TAMBAYA (39)❓
Dan Allah inaso a taimaka a yi write up mai dumi a kan mata masu neman yan uwasu mata wllh kazantar ta yi yawa takai har basajin kunyar bayyana kansu a cikin jamaa. MENE NE hukuncinsu (Daga: Abu Said BUK)
AMSA
❗
Innalillahi
wainna ilaihirrajiun
Na
dade da fitar da amsar tambayar nan. Sai naga dacewar bari na sake dawo da
rubutun laakari da mummunan halin da GWAMNATIN kasarmu ta Nigeria take ƘOƘARIN
jefa mu ciki na karban YARJEJENIYAR SAMOA da take da alaƘa da kungiyar LGBTQ
wato auren JINSI. Wal iyazubuillah. Muna cikin MUSIBA sai Kuma ga wata MUSIBAR
da ta zarce wadda muke a baya. Wannan alamu ne na tashin ALƘIYAMA suke ta sake
bayyana akan idanunmu da kunnuwanmu
Rashin
kunyar bayyana kansu a cikin jama'a yanada nasaba da raguwar imaninsu, kuma
daman ya tabbata a hadisin Abu Hurairah RA yace ma'aiki SAW yace mutumin da
yake aikata zina ana a cire masa imaninsa ne, imanin zai dinga yawo a saman
kansa kamar hadari, bayan ya gama zinar sai imaninnasa ya dawo jikinsa (Abu
Dawud da al-Hakim suka rawaitoshi, Shaikh Albani ya ingantashi a cikin Silsila
Ahadis-Assahiha mai lambata 509)
Lesbianism
ga mata wadda ake kira da madigo da hausa basada banbanci da Homosexuality ga
maza wato Luwadi halayyar wasu daga cikin mutanen Annabi Lud AS, jinsi ne kawai
ya banbantasu amman sun kasance daga cikin manyan alkaba'ir wadanda kan iya
zama silar salwantar imanin mai aikatawa idan bai tuba ba, a karshe a tashi
mutum cikin al'ummar Annabi Lud AS wadanda Allah ya hallakar
A
binciken da nayi kwanannan naga wasu Archeologist (masana tarihin ragowar kasa
da abinda ta kunsa tun zamanin da) sun gano wani gunki mai suffar mace a garin
da aka halakar da mutanen Annabi Lud AS (Ana kiran wajen da "Dead
Sea" wanda yake a kasar Jordan) da sukayi bincike sai sukaga gunkin macen
ya dace da abinda ya faru a yankin shekaru dubunnai da suka gabata (Wallahu
a'alam)
Allah
SWT ya sanardamu irin zunubin da mutanen Annabi Lud AS suke aikatawa na neman
jinsi a cikin Suratul A'araf ayata 80
"Da
Luɗu, a lõkacin daya ce wa mutanensa: "Shin, kuna je wa alfasha, babu kõwa
da ya gabace ku da ita daga halittu?"
81)
"Lalle ne ku, haƙiƙa kuna je wa maza da sha'awa, baicin mata; A'a, ku mutane
ne maɓarnata."
82)
"Kuma babu abin da ya kasance jawabin mutanensa, face ɗai suka ce:
"Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne su, wasumutane ne masu da'awar
tsarki!"
83)
"Sai Muka tsirar da shi, shi da iyalansa, face matarsa, ta kasance daga masu
wanzuwa"
84)
"Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka duba yadda aƙibar masu
laifi ta kasance!"
Haka
kuma bayanin hallakar da tsohuwar (wato matar Annabi Lud AS) da kuma mutanensa
yazo a cikin Suratu Ash-Shu'araa daga ayata 165 har zuwa ayata 175
165)
"Shin kuna je wa maza daga cikin talikai?"
(Yana
nufin kuna luwadi ?)
166)
"Kuma kuna barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga matanku? A'a, ku
mutane ne masu ƙetarewa!"
167)
Suka ce: "Lalle ne haƙiƙa idan ba ka hanu ba, ya Luɗu! Tilas ne kana
kasancewa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
(Ya
zama tilas ga kowanne musulmi yayi hani kuma ya Ƙyamaci wannan ta'asa ta auren
jinsi kamar yanda Annabi Lud AS ya Ƙi sa)
168)
Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙiƙa, ina daga masu ƙinsa."
169)
"Ya Ubangijina! Ka tsirar da ni da iyalina daga abin da suke aikatawa."
170)
Sabõda haka Muka tsirar da shi, Shi da mutanensa gaba ɗaya
(
إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ )
171)
Face wata tsõhuwa a cikin masu wanzuwa
(Wannan
tsohuwar itace matar Annabi Lud AS, wadda masu bincike suka gano gawarta a
suffar dutse wanda ke daukeda sinadarin gishiri a kasar Jordan. Wallahu a'alam)
172)
Sa'an nan kuma Muka darkake wasu
173)
Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi
ya munana
174)
Lalle ne ga wannan, akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance masu imani ba
(To
ammanfa dukda haka idan sun tuba Allah mai Jin Kai Ne ga bayinSa kamar yanda ya
rufe labarin da:)
(
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ
الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ )
175)
Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Hakama
a cikin addinin Judeo-Christian (Juda/Nasara) an haramta wannan babban laifi a
cikin littafin Genesis Surah ta 19 ayata 4 zuwa 11, a cikin labarin Sodom da
Gomorrah (mutanen Annabi Lud AS) sannan kuma Clement na Alexandria da Novatian
ya kawo Ƙwararan hujjojin haramcin madigo da luwadi inda yace yana cikin
al'adun yahudawa Ƙyamatar wasu dabbobi kamar irinsu zomo da weasel saboda nuna
wasu sababbin dabi'u yayin jima'insu (ma'ana suna auren jinsinsu) to indai
yahudawa zasu Ƙyamaci dabba silar wannan mummunar dabi'a ta auren jinsi ai mu
musulmai ne mukafi cancanta mu tsani wannan kazamar dabi'a (Karin bayani yana
cikin littafin "World Of Homosexuality" ma'ana "Duniyar Yan
Luwadi" babin "Addini da Luwadi" shafi na 39, wallafar
shahararriyar Marubuciyar India, Shekuntala Devi)
Zanso
mutane su karanta daya littafin nata mai suna "World of Lesbianism"
ma'ana "Duniyar Yan Madigo"
Wasu
sun maida abin sana'a wadda da ita suke ci suke sha harma su dinka sutura.
Yayin da wasu kuma shaidan ya Ƙawata musu laifin a matsayin dabi'a, Ƙwalamar
son abin duniya da kuma rashin kiyaye al'aura ke sa shaidan ya Ƙawata musu
zunubin a matsayin dabi'a wadda yana wahala kaga mutum ya tuba, sai fa wanda
Allah SWT ya tseratar. Haka kuma yawan kallace-kallacen fina-finai yana taka
muhimmiyar rawa wajen fadawa tarkon zina, madugo da luwadi domin kuwa wasu
abubuwan mostly anan ake koyonsu. Addu'ar da Ma'aiki SAW ya roƘa ta kada Allah
ya halakarda al'ummarsa kamar yanda ya
halakar da na baya itace dalilin da yasa har yanzu Allah bai sa an halakar damu
ba dukda cewar laifuffukan da mukeyi ma sun shafe na al'ummar da suka gabacemu
Gashi
mun tsinci kanmu a wani zamani na hauhawar farashin komai da komai, to wannan
jarabawace kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Mulk ayata 2, kuma
idan mutum ya ci test din ya kiyaye hannunsa daga sata silar talauci, ya kiyaye
abinda ke tsakanin cinyoyinsa (farjinsa kamar yanda Allah ya fada a cikin
Suratul Mu'uminun ayata 5) dakuma abinda ke tsakanin lebbansa (wato harshensa,
Mu'uminun ayata 3) to Allah yana masa albishir da Aljannah (Mu'uminun ayata 10
zuwa 11) idan kuma masu kudi sukai amfanida kudinsu wajen lalata mata da maza
ta hanyar sakasu a wadancan kazaman hanyoyi to saidai muce "Inna rabbaka
labir mirsad" maana "Allah yananan a madakata" yana jiran kowa.
Zabi ya rage namu
Rashin
ambaton Allah shine dalilin dayasa muketa kidimewa, yanzu dai ka duba kaga
mutane duk sun daga hankali akan tashin farashin petrol, to idan Dajjal ya
bayyana wanne halin rikici za'a kasance kenan, kaga ai sai wanda Allah ya
tserar kawai. Kuma daga cikin yawan wadanda zasu bi Dajjal a karon farko sune
yahudawan Kasar IRAN su 70,000 sannan kuma sai mata dayawa da kuma yayan da aka
haifa ta hanyar zina wanda kuma ya tabbata a cikin hadisin Abi Umamah Al-Bahili
RA yace: Ma'aiki SAW yace: "An nunamin a cikin mafarki na ana yiwa wasu
maza da mata azaba a cikin wani kwatami mai tsananin doyi, da na tambaya sai
akacemin ai wannan mazinata ne" (Ibn Khuzaima lambata 1986 da Ibn Hibban
da wasunsu sannan Nasiruddin Albani ya ingantashi a cikin Sahihut Targhib
lambata 991)
A
kula: Wannan fa makomar mazinata kenan wadanda basu tuba ba, ina kuma ga
makomar masu luwadi da madigo ?
Akwai
hadisin Ibn Abbas Radiyallahu anhu, yace Maaiki Sallallahu alaihi wasallam
yace: "Ku kashe Wanda ya aikata aiki irin na mutanen Annabi Lut da Kuma
Wanda aka yiwa aikin"
Al-Tirmidhi
(1456), Abu Dawud (4462) da kuma Ibn Majah (2561)
Al-Albany
ya hassanashi a cikin Sahih al-Tirmidhi
Ga
kuma daya hadisin na Ibn Abbas, Maaiki Sallallahu alaihi wasallam yace
"Ya
Allah ka laanci Wanda ya aikata aiki irin na mutanen Annabi Lut" Sau 3
Yana tsine musu
Hadisin
yana cikin Musnad na Imam Ahmad mai lambata 2915
Shu'aib
al-Arna'ut ya hassanashi a cikin TahƘiƘ al-Musnad
Nidai
kam lamarinnan abun tsoro ne ga wanda yasan girman zunubbin
A
shawarce ina son nayi amfanida wannan damar wajen janyo hankalin iyayenmu da
kuma malamai akan su daina amfanida littafin "Ƙueen Primer" Part II
wajen koyar da yayansu na Nursery da Primary domin kuwa manufar mawallafan
wannan littafin (Nelson Publishers Limited) shine su koyawa yayanmu musulmai aƘidar
auren jinsi (Homosexuality, Lesbianism da ake kirada LGBTQ). A shafi na 5 cikin
littafin sun rubuta "Let us be gay. Let us run" ma'ana "Mu zamo
gay. Mu gudu". Sai kuma shafi na 22 inda suka rubuta "Is this the
way. Yes, let us be gay" ma'ana "Wannan ce hanyar. Eh, mu zamo gay"
(Wal'iyazubillah). Silar hakan tuni gwamnatin jihar kano ta umarci malaman
Nursery da Primary da su gaggauta dakatarda amfani da irin wannan littafin da
makamantanshi wajen koyarda yayanmu yaren English
Hakama
a hanasu kallace-kallacen Tom & Jerry domin kuwa akwai bincike mai zaman
kansa da nayi wanda babu lokacin fayyaceshi anan. Sannan kuma a hana yara
amfanida Games irinsu Subway Surfers wadda itama a hankali a hankali sun fara
bayyana manufarsu ta auren jinsi ta hanyar updating game din da wata sabuwar
fuska mai suna "Rain" yar jihar New York dake Amurka mai sanye da
kaya launukan bakan gizo (Rainbow) wanda daman shine alamar masu aƘidar auren
jinsi (LGBTQ). Na bibiyi posting dinsu inda sukace "Subway Surfers da
hadin gwiwar LGBTQ da kungiyar taimakon marayu na muku maraba da sabon
tsarinsu". Sun saka kungiyar taimakon marayune saboda yawancin marayu
sunada naƘasu da kuma neman taimako na gaggawa musamman idan akwai Ƙarancin
fahimtar addini a taredasu. Kumadai munsan yanda wannan Game ta Subway Surfers
ta samu karbuwa sosai. Saidai muce Allah ya tsare mana imaninmu baki daya
A
karshe ina mai bawa kaina shawara da kuma masu karanta wannan sako da ma sauran
musulmi baki daya, da mu yawaita istighfari, sannan mu yawaita halartar
karatuttukan addini ko don samun bonanzan taka fuka-fukan mala'ikun rahama,
zanso mu nemi littafin "Adabul Mufrad" wallafar Imam Al-Bukhari, mu
karanta littafin "Talbis Iblis" wallafar Ibn Al-Ƙayyim dalibin Ibn
Taimiyya, a littafin zakagane yanda Iblis yake danawa musulmai tarko, kai har
malamai ma bai barsu a bayaba
Sannan
mu karanta littafin "Zaadul Ma'ad" wato "Guzurin AlƘiyama"
na Ibn Al-Ƙayyim" domin kuwa ko sanda aka sakani makarantar boarding saida
aka hadani da Provision (Guzuri) ballantana kuma zuwa Lahira, tabbas ita
yakamata a hadawa guzuri tunda zuwanta ya zama dole
Ya
Allah duk wanda yake da HANNU akan wannan doka ta LGBTQ ka maida bala'in a
Kansa, ka kiyayemu ka tsare Imaninmu
Ku
tayamu yada wannan saƘo, Allah kadai yasan adadin mutanen da zaka zama silar
shiriyarsu
Amsawa
Usman
Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.