Ticker

6/recent/ticker-posts

Hawan Social Media Ga ‘Ya Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum  mal wai don Allah meye anfanin hawa yanar gizo (social media) ga 'ya mace.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu.

Yanar gizo-gizo (social media) wata kafa ce da Ake Amfanuwa ga wanda yake fatan ya Amfanu da ita, Kamar yadda Kaima haka Yanzu kayi tambaya ta Ilimi. Kuma kana kwance a ɗakinka Zaka ga amasar Tambayarka kuma ka Karu. Haka zalika ita ma mace zata Iya Karuwa da tambayoyi Akan Abinda ya Shige Musu duhu. Kuma su Karu.

Wallahi Akwai Matan da su ne suke bani Number ɗin Mazajensu a sanyasu a group kuma Harma su kira Suyi Addu'a, Sabida Karuwar da Suke yi kuma ta Dalilin Matansu. Kuma Muma Waɗannan Matan Nasu Katangaggu ne a Shirme a social Media. Wannan ne ma yasa Su Kansu sun Yarda Da Suyi. Kuma Wasu Matan Idan Suka turo da Sunansu da Adreshinsu ayi adding ɗinsu a group, zasu ce Amma Ni Matar Aure ce. Duk da zakaga a Wasu group ɗin Shirmammun Mata Suna Rashin Tarbiyya Da Maza.

Haka zalika Mace zatayo downloading na Wa'azuzzuka kuma ta Saurara Sannan ta Karu akan Abinda ba ta sani ba a baya.

 Amma dai ita waya. Yadda Mutum yake haka wayarsa take. idan har Wannan Matar Mutuniyar Kirki ce, to Zaka sami wayarta ma haka. Haka zalika idan ba ta Kirki bace, to wayarta ma Zaka samu ba ta kirki bace.

Wannan ba sai mace ba. Ko da Namiji ne idan ba na kirki bane, haka zaka ga wayarsa. Sabida haka Bai Halatta ga Matar Banza take hawa Network ba. Ma'ana bai kamata take Social Media ba. Domin ba Abinda zata Kara mata In banda Halaka.

Kaga Na Sha ganin Group Ana Tallarsu Na Homosexuality da Lesbianism, ana Tallar Waɗannan groups ɗin.  Ga wadda take da Ra'ayi Idan ta Kirki ce ba Zata Shiga, wadda kuma Lalatacciya ce Zata shiga kuma Irinta ne suke Shiga wannan Group ɗin Kuma Irinta ne Suke Yaɗa wannan Abin. Mutuniyar Kikri kuma ta Kwarai. Babu Abinda waya zata kara mata sai Dai Karuwa.

Allah shine Masani.

WALLAHU TA'ALAH A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments