Hukuncin Hada Sauraren Kida Da Karatun Qur'ani

    TAMBAYA (158)

    Don Allah addu'a nake so a bani ta budin qwaqwala gameda karatun da nake yi

    AMSA

    Babu wata addua ta musamman da na sani dangane da budun qwaqwala saidai Zan Dora ka akan wata turba wadda idan ka bi zaka samu budi a qwaqwalar ka in Sha Allaah

    Kwanakin baya akwai wasu dalibai na da suke min tambayoyi Ina basu amsa, sai suka ce "Gaskiya Malam kana da tarin ilimi..." (Ko wani abu makamancin Haka), sai naji gaba na ya fadi Nan danan nace musu: bana da abinda zan faɗa muku face abinda Mala'iku suka faɗa a lokacin da Allaah Azzawajallah ya tambayesu sunayen abubuwa Wanda Annabi Adam Alaihimus Salam ne kadai ya iya bada amsarsu gaba daya. Ayar tana cikin Suratul Baqara inda Mala'iku suka ce:

    ( قَالُوا سُبْحَانَكَ لَا عِلْمَ لَنَا إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَا ۖ إِنَّكَ أَنتَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ )

    البقرة (32) Al-Baqara

    Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."

    Da ace na sake na yarda da maganar su cewar Ni din masani ne to da na cuci kaina Kuma da Shaidan ya sa nayi girman Kai a wannan lokacin harma naji Ni Wani ne, to amman da ya zama na namaida sanin ga "al-Alimu" Kuma "Alimul Ghaibu" to sai naji na samu sa'ida a raina😌

    Don Haka, ya dan uwa mai albarka, kaima Ina baka shawara da ka dinga yawaita maimaita wannan ayar

    Bayan kayi ta sai ka qara da "Rabbi Zidni ilman" ma'ana: Ya Allaah ka qaramin ilimi

    Sharadi na biyu Kuma shine ka nace akan karatun ka yawaita bibiyar abinda aka koya maka sannan Kuma uwa uba ka nesanta kanka daga sauraren kade kade da Waqe Waqe da sauran Zunubbai sannan ka yawaita sauraren da Kuma karatun Qur'ani domin kuwa sauraren kida da Qur'ani basa zama a zuciyar muminai kamar yanda Ibn al-Qayyim al-Jawziyya ya faɗa a cikin littafin sa: "Sharrin sauraren kida da waqa: Sautin Shaidan da Kayan aikinsa" da Kuma Ibnul Jauzy a cikin littafin sa mai suna "Talbis iblis" ma'ana: Yaudarar da iblis yakewa Yan Adam

    Yanzu masifar da muka tsinci kanmu itace kusan ko'ina kida ke tashi, a Adaidaita Sahu Kida, Mota kida, Wajen sana'a kida, matar aure a kitchen kida, dalibai a aji, Malami na lecture daliba ta saka hijabi Wanda ya kare earpiece dinta tana sauraren kida, biki zaayi amman cigiyar Dj ake azo asa kida, kai nasha amsa gayyatar makarantun Islamiyah na saukar Qur'ani amman a qarshe sai an saka waqar makarantar mai dauke da kida. To ta yaya Zamu ga daidai ballantana mu samu nutsuwar zuciya

    Da ambaton Allaah Subhanahu wata'ala ne kadai zuciya take samun nutsuwa bawai da sauraren kide kide da waqe waqe ba kamar yanda wani shahararren mawaqin hausa ya rubuta a cikin studio dinsa: "Da sauraren kida da waqa zuciya take samun nutsuwa". Musamman naje har studio din domin yi musu Da'awah, nace su gaggauta cire wannan lafazin sannan su tuba ga Allaah "al-Jabbaru" domin kuwa wannan maganar ta ci karo da fadin Allaah:

    ( الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ )

    الرعد (28) Ar-Ra'd

    Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa.

    Sannan Kuma an karbo hadisi daga Abdurrahman bin Ganm wanda yace: Abu Amir ko Kuma Abu Malik al-Ash'ari cewar ya ji Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Za'a samu wasu mutane daga cikin al'ummata wadanda zasu dinga halasta Zina, saka tufafin alhariri, Shan giya da kuma Kayan kide kide"

    Sahihul Bukhari 5590

    A wani hadisin Kuma yace: "Allaah zai umarci kasa ta hadiye su sannan kuma zai maidasu birrai da aladu"

    Karin bayani sai a duba: Sunan Ibn Majah 4020. Ibn Abi Shaybah Vol. 5 page na 68. Imam Ahmad Vol. 5 page 342. At-Tarikh al-Kabir Vol. 1 page 305 da Vol. 7 page 222. Abu Dawud 3690. At-Tabarni a ciki al-Kabir Vol. 3 page 283. Al-Bayhaqi a cikin al-Kubrah Vol. 8 page 295 da Kuma Vol. 10 page 221. Ibn Hibban 6759. Ibn Taimiyya a cikin Fatawa al-Kubrah Vol. 6 page 37. Ibn al-Qattan a cikin Bayan al-Wahm Wal Iham Vol. 3 page 245 Haka kuma al-Albany ya inganta shi a cikin Silsilatu Ahadis as-Sahiha Vol. 1 page 138

    Haka Kuma da akwai hadisai da suke da alaqa da wannan daga Ubadah bin as-Samit, Abu Umamah, Ibn Abbas, Kaysan ko Kuma Nafi' Ibn Kaysan da Kuma Nana Aisha da wasunsu

    To amman wai duk da wadannan hujjojin Haka zakaji Mawaqi ba tsoron Allaah yazo Yana cewa ai sana'a muka dauki kida da waqa Kuma ai mu ba sata muke ba. Ko da basu San wannan hadisin ba suke ci gaba da wannan harkar sun siffanta da dabi'ar Nasara kenan ta Jahilci ko Kuma sun Sani suka take sanin kamar yanda Yahudawa suke take gaskiya

    Na qara tsorata da Sharrin sauraren kide kide bayan na saurari Tafsirin Aya ta 6 dake cikin Suratu Luqman. Sannan Kuma illar ta qara bayyana a gareni a lokacin da na karanta littafin: "Music Made Me Do It" ma'ana: "Sauraren kade kade yasa nayi hakan" wallafar Dr. Gohar Mushtaq

    Ya Allaah ka yafe mana su Kuma masu saka kida a waqoqi ka ganar dasu

    Wallahu taala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.