𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Ina da tsohon ciki, idan ina
Sallah sunkuyo da tashi yana bani wahala, zan iya yi a zaune?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum as salam. Za ki iya yi a zaune, in har
ba za ki iya yi a tsaye ba, saboda Hadisin Imran ɗan Hussain lokacin da ya faɗawa Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) Basir ɗin da yake damunsa, sai yace masa: "Kayi Sallah a
tsaye, in ka kasa kayi a zaune, in ka kasa yi a zaune kayi da gefenka",
kamar yadda Bukhari ya rawaito a Hadisi na (1066).
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: wanda yake da
lalurar da zata hana shi yin Sallah a tsaye, zai iya yi a zaune, saboda addinin
Musulunci mai sauƙi ne, ba ya ɗorawa rai abin
da ba zai iya ba.
Allah ne mafi sani.
𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.