Yadda Akeyin Taimama

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mal. Ina da tambaya

    Ya akeyin taimama? kuma, a wanne guri ya hallata ayita?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Allah ta’ala yayi umarni da yin taimama ayi sallah idan aka rasa ruwan wanka ko ruwan alwala. Acikin suratun Nisa’i da suratul Ma’idah.

    Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yayi taimama, kuma ya koyar da yadda ake yin taimama. Kamar yadda yazo a hadisan Ammar Bn Yasir a riwayar Bukhari Da Muslim da Ibn Majah.

    Idan za ayi taimama sai a sami guri mai tsafta, kamar ƙasa ko yashi ko birji ko dutse, da dukkan dangogin ƙasa.

    Sai ayi BASMALA a buga hannu a gurin, sannan a karkaɗe idan wani abu ya maƙale, sai a shafa a fuska, kamar yadda mutum yake wanke fuska a lokacin da yake yin alwala, faɗinsa daga kunne zuwa ɗaya kunnen, tsawonta daga goshi zuwa haɓa. Sai ya ƙara buga hannunsa a ƙasa ya shafi tafin hannunsa zuwa maɗaurar agogo gaba da baya ciki da waje, ya cuɗa tsakanin yatsunsa. Wannan shine yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya siffantwa Ammar Bn Yasir yadda zaiyi taimama a riwayar Bukhari da Muslim.

    Amma sake buga hannu a kasa kafin ayi shafar hannu yazo a riwayar Ibn Majah shaikh Albani ya inganta ta. A cikin sahihu sunan abi Dauda.

    Sai dai wasu malamai suna ganin a wajan shafar hannu sai an kawo har gwiwar hannu kamar yadda akeyi a wajan alwala, kamar yadda aka ruwaito daga Abdullah Ɗan Umar yana yin haka, amma riwayar Ammar tafi ƙarfi, tunda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya koya masa da kansa.

    1. Idan mutum yayi taimama kafin yayi sallah sai ya sami ruwa, taimama ta ɓaci wajibi yayi alwala ko wanka kafin yayi sallah.

    2. Idan mai janaba yayi taimama yayi sallah, daga baya sai ya sami ruwa, sai yayi wanka ba tare da ya sake sallar da yayi ba.

    3. Idan mutum yayi taimama yana cikin sallah sai ruwa ya samu, sai ya yanke sallar yayi amfani da ruwan.

    4. Idan mutum yayi taimama yana cikin Sallah sai ya tuna ashe yana da ruwa, a kusa, sai ya yanke sallar, yayi amfani da ruwan.

    5. Anayin taimama ne bayan an rasa ruwa, kuma ba'a cewa an rasa ruwa sai an nema, idan mutum yanajin zai iya samun ruwa kafin lokacin salla ya fita, sai ya jinkirta zuwa ƙarshen lokaci, amma kada ya bari lokaci ya fita bai yi salla ba.

    6. Idan mutum ya farka daga bacci sai yaga yayi mafarki, gashi ana tsananin sanyi, yana tsoran idan yayi amfani da ruwa zai sami rashin lafiya, sai yayi taimama yayi salla kafin lokaci ya fita, daga baya sai yayi wanka.

    7. Ba'ayin taimama domin a sami jam’in salla kawai, Anayin taimama idan ana tsoran lokaci zai fita babu ruwa ko rashin lafiya ko tsoran samun larura idan anyi amfani da ruwan.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.