Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ana Biyan Bashin Azumi Da Istigfari?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatullahi, malam ya aiki? Tambaya ita ce, ina da makociya wacce shekarunta sun ja sai ta zo ta tambaye ni a kan cewa shekaru 25 zuwa 27 a lokacin da ta haifi 'yar autar ta da wacce take binta ta sha azumi a dalilin haihuwa a Ramadana kuma bata ranka shi ba sai daga baya aka fada mata sai ta ranka, sai tazo guna ni kuma sai na tambaya mata malaminmu a kan matsayin ta sai ya ce ba sai ta ranka ba kuma ba za ta ciyar ba sai dai ta yi istigfari na fada mata. Amma yanzu haka ba ta da lafiya sosai, shine nake son in kara sani shin waccan fatawa daidai ce ko kuwa saboda azumin da aka lissafa ya kai azumi 40? Shin ya zan yi dan a halin yanzu da wuya in za ta iya azumi saboda rashin lafiyar, dan ta kai wata hudu komai sai an mata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám. 'yar uwa an amsa makamanciyar wannan tambaya a baya da dama, malaman Musulunci sun yi maganganu kusan guda huɗu a kan matar da ta sha azumi saboda ciki ko shayarwa, amma maganar da ta fi rinjaye, kuma wadda ita ce mafi yawan malamai suke tafiya a kai ita ce:

Duk matar da ta sha azumi saboda ciki ko shayarwa, to hukuncinta shi ne za ta rama (ranka) wannan azumin ne, ba ciyarwa za ta yi ba, kuma wannan ita ce fahimta mafi rinjaye a wurin malamai.

Idan kuma rashin lafiya ya hana ta rankawa, to za a duba ciwon da take fama da shi ne, idan likitoci ne suka tabbatar da ciwon da take fama da shi ba wanda akan warke ba ne a iliminsu, to wannan ita ce za ta ciyar ba sai ta rama ba, amma idan har ciwon da take fama da shi ana iya warkewa, to wannan ba ciyarwa za ta yi ba ranka azumin za ta yi.

Saboda haka, waccan fatawar da aka ba ta na cewa ba sai ta rama azumin ba, kuma ba sai ta ciyar ba istigfari kawai za ta yi, wannan kuskure ne babu ko shakka, istigfarin zai yi mata amfani ne a kan jinkirin ramawa da ta yi, amma bai wadatar wurin biyan mata bashin wancan azumin da ake bin ta ba.

Sai dai idan ya kasance ta tsufa da yawa ne, ta yadda ba za ta iya yin azumi ba saboda wannan gajiyawar ta tsufa, to a nan shi ne za ta iya ciyarwa, amma asali abin da ke kanta shi ne rankawa ba ciyarwa ko istigfari ba, lallurar tsufar da zai hana ta ramawa ne ya sa aka ce za ta ciyar ba rankawa (ramawa) ba.

Domin qarin bayani a duba Assharhul Mumti'u Ala Zaadil Mustaqni'i (6/347-350).

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎��👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments