Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Daukar Hoto

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ɗaukan hoto da muke yi da Handsets ko Camera, Halal Ne Ko Haram ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sunyi saɓani akan hukuncin hoto, inda waɗansu malamai irinsu (Nasirudden Albani) suke da fahimtar haramcin hoto kai tsaye indai ba na laruraba, kamar Fasfo (passport) na aikin hajji ko na shiga wata qasa dai kokuma dai duk wani hoto wanda larurace take hukunta ayishi toh sukace wannan babu laifi saboda larura, amma hakanan kawai dan gayu ko wani abu ayi hoto sukace bai halasta ba.

Amma irinsu ( Usaimin) idan ka duba fatawarsa za ka ga yayi wani tafsiri me ban qaye wanda muma akanshi muke, wato muna tareda fahimtarsu ( usaimin).

Malamin ya ce: haramun ne ayi zanen duk wata halittar Allah, kamar zana hoton mutum ko akuya ko kaza ko jaki kawai mutum ya zauna yana zana hotonsu wannan kaitsaye haramun ne, wannan ya kunshi har hotunan da akesa yara yan primary suna zanawa na dabbobi, dakuma wanda yake sana'ar zana hoton mutane, kawai mutum ya zauna ana kallonshi ana zana surarshi ahoto wannan dukansu haramun ne.

Amma hoto na camera sukace wannan babu laifi, baya cikin kwaikwayon halittar Allah matukar baza'ayi editing ba, shi wannan editing ɗin haramun ne. Masamman sanya fuska a wani gangan jiki da abinda yayi kama da hakan. wannan haramun ne kwarai da gaske.

Amma dai shima hoton cameran sukace kar ayawaita a ɗan yinshi sama sama, musamman ga namiji sukace idan kabiyema yawan ɗaukar hoto sekuma kazama tamkar ɗan daudu.

Aduba fatawa ta (Ibn usaimin) za'aga tafsirin da yayi In shã Allahu, hakama acikin littafin usulut tafsir yadanyi tsokaci gameda hakan.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments