Matsalar Girki A Gidan Aure

    TAMBAYA (152)

    Assalamualaikum malam Dan Allah ya halatta a hada mata biyu a gida daya kuma a hadamasu girki kuma auri ta uku  Bata gida daban bama unguwa daya ba lta tana zaune cikin konciyar hankali mukuma kullum cikin tashi hankali sabida nace a raba mana girki yace bazai raba ba nikuma nace bazan kara girki da wataba lnada laifi a shari a nagode

    AMSA

    Waalaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh

    Ya halatta miji ya hada Mata 2, 3 ko 4 a gida daya domin kuwa duk suna karkashin ikon sa ne saidai Kuma ya zama dole yayi adalci a tsakanin su don kada ya fada cikin sahun mazajen nan da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace zasu tashi da shanyayyen jiki a ranar lahira silar rashin adalci ga matayensu kamar yanda hadisin ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari

    Ibn Abi Shaiba Rahimahullah yace

    Tabi'i - Muhammad Ibn   Rahimahullah) yace: Idan Sahabi yana da mata 2, yakan Yi alwala a gidan daya sannan idan wata alwalar ta kama yakan Yi ta a gidan daya matar tashi duk dai don yayi adalci a tsakanin su

    Jabir ibn Zayd yace: Ina yin adalci a tsakanin Mata na 2, idan na sumbaci (kissing😘) din ta farko to itama ta biyun sai na sumbace ta don yin adalci a tsakanin su

    Mujahid yace: Sahabbai suna adalci ga matayensu ko a bangaren shafa turare, ta Yanda ba sa banbanta shafa turare ga matansu idan ya shafa turare kala kaza to irinsa zai shafa idan ya shiga wajen daya matar tashi duk dai don yin adalci ga matayensu

    [A duba: Musannaf na Ibn Abi Shayba, Durr al Munthur - karkashin 4: 128]

    Qalubale ga mazaje masu aure wadanda basa sumbatar matayensu Wai don kada su raina su. Rashin koyi da Sunnar Manzon Rahama yasa yawancin mazaje sukai watsi da hadisin da Nana Aisha (Radiyallahu anha) tace Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya kasance Yana sumbatar matansa. Ga samun lada ga Kuma samun shaquwar so da qauna

    Dangane da batun da kikai na umarnin da ya baki, Indai shine yace kiyi girkin Kuma ki ka nuna bazakiyi ba to anan kina da laifi saboda kin sabawa umarnin Mijin ki ne. Amman indai itace to anan yakamata ki zauna da ita kuyi sulhu domin kuwa babu komai a cikin sulhu sai alkhairi kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya fada a cikin Sahihul Bukhari

    Tunda shi yace bazai raba girkin ba to kamata yayi ku hade kanku ku zauna dashi cikin girmamawa ku ce kuna buqatar kowaccen ku ta dinga yin girkin ta. Idan ya qi yarda to menene a ciki don kunyi girki tare. Ba wata matsala bace babba saidai idan ke kika dauki lamarin da girma

    Kada fa ki manta wallahi da akwai daruruwan Matan da a yanzu Haka suke son su samu dama irin wadda kika samu amman Allah bai kawo Mijin auren ba. Kai akwai wadda ma da zata samu damar zama da kishiyar su dinga girkin tare Haka take so. Don Haka Ni a shawarata kamata yayi ku daidaita tsakanin ku ta hanyar zama ku fitarda maslaha a junanku ko don yayanku su taso da jin qan ku domin kuwa idan yayanki suka taso suka ga bakwa jituwa akan girki to tabbas bazaa samu hadin Kai tsakaninsu ba har su girma, kinga Kuma ai anan Shaidan yayi Nasara. Ina roqon Allah ya hade kawunanku baki daya ta Yanda zaku ci jarabawar rayuwar zamantakewar auratayya

    Wallahu taala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...


    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.