Ticker

6/recent/ticker-posts

Kashe-Kashen Ustazai A (H)Abuja

Lafazin 'uztaz' a ƙamus ɗin Hausarmu ta yau da gobe ya fi kama da generic name wanda ake faɗinsa don nuni izuwa ga gungun matasa ƴan kishin addini da ɗaliban ilimi da malaman islamiyya da sauran masu ruwa da tsaki a cikin ƙungiyoyin addini irin Izala da matasan ƴan boko masu yin harkar MSSN, musamman waɗanda ke barin gemu da ɗangale wando.

Akwai ustazai da yawa a cikin birnin tarayyar Nigeria da yankunan dake kewaye da birnin waɗanda suke faɗi-tashi wajen karantawa da neman na-kansu da faɗi-tashin yau da gobe. A cikin wata fira da muka yi da wani mai sa ido akan harkokin ustazanci, ya yi mana fashin baƙi akan nau'o'in ustazai ƴan (H)Abuja inda ya kasa su gida biyar.

1. Ustazai Ƴan Boko

A cikin tawagar ustazan (H)Abuja akwai graduates na fannonin digirin jami'o'i, da ma daktoci masu digirin digirgir, galibinsu mahaddata Alqur'ani ne, ƴan gayu, masu aikin yi da ƙumbar susa. Wasunsu suna ci gaba da harkar kishin addini da aka san su da ita tun kafin su san (H)Abuja. Wasu kuma sun rage tempo amma dai za ka same su da natsuwa da kula da sallah akan lokaci, wasunsu ma limamai ne ko jagorori a harkar addini.

2. Ustazai Zalla

Ustazan dake cikin wannan rukunin sune irin ustazan nan da suke kwararowa (H)Abuja da nufin neman halas ɗin su. Galibin ayyukan da suke yi shine karantarwa a islamiyya ko Tahfeez ko private schools ko lesin a gidajen ƴan Abuja. Galibin waɗannan bayin Allah hustlers ne na bugawa a jarida. Ina ganin irinsu ne Malaminmu Sheikh Albaniy Zaria (RahimahulLah) yake ƙyamar zamansu a (H)Abuja.

3. Ustazai Ritaya

Nau'i na uku na ustazan (H)Abuja ana kiransu da ustazai ne kawai saboda ba a raina asali. Mutane ne waɗanda da can a garuruwansu ƴan kishin addini ne, amma bayan sun shigo birni, Naira ta zauna da gindinta sai suka ajiye ustazanci waje guda suka kama cin duniyarsu da tsinke. Irinsu ne waɗanda za ka ga suna yi wa sauran ustazai gani-gani da ƙoƙarin koya wa Ustazai Zalla hanyoyin bijire wa ustazanci.

4. Ustazai Ruwa-Biyu

Wannan nau'in na ustazai yana burge abokin fira ta. Su ustazai ne waɗanda suka hau level na elevation a harkar ustazanci, rayuwarsu ta yi albarka harkokinsu na garawa. Yawancinsu sun sami ɗaukaka a harkokinsu na kasuwanci ko aikin gwamnati ko siyasa; suna baza kafasiti, amma kuma har yanzu ustazai ne; no shaking. Waɗannan ustazan sune model ɗin da galibin mutane ke yi wa kallon fafet.

5. Ustazai Ba-Wan Ba-Wan

Idan mutum ya fiye zafin kan addini amma kuma ba shi da ilimi mai ƙwari sannan kuma ba shi da ko sisi, to Abuja ba ta shi ba ce. in kuma ya ce ya ji ya gani, to a nan ne za ka same shi ya yi rajista automatically a wannan rukunin. Galibinsu ustazai ne kawai a suna. Ƴan Abuja ba sa son irin waɗannan ustazan saboda ba su da kafasiti sam. Waɗannan ustazan suna da wasu 'false cousins'; sune waɗanda suka tsinci ustazanci rana a tsaka ba tare da sun san lagon karatu ba.

Bissalam.

Kashe-Kashen Ustazai A (H)Abuja

Post a Comment

0 Comments