Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Haihuwa

TAMBAYA (141)

Aslm antashi lfy ya kokari nikam faa saede ayita hakuri dani ( ina yawan mafarkin inada ciki ko kuma wai na haihu harma nata6a mafarkin nahaifi yan biyu twins kuma banida ciki haryanxu tukunna Allah bae baniba shine nakeson a fassaramin mafarkin nagode) Allah ya kara daukaka

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

Mafarkin mace ta haifi namiji alhalin ba ta da ciki a zahiri na nufin arziqi. Idan mace mai ciki tayi mafarkin ta haifi namiji hakan na nufin mace za ta haifa idan kuma ta haifi mace a mafarki hakan na nufin za ta haifi namiji. Haihuwar mace na nufin samun saukin rayuwa haihuwar namiji kuma na nufin damuwa da baqin ciki

Idan namiji talaka yayi mafarkin an haifa masa da hakan na nufin daukaka. Idan mai kudi ne kuma hakan na nufin qunci. Idan gwauro ne hakan na nufin zubewar cikin matarsa

A taqaice, idan namiji yayi mafarkin ya haihu hakan na nufin mutuwarsa ko kuma mutuwar wani a cikin danginsa ko kuma mafarkin zai iya zama silar talaucinsa

SHARHI

Ki yawaita tsayuwar dare kina kai kukan ki ga Allah akan ya baki haihuwa indai za ta zame miki alkhairi

Domin kuwa wata haihuwar ba alkhairi bace ba

Kuma Allah mai iko ne akan komai ko da kin kai shekaru irin na matar Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) sai ki ga ya azurta ki da samun juna biyu kamar yanda ya ba su haihuwar Isma'il da Ishaq (Alaihimus Salam)

Kuma yan biyun da kika gani a mafarki, abu mai sauqi ne a wajen Allah ya azurtaki da samun su a zahiri

Kamardai yanda ya azurta wata yar kasar Mali, Halima Cissé da haihuwar yaya har guda 9 a jere a haihuwa guda daya, a shekarar 2021

Ki ci gaba da addu'a Allah ya baki yaya nagari wadanda zasu zamo abin alfahari ga al'ummar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)

Wallahu ta'ala a'alam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments