhari, har zuwa ga Waziri
Usman Giɗaɗo wanda daga sunansa ne shiyyar ta samo sunanta, da Nana
Asma’u, da mahaifinta Shehu aUsmanu ɗan
Fodiyo.
Karatu a Gida da Makarantar Zaure
Malam Yahya ya fara
karatun allo a gida wajen mahaifansa guda biyu wato Waziri Abdulƙadir Macciɗo da Modibbo
Maryamu. Daga bisani ya fara zuwa wajen wasu malamai a makarantunsu kamar Abdulƙadir Macciɗo Limamin
Masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, da Malam Bube da Malam Muhammadu da
Modibbo Faɗimatu. Malam Yahya ya fara shiga sahun manyan ɗalibai waɗanda ake iya bai
wa ƙananan ɗalibai
su fara koya musu karatu. Wannan aiki yana fuska biyu, koyon aikin malanta da
kuma taimaka wa manyan malamai wajen tarbiyantar da ƙananan ɗalibai. Idan aka
samu sallamar ƙanana waɗanda ba su buƙatar dogon lokaci saboda shekaru, sai manya irinsu Yahya
Nawawi su zauna su fara ɗibar nasu ilmin wajen Malami mai makaranta zuwa lokacin da
mutum ya gamsu da abin da ya samu a wannan ranar. Haka nan kuma a wannan
mataki, Malam Yahya ya samu ilmi na litattafai a wajen Malam Ubandoma[12]
da Liman Abdulƙadir Macciɗo[13].
Halayensa da Sha’awarsa
Malam Yahya Nawawi yana son zaman majalisi biyu: Zaman
karatu a gaban malamansa da zaman yanke hukunci idan ba a makaranta ko wurin
aiki yake ba; yin karatu idan a gida yake ba tare da waɗanda suka kawo masa ziyara yake ba, mutane daga waje ko
‘ya’yansa, ko kuma ba salla ko azkar yake ba. Kusan duk inda za ka gan shi a
zaune cikin mutane to irin waɗannan majalisai
ne. In ba haka ba, shi ma’abucin zama gida ne riƙe da littafi koyaushe. Abin da Malam Ibrahim ya shaidar shi
ne, babu abin da ke raba Malam Yahya Nawawi da littafi sai salla ko zikiri ko
zama da ‘ya’yansa ko idan aka kai masa ziyara ta zumunci ko neman karatu. Sai
kuwa bacci in ya kama[14].
Halayyarsa ta fuskar abinci kuma ita ce, shi a koyaushe ba
ya son cin abinci mai yawa, ko abinci mai nauyi. ‘Ya’yan itace ne ya fi so, da
zuma. Iyalan Malam Yahya Nawawi sun shaidar da ba ya shan ruwa sai waɗanda aka tafasa suka huce, sai a zuba cikin abu mai marfi
kamar buta, yana riƙa sha. Amma duk ƙishirwa sai an dafa ruwa sannan zai sha. Malam Yahya bai cin
abinci mai maiƙo ko yaji. Ba ya
cin abincin da aka dafa da man gyaɗa ko
aka saka twanka (barkono)[15].
Iyalansa sun shaidar bai cika cin abinci daga wani wuri ba, sai kuwa idan
‘ya’yansa sun dafo sun kawo masa saboda sun san irin abincinsa. Wannan bayani
ya nuna irin yadda Malam Yahya ke bai wa lafiyarsa muhimmanci. Idan tafiya zai
yi to lalle akwai butoci kamar uku zuwa huɗu a
tafiyar, ɗaya wadda aka saka ruwan da aka tafasa, ɗaya wadda yake lalura da ita kamar kama ruwa ko alwala, ɗaya wadda aka saka masa goron da yake ci a yayin da ɗaya kuwa ake saka masa hura. Waɗannan suna daga cikin guzurin duk tafiyar da zai yi mai
tsawo. Idan ma tafiyar wadda ke ɗaukar
kwanakki ce, yakan tafi tare da ɗaya
daga cikin matansa.
Wani abin da iyalansa ke tunawa na game da shi kan abinci
shi ne, shi mai son dabino da madara ne, kuma yana samun gamsuwa da su kaɗai, domin idan ya ci dabino ya sha madara da zuma, to yana
iya wuni bai nemi abinci ba. “Ku ci abinci don ku rayu, kada ku rayu don ku ci
abinci”[16],
wannan wata maganar hikima ce da Malam Yahya Nawawi ke nuna wa iyalansa da
cewa, kada mutum ya zama bawan ciki, wanda koyaushe abinci yake nema don ya
cika ciki ya kwanta. Amma mutum ya nemi abinci mai kyau ya ci domin lafiyarsa
ta inganta, ya samu ƙarfin amfanar da
kansa da al’umma. Idan ya samu abinci mai gina lafiya, to yana iya neman ilmi,
ya kuma koyar da ilmi.
Dangane da halayen Yahya Nawawi ga kaɗan daga waƙar
da Alƙali Haliru Wurno
ya faɗa:
3. Tuna ka nikai ammu ƙul
Yahya
Ƙadi na Lardi fa don
ku jiya
Tunawa nikai ko dare safiya
Da halinsa mai kyau halin anbiya
Bale dai yinin nan da zai tafiya
4. Shina la’asar yai sujuda jiya
Nan Rabbuhu yak kirai Yahaya
Da tsarkin hali na jiki zucciya
Da
tasbihu yab bar gidan duniya
Ilahi
ka sa ya gama lafiya (Ya Rabb ka gafarta
masa, amin)
5. Daɗai bai
ɗumin hira illa sani
Na tafsiru kullum mutum ya gani
Bai batsa ko dauri bai lahani
An san shi bai bin hawad dut wani
Ya karkace
hanya ya ce anniya
6. Ibada yakai ko ga hanya tafe
Bai dube-dube idonai kife
Bai yin fululu bale rattafe
Ɗumin Yahya ba da ilmi ɗafe
Da yin
gargaɗi ga zama lafiya
7. Ya wuce tsarassa ilmi kuma
Da yannai da ƙannensu bai da kama
Daɗai Yahya yanke bai fankama
Bale tafiya ba shi yin taƙama
Ba shi kula
don abin duniya
(Alƙali Alhaji Haliru
Hurno: Marsiyyar Mallam Yahya Nawawi Giɗaɗawa)[17]
Ayyukan Alƙalin Lardi Malam Yahya Nawawi a Wasu Hukumomi da Tarurruka
Malam Yahya ya yi ayyuka da dama da suka taimaki al’ummarsa.
Da farko dai malamin sani ne da ya karantar da ɗalibai
da dama. Daga cikin ɗalibansa akwai Malam Haliru Giɗaɗawa Alƙalin Wazirin
Sakkwato da Malam Abdullahi Jatau Giɗaɗawa. Haka kuma daga cikin ɗalibansa
akwai waɗanda suka kai matsayin manyan malamai mashahurai kamar
Waziri Junaidu da Malam Haliru Binji da makamantansu[18].
Ta fuskar ayyukan hukumomi ya karantar a makarantar Midil da
yanzu ake kira Kwalejin Nagarta daga 1917 zuwa 1931. A 1931 sai aka yi masa
sauyin wurin aiki zuwa makarantar koyar da aikin alƙalanci ta Sakkwato, wato Khad School ko Kadi Sukul a
Hausance. A lokaci guda kuma ya karantar a makarantar mata wadda a yanzu ake
kira Government Girls College, Sokoto. A 1942 sai aka yi masa Wali na kotunan ƙasar Sakkwato, wato Lardin Sakkwato daga 1942 zuwa 1954.[19]
A wannan shekarar ce ya zama Babban Alƙalin Lardin Sakkwato a ƙarƙashin En’e (N.A.)
ta Sakkwato. Wannan muƙami ya shafi
kotunan da ke ƙarƙashin En’e ta Sakkwato. Malam Yahya Nawawi yana a wannan
matsayi daga 1954 har zuwa 1960, lokacin da aka ba shi makamancinsa amma a ƙarƙashin Gwamnatin
Jihar Arewa. Matsayin shi ne Alƙalin
Lardin Sakkwato na ita gwamnatin, a turance Provincial Judge. Lardin Sakkwato
ya ƙunshi ƙasar Sakkwato da ta Gwandu da ta Argungu da ta Yawuri. Duk
dai yana riƙe da wannan muƙami aka yi masa muƙamin ɗaya daga cikin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara ta Musulunci ta Jihar Arewa da ke zama a Kaduna.
A tsawon sheksarun nan da ya yi yana aiki na hukumomin En’e
da Gwamnatin Jihar Arewa, Malam Yahya Nawawi ya kasance mai gabatar da tafsirin
Alƙur’ani mai tsarki a Masallacin Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello cikin watan Ramadana. Abdullahi Bayero ya shaida wa mai
wannan muƙala cewa ya taɓa jin mahaifinsa yana ba wani daga masu ziyartar sa cewa shi
har ya aje aikin hukuma yakan yi hutun shekara-shekara cikin watan Ramadana.[20]
Wannan lamari ne da ke nuni da cewa Malam Yahya mai tsara harkokinsa ne domin
gudun su ci karo da juna. Bai bar aikin hukuma ya ci karo ko ya hana shi yin
aikin da ya jiɓinci na Addininsa ba. Haka kuma tsarin yana nuni da cewa
Malam Yahya yakan yi hutun shekara-shekara ba don ya huta ba, sai don ya yi
wani babban aiki.
Halin Yahya Nawawi ne
na tsayawa a kan ayyukan magabata ta fuskar Addinin Musulunci. A kan haka ne
tafsiri da yake gabatarwa a Masallacin Muhammadu Bello da ke a garin Sakkwato,
ko ma a ko wane wuri ne ta kama to littaffan magabata na Sunnah yake tsayawa a
kansu. Misalan waɗannan ayyuka na magabata sun haɗa da tafsirin Jalalaini da na Abdullahi ɗan Fodiyo, Diya’ut Tawiil da sauransu. Shi bai rubuta
tafsiru ba amma ya karantar da tafsiran da magabata suka rubuta. Cikin harshen
Hausa yake gabatar da tafsiru. Haka kuma kamar wada ya gabata Yahya Nawawi ya
koyar da hanyar yin Tafsiru.
A shekara ta 1967 sai Malam Yahya Nawawi ya aje aiki don
ra’ayin kansa.[21]
Abin tunani shi ne Malam Yahya Nawawi ya aje aikin gwamnati wanda ya yi shekru
50 yana yi, to haka ɗansa da wannan muƙala ta shiga cikin karrama shi, wato Abdullahi Bayero Yahya,
shi ma hamsin ɗin ya zuba wa gwamnati sannan ya aje aiki! Watakila da sani
ne ɗan Barewa ya yi gudu kamar mahaifiya!!
Ayyukansa na Bayan Ritaya Gwamnati
Malam Yahya Nawawi ya aje aikin Gwamnati a shekarar 1967.
Sai dai bai kwanta ba kamar yadda kalmar Turanci ta ‘retire’ ke nuni. Malami
ne, malami ko na Musulunci ba hutu yake yi ba. Karantarwa bai bari ba. Ya ci
gaba da wannan ta fuskoki da dama. Yana aje aikin gwamnati sai nan take
Jama’atu Nasril Islam, reshen jihar Sakkwato ta naɗa shi shugaban masu wa’azu saboda sanin da aka yi masa ba ma
a wannan fage ba, har a fagen shari’a da karantarwa.
Haka nan kuma Sarkin Musulmi Abubakar III ya kafa wata
makaranta a nan cikin fadarsa da ake kira Ma’ahadul Ilmi, aka naɗa Malam Yahya Nawawi shugabanta. A wannan makaranta mai
matsayi daidai da abin da ake kira “Academy” a Turance, ana horar da ɗalibai ilmi da tarbiyyar yin wa’azi da kuma na tafsirin Alƙur’ani mai tsarki. Ya riƙe wannan matsayi na Shugaban masu Wa’azu da Jama’atu Nasril
Islam da kuma na Shugaban makarantar Ma’ahadul Ilmi da ke gidan Sarkin Musulmi
Abubakar III har zuwa wafatinsa ranar Assabar 22 ga watan Disamba na shekarar
1979. Allah Maɗaukaki ya yi masa rahma, amin.
Malam Nawawi ya kasance malami mai yin tafsiri a masallacin
Muhammadu Bello a duk lokacin azumin watan Ramadana. Haka kuma ya sha yin
wa’azi a duk ranar Mauludi a makarantar Nizamiyya ta Sakkwato. Mafi yawan
wa’azinsa a wannan rana yakan shafi ire-iren matsalolin da al’umma ke fuskata a
lokacin, kamar matsalar ganin wata da tawassuli da usulud Dini da makamancin
haka.
Malam Yahya Nawawi babban malami wanda saboda yawan ilminsa
da adilcin da aka san shi da su aka kuma yarda da shi, ya kai har yakan wakilci
Sarkin Musulmi Abubakar III ko Waziri Junaidu a wasu tarurruka, ko ya jagoranci
wasu kwamitoci masu sarƙaƙiya. Idan kuma Sarkin Musulmi ko Wazirinsa, Junaidu, suka sa
shi irin waɗannan ayyuka, to zai yi tsakaninsa da Allah Mahalicci.
Misali, Sarkin Musulmi ya taɓa sa shi ya
binciki musabbabin wani rikici da ya haɗa
mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya da ta Tijjaniyya a garin Gusau. Malam Yahya Nawawi
ya gudanar da wannan bincike ya kuma miƙa sakamakon binciken ga Majalisar Sarkin Musulmi. Ya dai
gudanar da binciken a shekara ta 1949, wato lokacin da yake a matsayin Walin
Sakkwato. Mafi yawan mutanen ƙasar
sun ɗauka cewa ɗariƙar Ƙadiriyya ce Nawawi
zai ba gaskiya a wannan bincike saboda ganin cewa ɗariƙar ce Sarkin
Musulmi da ilaharin’yan majalisarsa da mafi rinjayen talakkawan ƙasar Hausa ɗariƙar da suke bi a zamanin. A dalilin haka ne ma a wancan
zamani idan Sarkin Musulmi ya ba da umurnin wata sanarwa ga jama’a, misali
sanarwar ganin wata, to mai shela kan zagaye gari yana yin wannan sanarwa. Zai
fara da cewa, “Kuna jiyawa Ƙadirawan
Shehu! Sarkin Musulmi ya gaishe ku!” Daga nan sai ya faɗi saƙon Sarkin Musulmi.
Wannan ne dalilin da ya sa jama’a suka ɗauka
cewa mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya wannan kwamitin bincike da Sarkin Musulmi ya naɗa rufa-rufa ne kurum aka yi, ɗariƙar Ƙadiriyya kwamitin
Nawawi zai ba gaskiya. To amma ba haka ta kasance ba, domin kuwa Malam Yahya
Nawawi ɗariƙar Tijjaniyya ya
ba gaskiya, ya kuma ce dole a biya ta hasarar da ta yi na rushe mata masallaci
da mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya suka yi.
Wallafe-wallafen Malam Yahya Nawawi
Ayyukan Malam Yahya Nawawi sun fi ƙarfi a fagen Tauhidi da Fiƙihu. Ya yi rubuce-rubuce a sauran fannoni kamar na adabi
musamman waƙa da kuma tarihi.
Tauhidi ne da Fiƙihu da ilmin
shari’a ya fi mai da hankalinsa. Waɗannan
kuwa suna ɓuɓɓuga ne daga Alƙur’ani da tafsirinsa. Tafsiri kuwa da shari’a ilmi ne da aka
shaidar da ƙwarewar Malam
Yahya Nawawi a kai.
Daga cikin ayyukansa 14 waɗanda
Abdullahi Buhari ya kawo cikin littafinsa, Intellectual
Foundation of Sokoto Caliphate, uku ne za a iya cewa ba su kai ga lurar
marubucin ba. Aiki na ɗaya shi ne tarin shari’o’in da Malam Yahya Nawawi ya yanke a
lokacin da yake alƙali a matakai
daban dabam da aka ambata cikin littafin Abdullahi Buhari da kuma cikin wannan
muƙala[22]. Tsawon
lokacin da ya shuɗe, da rashin na’urorin zamani a lokacin da Nawawi ya yi alƙalanci, da kuma matsalolin da ke tattare da samun
rubuce-rubucen hukuma idan mai bincike na ƙoƙarin samo su, da
kuma uwa uba ɓarnar da gobara da canje-canjen wuraren adana kaya, duk masu
yin tarnaƙi ne ga mai
gudanar da bincike. Wallafa ta biyu da Nawawi ya yi ita ce tarjamar da ya yi wa
littafin Usulud Dini cikin harshen Hausa wanda Shehu Usmanu ɗan Fodiyo ya rubuta. Abin mamaki ne a ce Abdullahi Buhari
bai ambaci wannan aiki ba duk kuwa da cewa littafin ya watsu. Ibrahim Yaro
Yahaya ya kawo sunansa cikin littafinsa, Hausa
a Rubuce… (1988). Haka kuma akwai
nasihar da Nawawi ya bai wa kwamitin da Sarkin Musulmi Abubakar III ya kafa har
wannan kwamiti ya buga nasihohin da malaman da ya tuntuɓa, ciki har da ta Nawawi. Kwamitin ya sanya wa littafin da
ya buga sunan, Nasiha Ga Musulmi.
A ganin wannan marubuciya abu ne da ya dace a tattaro
hukumce-hukukumcen da Malam Yahya Nawawi ya yanke a lokacin alƙalacinsa, aikin da in sha Allahu marubuciyar ke a kan yi.
Haka kuma ya dace a bibiyi laccocin wa’azi da Nawawi ya gabatar a tarurrukan
Maulidi da ya halarta don a taskace su don amfanin ɗalibai. Abdullahi Buhari ya kawo sunayen wasunsu kamar
Durratu Ahlus Sunna.
Akwai wasu ayyukan Nawawi na tarihi waɗanda mai muƙala
ta samu gani guda biyu ne: da Akhbaru Biladil Hausiyyat was Sudaniyyat wa ɗarfi akhbari Muluukiha was Salaaɗiiniha. Wannan littafi ne mai tsawon shafi 46 a kan tarihin ƙasar Hausa da sauran ƙasashen da ake kira Sudan dangane da sarakunan ƙasashen. Ya wallafa shi cikin harsunan Larabci da Hausa,
kamar yadda ya fi yi a rubuce-rubucensa. Ya rubuta wannan littafi, kamar yadda
ya faɗa ciki, domin Sarkin Musulmi Abubakar III, abin da ke nuni
da cewa an rubuta shi domin ya yi wa Sarkin Musulmi nuni ga yadda tarihin ƙasar ya kasance, da kuma yanzu da ƙasar take ƙarƙashin ikonsa. Littafin an rubuta shi cikin sigar wasiƙa zuwa ga Sarkin Musulmi domin haka ya faɗa a sakin layin farko cewa zuwa gare shi yake wannan rubutu
domin dalilan da suka haɗa da jin daɗi, da zaburarwa ga
mai hankali, wato don ya kasance darasi ko wa’azi.
Dangane da adabi Malam Yahya Nawawi a gefen waƙa ya fi ƙarfi.
Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya ambata cikin kundinsa na digiri
na uku, cewa mahaifinsa Waziri Junaidu wanda Baba ne ga Nawawi saboda ƙanen Waziri Abdulƙadir Macciɗo mahaifin Nawawi
ne, Nawawi ya yi wa wata waƙa
tashɗiri da Waziri Junaidu ya yi lokacin da suka biya ta wani
fili a gefen Sakkwato mai shuke-shuke da suka yi libliblib saboda ni’imar da ke
wurin. (Sambo W. Junaidu1985:140-141). Wannan bayani yana nuni da cewa ko a
cikin mawaƙa Nawawi ƙwararre ne, domin kuwa duk da yi wa waƙa tahmisi mawuyacin abu ne, balle tashɗiri. Manazarta waƙa sun san da abin da wannan iƙrari ke nufi. To sai dai Nawawi bai shagaltar da kansa da
rubuta waƙa ba, watakila
saboda tasirin fannonin ilmin da ya fi ƙarfi a kai da na ambata sama, wato Tauhidi da Fiƙihu da Alƙur’ani
da Tafsirinsa.
Akwai wani aiki da Nawawi ya rubuta wanda ya tara tarihi da
zube da waƙa. Wannan aiki shi
ne a kan ziyarar da Yahya Nawawi ya kai a birane masu tsarki, Makka da Madina da
kuma yake shauƙin ya sake
ziyarta. Ya kira littafin, ‘Tarwiihil Ƙalbil Haziini bi Zikri Akhbaari
Rihlatinaa ilaa Makkati wa Buldatil Amini’.
Bayan ya gabatar da sunan littafin da dalilin rubuta shi cikin layuka goma sha ɗaya gami da Basmala sai ya bi su da baitoci ishirin da
bakwai 27 sannan ya koma ga zube na kamar shafuka huɗu. Ta haka ya rubuta littafin mai shafuka talatin, 30, da waƙa ta fi tsawo ciki.
Manazarta
Abba, A.ds. (editoci) Sultans of
Sokoto. Kaduna: Arewa House.
Adamu, L.S. (2015) Hafsatu Ahmadu Bello: Jarumar Da Ba A Ruruta Ba (fassara: Dunfawa,
A.A.). Kaduna: Littattafan Adams.
Adamu, L.S. (2015) Hafsatu Ahmadu Bello: The Unsung Heroine. Kaduna: Adams Books.
Alƙali, H. (2002) The Chief Arbiter: Waziri Junaidu and HisIntellectual Contribution. Sokoto: Usmanu Danfodiyo
University.
Boyd, J. (1989). The Caliph’s Sister: Nana Asma’u 1793-1865. London: Newbury House,
900 Eastern Avenue.
Buhari, A. (2014), Intellectual Foundation of Sokoto Caliphate: Scholarship, Faith,
Revolusion and An Empire. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Gwandu, A.A. (1977). ‘Abdullahi b.
Fodio As A Muslim Jurist’ Ph.D. thesis, Durham.
Wasu ayyukan Malam Yahya Nawawi cikin
Larabci ko Ajamin Hausa da hannunsa ko aka juya, waɗanda mai muƙala
ta mallaka.
Hira da Farfesa Abdullahi Bayero Yahya
Nawawi a ɗaya daga cikin tattaunawarmu da shi kan Halaye da Rayuwar Alƙalin Lardi Yahya Nawawi’ a gidansa da ke Gwiwa Eka Sakkwato,
ranar 18 ga Yuni, 2023 da ƙarfe
5 yamma.
Hira da Ibrahim Yahya Nawawi ranar 28
ga watan Mayu, 2023.
Hira da Ibrahim Yalauɗo ranar 26 ga watan Maris, 2023.
Hira da Justice Shehu Yahya mai murabus
ranar 25 ga watan Maris, 2023.
Last, M. (2007) Daular Sakkwato (fassara: Bunza, A.M. da wasu). Sokoto: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Ref. No Sokoto I/23/169 Alƙalai a Sokoto, 1931-1961 History Bureau Achieves, Sokoto
Sashen Koyar da Harsunan Najeriya,
(2020), ZAUREN WAƘA. Sokoto:
Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Talata Mafara, M. I. (199), Daular Usmaniyya I-3. Kaduna: Nadabo
Print Production.
Waziri Junaidu History and Culture
Bureu Reference Files.
Yahaya, I. Y. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin
Hausa. Zariya: Northern Nigeria Publishing Company.
Rataye
Hoto na 2
Hoto na ɗaya da na biyu (1 da 14) shafukan farko da na ƙarshe ne na sakamakon binciken da Yahya Nawawi (lokacin yana Wali)
ya gabatar wa Majalisar Sarkin Musulmi Abubakar III a 1949.
Hoto na 4
Hoto na 5
Hotuna na 3,4,5 da na 6 nasiha ce da Yahya Nawawi ya ba Kwamitin
Yaƙi da Shashanci da Almubazzaranbci na Majalisar Sarkin Musulmi
Abubakar III a 1971 da ya.
Waɗannan kuma wasu shafuka ne na wani talifin Yahya Nawayi da ya yi
cikin waƙa da taƙaitattun bayanai cikin zube. Ya kira aikin da Kitab Tarwiihil Ƙalbil Haziini (Hutar Da Zuciya Mai Damuwa). A cikin waƙar akwai jigogi da dama. Ya yi wannan talifi ne domin ya taya ƙanin mahaifinsa, Waziri Junaidu, murnar dawowa daga Hajji. Yahya
Nawawi ya ce wannan dawowa da ƙanin mahaifinsa ya yi ta motsar da zuciyarsa da tsananin ƙaunar Allah ya nufe shi (shi Nawawi) da sake tafiya ƙasa mai tsarki.
[1] Mallam Yahya Nawawi
ya rubuta sunansa a msatsayin ‘Yahya Nawawi’ cikin littafin day a rubuta, kamar
cikin da dama daga ayyukansa, mai mai suna, Kitaabat- Tanbiih wal Irshaad.
[2] Duba jaridar JAGORAta
Disamba 7-13, 2001; ta Ingilishi kuwa, THE PATH December 5-11, 2001.
[3] Usman Giɗaɗo shi ne
miji ga Nana Asma’u ɗiyar Mujaddadi
Shehu Usman bn Fodiyo rahimahullahu bi Rahamatihi.
[4]AlKasum Abba, Ibrahimn
Jumare, Shu’aibu Aliyu, (2017) Sultans of
Sokoto, Shafi na 215-245 Arewa House Kaduna
[5]Damascas da Nawa duk suna a ƙasar Siriya ta yanzu
[6]Al-Nawawi
40 Hadith Arabic Text with English Translation and Commentry, by Basheer A.
Mohyidin
[7]Na samu
wannan bayani a wajen Justice Shehu Yahaya Nawawi a tattaunawarmu da shi a
gidanshi na Clapparton Road, kusa da Unguwar Gawon Nama, Sokoto, a ranar
Assabar 25 ga watan Maris, 2023.
[8]Akwai
bayanai kan Waziri Abdulƙadir Macciɗo a cikin
Littafin Tsarabar Buhari da Waziri
Junaidu (2007) wallafar Ibrahim Junaidu. A cikin Littafin an kawo sharhi
kan ‘ya’ya da jikokin Waziri Abdulƙadir Ɗan Waziri Buhari. Waziri Abdulƙadir kuma
shi ne mahaifin Alƙalin Lardi Yahya Nawawi.
[9]Tare da mijinta
sojojin da suka yi juyin mulki na 15/1/1966 aka kashe ta tana mai kariyar
mijinta. Duba Hafsatu Ahmadu Bello: Jarumar
Da Ba A Ruruta Ba (fassara: Atiku Ahmad Dunfawa), da Ladi S. Adamu (2015), Hafsatu Ahmadu Bello: The Unsung Heroine.
[10] Hirar da
aka ambata da Justice Shehu Yahya (mai murabus) da kuma littafin Ibrahim Gandi
Junaidu (Tsarabar Waziri Buhari da Waziri
Junaidu).
[11] Hira da
Malam Ibrahim Yoloɗo ranar
Lahadi 26 ga watan Maris, 2023.
[12] Malam
Ubandoma shi ne Kakan Sidi Attahiru Ibrahim Sannanen Malamin Addinin Musulunci
a garin Sakkwato.
[13]Malam
Abdulƙadir Macciɗo shi ne
Limamin Masallacin Sarkin Musulm Muhammadu Bello na wanan lokaci.
[14] Tattaunwa
da Malam Ibrahim Yahya Nawawi a Giɗaɗawa, gidan Malam Yahya
Nawawi Alƙalin Lardi a ranakun 27 da 28 ga
watan Mayu, 2023.
[15]Ɗansa, Abdullahi Bayero ya taɓa shaida wa mai wannan muƙala cewa a farkon kama
aikinsa sai da mahaifinsa ya ja kunnensa da kada ya ci abinci mai man gyaɗa ko twanka, amma sai
shi Bayero ya ɗauka cewa wannan
takurawa ce tsohonsa ke yi masa, saboda haka bai kula ba. Watan farko na ƙarewa sai ya zo gida ya
faɗa wa mahaifiyarsa cewa
wani ciyo yake ji a maƙoshi da kuma ɗankanoma, sai ta ce masa
halan yakan yi amfani da twanka da kuma man gyaɗa. Da ya ce lalle duk yana amfani da su sai ta ce
masa ya faɗa wa mahaifinsa zai ba shi
magani. Sai ya ce Baba fa ya hore shi da kada ya haye ma waɗannan, amma sai ta ce
masa kada ya ji tsoro ya dai tafi ya faɗa masa. Ai kuwa da Bayero ya je ya yi yadda
mahaifiyar ta umurce shi, sam Yahya Nawawi bai yi wata-wata ba sai ya tura shi
inda wani malami mai haɗa maganin irin wannan
matsala. Ai da shan maganin kamin Bayero ya koma garin da yake karantarwa ya
warke. Sai ya tafi kasuwa inda ya ajiye kuɗi ga mai man gyaɗa ya ce duk kuɗin man gyaɗa ya mayar ga man ja!!!
[16] Wannan bayani na
hikima na same shi ne a wajen Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi a ɗaya daga cikin
tattaunawarmu da shi kan Halaye da
Rayuwar Alƙalin Lardi Yahya Nawawi’. An yi wannan tattaunawa a gidansa
da ke Guiwa Eka Sakkwato, ranar 18 ga Yuni, 2023 da ƙarfe 5 yamma.
[17] Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, ZAUREN WAƘA. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, sh.
180-181.
[18] Akwai bayani a kan haka cikin littafin Hamidu Alƙali, Waziri Junaidu: The
Chief Arbiter (2004:sh. 50 -56) a babi na Huɗu, da shafi na 74 na
Babi na Shidda.
[19] A dubi Hamidu Alƙali, Waziri Junaidu: The
Chief Arbiter (2004:) da Abdullahi Buhari, Intellectual Foundation of Sokoto Caliphate (2014:689-690)
[20] Hira daga cikin
hirarrakin da marubuciya ta sha yi da Abdullahi Bayero Yahya a ofishinsa da ke
Jami’ar Jihar Sakkwato ko a gidansa da ke Sakkwato a shiyyar Gwiwa Eka.
[21] A bubi
Abdullahi Buhari (2014:690).
[22] Wani abin ban takaici
da mai wannan muƙala, watakila har da ga Abdullahi Buhari mai Intellectual Foundation.., ta ci karo da
shi shi ne, rashin samun kai hannunta ga ko da aƙalla shari’a guda da
Malam Yahya Nawawi ya yanke a zamanin da yake Alƙali. Lokacin da ta
shiga Cibiyar Adana Kayan Tarihi Da Al’adu Ta Waziri Junaidu (Waziri Junaidu
History and Culture Bureau) ta samu ganin akwatunan da ake saka shari’o’in
kotuna daban daban, har kuwa na kotunan da Malam Yahya Nawawi ya yi alƙalanci ta samu gani.
Amma kash! Kome babu cikin akwatin!! Ko dai an sauya musu mazauni ko kuwa an
sace. Abu mai ƙarin ban mamaki da takaici shi ne, akwai shari’o’in wanda
Nawawi ya gada a 1954 a matsayin Babban Alƙali cikin
akwatunan!!!. Sai dai ayyukansa waƙanda ba shari’a ba, su
kam an same su a ɓangaren
da ba na shari’o’i ba. Kai hatta da ɓangaren da ake liƙa hotunan manyan
malamai wannan marubuciyar ta zagaya amma ta tarar da babu hoton Yahya Nawawi,
alhali kuwa ta sha kai ziyara a wannan wuri a baya kuma hotonsa yana nan liƙe. To amma har yanzu
da ake rubuta wannan muƙala marubuciyar tana kan nema a wasu garuruwan Lardin
Sakkwato inda Nawawi ya kai ziyarar aiki.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.