Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Yake Cikin Sallar Nafila Sai Aka Tayar Da Iqama

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Menene hukuncin wanda yake cikin nafila sai aka tayar da iqama? Zai dakatar ne ko kuwa zai iya kammalawa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Akwai maganganun malamai mabambanta har guda tara (9) a kan wannan mas’alar, kamar yadda mai littafin Al-Bahrul Muheetut Thajjaj (15/250-252) ya kawo. 

Amma maganar da ta fi ita ce wacce ta dace da maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce

« إِذَا أُقِيمَتِ الصَّلَاةُ فَلَا صَلَاةَ إِلَّا الْمَكْتُوبَةُ »

Idan aka tayar da iqama to babu wata sallah sai wannan ta farillar. (Sahih Muslim: 710).

A nan kowace irin nafila ba ta halatta ba a lokacin da aka fara tayar da iƙama. Kuma da zaran an fara tayar da iƙamar shikenan nafilar ta warware, ba sai shi mai sallar ya warware ta ba.

Akwai ayar da waɗansu malamai suka kafa hujja da ita a kan halatta cigaba da nafilar matuƙar dai ba zai rasa kabbara ko raka’ar farko ba, wato

وَلَا تُبْطِلُوا أَعْمَالَكُمْ

Kuma kar ku ɓata ayyukanku. (Surah Muhammad: 33).

Malaman da suke da wancan ra’ayin sun amsa da cewa, a nan ai ba mai sallar shi da kansa ne ya ɓata nafilar ba. Shari’ar musulunci ce ta ɓata ta, kamar yadda nassin hadisin da ke sama ya nuna. Al-Bahrul Muheetut Thajjaj (15/253).

Amma kamar yadda ya gabata, akwai waɗansu malaman da suka zaɓi cewa, matuƙar dai ba zai rasa kabbarar farko na sallar da aka tayar da iƙamarta ba, saboda ya riga ya yi nisa a cikin nafilar ko domin limamin yana daɗewa kafin ya yi kabbarar harama, to a nan suna ganin zai iya cigaba har ya kammala nafilar. (Al-Mausuu’atul Fiqhiyyah: 1/356, As-Sharhul Mumti’: 4/164).  

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments