Tambihi da Tunasarwa Dangane da HaDuwar Zumunci ta kungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano

    Citation: Gusau, S.M. (2024). Tambihi da Tunasarwa Dangane da Haɗuwar Zumunci ta Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 67-70. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.008.

    Tambihi da Tunasarwa Dangane da Haɗuwar Zumunci ta Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano

    Sa’idu Muhammad Gusau
    Jami’ar Bayero, Kano

    Tsakure: Zamfarawa wani sashe ne a cikin al’ummar Hausawa waɗanda suka kasance da hasaloli kyawawa cike da halayen kirki tare da aiwatar gaskiya da son ‘yan’uwa da kuma abokai. Mutane ne masu kunya, masu kawar da kai, sannan kuma masu neman shawarwari a tsarin hasalolin rayuwa. Zamfarawa mutane ne, masu kulawa, waɗanda suke iya zama da kowaɗanne nau’o’in mutane da suka sami kansu a cikinsu ne. Suna tafiyar da kyawawan mu’amaloli ne da mutane daban-daban, musamman idan aka yi la’akari da yanayin harkokinsu da mutanen Legas da na Ibadan da na Ogbomosho da na Ghana da na Paris da na Ingila da na Amurka da na Libya da na Agadaz da na Anambara da na Adamawa da na Zuru da na Yawuri da na Argungu da na Kano da na Katsina da na Zariya da dai sauransu. An ayyana, ayyuka ne da hidimomin rayuwa suka kawo Zamfarawa jihar Kano. An fahimci Zamfarawa mazauna Kano sun haɗu ne a sigar mutuntawa tare da girmama duk wani jinsi na ɗan’adam da suke zaune da shi. Hakan ne kuma ya haddasa musu aiwatar da wani yunƙuri tare da azama na kafawa da samar da Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano kwata. Daga cikin manufofin da suka haddasa kafa wannan ƙungiya bai wuce a ƙara samar da danƙon zumunci ba, tare da lura da ɗorewar kulawa da juna. Haka kuma yana daga cikin manufofinta, a ƙara saka ƙaimi wajen taimakawa da ƙarfafawa juna da kuma abokan hulɗa, tare da lazimtar aikata halaye na gari da ƙarfafa ayyukan addinin Musulunci da bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa dukkan nauoi da rassa na ilimi da kuma kulawa da sa-hannun ƙungiya wajen samar da ayyukan-yi ga matasa. Ta haka ake ba da shawara da a bunƙasa wasu muhimman gurabu domin a aiwatar da hidimomin ƙungiyar. Sannan, gurabun kar su yawaita; a zaɓi mutanen da suka dace a ɗora su a matsayin Shugaban Ƙungiya da  Sakataren Dauwana Ayyukan Ƙungiya da Sakataren Tantance Shiga-da-Ficen Kuɗin Ƙungiya da Maaji da Sakataren Sadar da Ayyukan Ƙungiya. Sannan a samar da Kundin Tsarin Mulki (Constitution) da Kwamitin Amintattun Wakilai na Ƙungiya da Kwamitin Iyayen Ƙungiya da kuma Kwamitin Lauyoyin Ƙungiya.

    Fitilun Kalmomi: tambihi, tunasarwa, zumunci, zamfarawa, mazauna jihar kano

    Gabatarwa

    Tun da jimawa a zangon farko na haɗuwar Hausawa suke nuna ƙauna da haɗin kai a tsakanin junansu a kowace dangantaka ta jini ko ta wasu hulɗoɗi na yau da kullum, kai hatta ma ta musayar sadarwa ta wasiɗar tsarin harshen Hausa.

    Hausawa sun amince su ‘yan’uwan juna ne, a matsayinsu na dangin goro, suna tafiyar da harkokin rayuwarsu domin su taimaki kansu da kansu. Alalmisali, abin ci da abin sha da sutura ta suturce jiki har kuwa da yin ƙawa, da muhalli na zama da hutu da bacci da suturta kai, aƙalla ba za a iya samun su ba sai mafarauta ko maharba ko manoma ko masunta ko maƙera ko masaƙa ko maɗinka ko majema ta fuskar misalai sun taimaka, sun aiwatar da ayyukansu.

    Ta haka ne, Hausawa suka tsiri al’adu iri biyu gwargwadon tarbiyya da koyo ko ɗalibta da kwaikwayo ko halitacciyar ɗabi’a ko ma hali, har guda biyu.

    Akwai al’adu masu kyawo da kuma al’adu munana, marasa nagarta, wato ɓata-ingila kuma ɓata-gari.

    A dunƙule, jumlatin Hausawa, suna yin riƙo da kyawawan al’adu ne, musamman ma bayan sun karɓi addinin Musulunci. Su kuwa ɓata-garin al’adu sukan wanzu ne da ƙarfi irin na Shaiɗanu, wannan ne ya kawo suke bauɗe wa kyawawan shika-shikan zama na al’ummar Hausawa.

    Zamfarawa wani sashe ne a cikin al’ummar Hausawa[1], waɗanda suka kasance da hasaloli kyawawa irin na Hausawa. Za a daɗa kawo bayanansa a nan gaba kaɗan cikin yardar Allahu.

    Kanawa su ma masu tushe da asali na Hausawa ne waɗanda yawanci suke a zaune a farfajiya ta Kano. Mutane ne masu zumunci waɗanda za a iya zaunawa a cikinsu cikin lumana, a ƙaru da arzukansu, har kuma su dinga lulluɓe ‘yan’uwasu, Zamfarawa da kunya da hidimomi na zumunci. Haƙiƙa, a ko da yaushe, za a so a raɓu da Kanawa, a ribatu da zama da su.

    A wannan takarda za a yi tambihi da tunasarwa ne a duddunƙule ga ‘yan’uwan Kanawa, Zamfarawa da masu dangantaka ta ƙut-da-ƙut da su. Da farko dai ayyuka ne da hidimomi suka kakkawo Zamfarawa Kano, suka zo, suka zazzauna, wasu ma har suka yi kaka-gida ko zaman a dishan, ko na mutu-ka-raba[2].

    Har wa yau, takardar za ta yi magana ne kan Ƙungiya ta Zamfarawa Mazauna Jihar Kano.

    Tarayyar Zamfarawa

    Dukkan Zamfarawa abokan zaman juna ne, masu lura ne, kuma masu rarrabewa da tantancewa da daidaitawa da tsinkaya. Zamfarawa sun sa kai da bazama da himmatuwa a neman ilimin Musulunci da na rayuwar Zamantakewa da na sauran sassan fannoni da suka danganci rayuwar duniya har zuwa rayuwa ta lahira.

    A wata fahimta ta ƙanƙame zumunci a wajen Zamfarawa, haƙiƙa, suna yin lura tare da rarrabewa a tafiyar da mu’amaloli na yau da kullum. Ta haka ne suke kallon mutane a cikin gidaje uku:

    a.Gida na Farko: Ya ƙunshi mutane masu ƙima, magabata, dattawa ainun, masu mutunci, masu nagarta, masu muhibba, masu muƙami na tantancewa, masu zaɓar harshe na zance ko na wata sadarwa.

    A wannan kaso; Zamfarawa suna ƙarfafa mutanen nan su ne: mahaifa ko iyaye da sa’o’insu a mabambantan gidaje da Malamai da Shugabanni.

    b.                 Gida na Biyu: Ya tattara mutane masu darajoji irin nasu, masu tasiri na zama, masu mutunta juna, masu ƙara wa juna auki da dukkan madangantan abubuwan nan.

    Rukunin nan kuwa ya shafi ‘yan’uwan haihuwa, maza da mata, da abokan hulɗoɗi ko na zama a Unguwa ko a gari da ire-irensu, maza da mata.

    c. Gida na Uku: ya haɗa mutane masu biyowa baya a ilimi ko a wani matsayi ko a shekaru[3].

    Ire-iren mutane na wannan kaso sun ƙunshi ɗalibai na mutum da mataimaka na al’umma tun ma ba direbobi da ma’aikata masu yin hidimomin gida da sauran ƙananan ma’aikata masu tafiyar harkokin jama’a na mabambantan jinsunan mutane.

    Su mutanen Zamfara, mutane ne masu halayen kirki masu gaskiya ɓaro-ɓaro, masu son ‘yan’uwa, masu son abokai, masu kunya, masu kawar da kai, marasa hushi da sauri-sauri ko hanzari-hanzari, masu neman shawarwari, masu ɓoye asiri, sannan kuma marasa girman kai.

    Haka kuma Zamfarawa masu kulawa ne, masu iya zama da kowaɗanne nau’o’in mutane da suka sami kansu a cikinsu ne.

    Hakazalika, Zamfarawa masu tafiyar da kyawawan mu’amaloli ne da mutane, musamman idan ba a mayar da su wawaye ko sarakataha ba. Dubi yanayin harkokinsu da mutanen Legas da na Ibadan da na Ogbomosho da na Ghana da Paris da Ingila da Anambara da Adamawa da Zuru da Yawuri da Argungu da Kano[4] da Katsina da Zariya[5] da Sakkwato da Libya da Agadaz da sauransu da yawa[6].

    Gabatar da Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano

    A wannan haɗuwa ta zumunci mun tattaru ne domin mu gabatar da ƙungiya ta Zamfarawa Mazauna Jihar Kano. Ashe ke nan abu ne mai matuƙar alfanu a yi wa jagororin da za a zaɓa, su tafiyar da ƙungiyar nan wata tunasarwa.

    Ta haka ne muke ƙarfafa musu su zamanto masu riƙo da halaye nagartattu na Zamfarawa da aka bayyana wasu a wannan takarda. Ya yi kyau su zama masu kafa kyakkyawan misalai na Shugabanci, ta nuna adalci da riƙon amana da tsare yin gaskiya a ko da yaushe. Su kuma zama marasa karkata a wani gefe a tafiyar da mulki. Su kasance masu warware matsalolin al’umma ta sauraron kowane gefe cikin nutsuwa, da kalamai bisa hujjoji tare da yin nasiha da tsawatarwa da gargaɗi.

    Har wa yau, ya dace dukkan abubuwan da za su aiwatar su kasance masu haɗa kan mutane ne kuma waɗanda jama’a za su jimre ko daure yin su cikin daɗin rai.

    Shugabannin kuma su dinga yin taka-tsantsan a gudanar da kowace irin hidima ta jama’a, su zama masu ƙara wa ƙungiya arzuka ba masu ɗebewa ba.

    Manufofin Wannan Ƙungiya

    i.        Ƙara danƙon zumunci da ɗorewar kulawa da juna;

    ii.      Daɗa son ‘yan’uwanmu a ko’ina muka sami kanmu;

    iii.   Taimakawa da ƙarfafawa da raya junanmu da kuma abokan hulɗoɗinmu;

    iv.   Nisantar munanan halaye;

    v.      Lazimtar aikata halaye na gari tare da ƙarfafawa da raya addinin Musulunci;

    vi.   Bunƙasa Tattalin Arziki da ƙarfafa dukkan nau’o’i da rassa na ilimi;

    vii. Kulawa da sa-Hannun Ƙungiya a samar da Ayyukan yi ga masu Tasowa.

    Muhimman Gurabu na Tafiyar da Ƙungiya

    Wasu matsayai da za a bi ta kansu a aiwatar da hidimomi na ƙungiya, kuma ya cancanci a zaɓi mutanen da suka dace a ɗoɗɗora su a kansu, sun ƙunshi:

    1.   Shugaban Ƙungiya[7]

    2.   Sakataren Dauwana Ayyukan Ƙungiya[8]

    3.   Sakataren Tantance Shiga-da-Ficen Kuɗin Ƙungiya[9]

    4.   Ma’aji[10]

    5.   Sakataren Sadar da Ayyukan Ƙungiya[11]

    Amintattun Wakilai na Ƙungiya[12]

    Kimanin Mutane Shida (6)

    Iyayen Ƙungiya[13]

    Za a kalato dattawa na Ƙungiya daga Gida Zamfara da waɗanda suke zaune a Jihar Kano, aƙalla 2+3=5.

    Tsarin Mulki na Ƙungiya[14]

    Ya dace kafin a yi zaɓe sai masu riƙon ƙwarya na wannan Ƙungiya sun samar da Kundin Tsarin Mulki da zai yi jagoranci na haliyyar tafiyar da Ƙungiya.

    Akwai bukatar a kafa kwamiti da zai tsayu haiƙan a wannan aiki cikin himma da za a iya zazzaɓowa daga kowane ɓangare na farfajiyar ƙungiya.

    Lauyoyin Ƙungiya[15]

    Tsofaffin Shugabannin Ƙungiya[16]

    Kammalawa

    A wannan takarda an yi magana ne tare da yin tambihi da tunasar da wasu nauye-nauye da suka ɗoru a kan ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano. A bayanin an nuna Zamfarawa al’umma ce wadda take kiyaye darajar mutanenta da dukkan mutane, mabambanta, waɗanda take hulɗoɗi na zamantakewa a tare da su. Haka kuma an kawo bayani a taƙaice dangane da wasu halaye na mutanen Zamfara da yanayi da matakai na tattakinsu da jama’a. Daga nan ne kuma aka zo da wasu manufofi na kafa Ƙungiyar Zamfarawa a Kano da kuma wasu manyan gurabu da za a nannaɗa mutanen da suka dace, masu haƙuri domin su tafiyar da kyakkyawan jagoranci na wannan mashahuriyar Ƙungiya ta Zamfarawa.

    A wannan takarda kuma, an fahimci Zamfarawa mazauna Kano sun haɗu ne a mutuntawa tare da girmama duk wani jinsi na ɗan’adam da suke zaune da shi, ko ya shige su. Hakan ne kuma ya janyo ko ya haddasa yunƙuri da azama na kafawa da samar da Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano kwata.

    Sannan kuma an lura a ɗabi’u na Zamfarawa, mutanen Zamfara suna da lafiyayyar zuciya, mai nagarta da sukan iya raba gidaje ko dukiyoyinsu su ba na gida ba ko baƙi ko waɗanda suka shaƙu da su.

    Takardar nan ta kuma hango tare da tsinkayo Ƙungiya da ake ƙoƙarin gabatarwa ta mazauna Kano, tabbas, za ta bi turba ta Zamfarawa, musamman ta himmatuwa da ƙauna ta dangin goro da tabbatar musu da kariya bisa gwadabe na sunna da kiyaye dokoki na ƙasa da na zamantakewa.

    Manazarta

    Abubakar, Sarkin Musulmi Sir (1966) Hali Zanen Dutsi. Zaria: NNPC

    Gusau, B. M. & Gusau, S. M. (2012) Gusau ta Malam Sambo. Kano: Benchmark Publishers Limited & Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (1994) Ƙasar Zamfara: Tsokaci a kan Neman Jihar Zamfara. Gusau: Makarantar Sambo Sakandare Tudun Wada.

    Gusau, S. M. (1999) Muhimman Garuruwan Ƙasar Hausa; Waiwaye kan Tarihin Kafuwarsu a Taƙaice. Mujallar WAJLLC, Vol. 2 Kano: Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2015) Fulanin Zamfara Katsinar Laka a Daular Sakkwato. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2021) Tarihin Wanzuwa da Asalin Hausawa. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing.

    Gusau, S. M. (2023) Dauloli a Ƙasar Hausa da Jihadin Usmaniyya da Mulkin Turawan Ingila da Mulkin Jamhuriyoyin Demokuraɗiyya da na Sojoji. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing.

    Gusau, S. M. (2023) Matsayi da Darajar Ubangida a Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2023) Nazarin Al’adu da Adabi a Al’ummar Hausawa. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing.

    Kirk-Greene, A. H. M. (1966) Hausa ba Dabo ba ne. London: Oxford University Press.

    Nadama, G. (1977) The Rise and Collapse of Hausa State: A Social and Political History of Zamfara. Zaria: Ahmadu Bello University.



    [1] Duk da yake ingantaccen tarihi na Qasar Hausa ya tabbatar Zamfarawa rukuni ne daga cikin rukunin Hausawa na asali, amma za a iya dawo da tunani a kan wata ruwaya ta siyasar baka wadda take zayyana Zamfarawa suna cikin Banza Bakwai (Barth, H (1957), Palmer, H. R. (1928) & Dokaji, W. K. A. (1988 & 1978) sh: 10-11).

    [2] Wani abin lura ko la’akari a nan shi ne, Zamfarawan nan, zukatansu suna nan a xamfare da Zamfara a gidajensu na gado, ba tare da wata tantama ko xar-xar ba.

    [3] Wata rana wani Jagoran Gudanar da wata Asibiti yake gaya mana, yau da Direban wannan Asibiti mai ilimi ne da shi ma ya zama C. M. D. Domin haka, ya zama wajibi a zauna da shi yadda yake bisa irin nasa sabgogi a rayuwa. Hali nasa ko xabi’a tasa sun yi daidai ne da nauyi na fahimta da ganowarsa.

    [4] Yau, cikin amincin Allah, muna gabatar da Qungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano.

    [5] A wasu lokuta a baya, an sami wata zuriyya sukutum wadda ta tashi daga Gusau, Jihar Zamfara a yau, ta koma Birnin Zariya da zama. Wannan zuriyya ta xaukaka sosai, ta burunqasa ainun, daga cikinta, a Zariya, an sami manyan Malamai da Jami’ai da sauran ma’aikata da Hakimai a Zazzau, uwa-uba ma da Minista. Waxannan dukkansu daga cikin arbarkatu da ALlahu ya yi wa Zamfarawa. A yau jumlataninsu suna tunqaho da su Zamfarawa ne.

    [6] A wannan jere ba a bi fasalin qwarta ta bi qwarya ba, an yi la’akari da nauyi na dangantakokin Zamfarawa ne da su.

    [7] President.

    [8] Administrative Secretary.

    [9] Financial Secretary.

    [10] Treasurer.

    [11] Information Secretary.

    [12] Six Regional Reps or Association Trustees from Middle Elders.

    [13] Association Elders of High Cadre.

    [14] Association Constitution.

    [15] Association Legal Team.

    [16] Ex-Officio (Past-Presidents).

    Download the article:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.