Kisan da Sojijin Kasar nan suka yiwa Musulmi ‘yan bikin Maulidi a Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta hanyar jefa musu bom har sau biyu wanda hakan ya jawo asarar rayuka wajen 100 kuma ya jikkata dubbai abin Allah wadai ne.
Na ji da yawa wasu na kwatanta irin yadda za ta kasance da
wannan ganganci da rashin hankalin ya faru a kudancin Najeriya bori da
tanshintashinan da zai biyo baya daga matasansu da kafofin yada labaransu na
rashin yarda ko kadan da al'amarin.
Wasu a nuna rashin jin dadinsu na shiru da suka ji masu
mulki, manyan ‘yan siyasa, masarautu, malaman boko da na Islama, manazarta,
fitattu, sanannu a kowanne fage na rayuwa, masu fashin baki da uwa uba kafofin
yada labarai na Arewa suka yi akai.
Suke cewa da a Kudu hakan ta faru da gaba daya da kakkausar
murya za su yo can su ruda kasar ta hanyar amsa amon kokawa da korafin dole a
yi maganin ta'addanci da aka tafka wa wadannan bayin Allaah da aka raba su da
rayukansu ba su ji ba su gani ba.
Za kuma su ajiye duk wasu bambance- bambancen dake
tsakaninsu da dukkan abinda suke yi komai muhimmancinsa a garesu su ci gaba da
ruruta wutar zancen har sai duniya ta ji sannan a nemi ba'asi har ta kai
Amurka, Turai da ko'ina su nemi a yiwa wadanda aka zalunta adalci a biya su
diyya.
2!!
Shi ne wasu suka kama korafin rashin bude kafafen yada
labarai a wajen manyan Arewa suna cewa da an kakkafa su da muma zamu samu murya
daya ta isar da sakonninmu yadda duniya baki daya za ta dinga jin mene ne
damuwar Arewa da al'umarta.
A wannan ga6a ne na fito nake yi musu bayani cewa ba bude
kafofin yada labaran ba ne matsalar ba amma dalilin bude su shi ne ginshiki.
Sau da dama ana kafa gidajen radiyo da talabijin da jaridu ne saboda wasu
muhimman dalilai
Mafi akasarin kafafen yada labarai a Arewa ba a bude su da
manufar wadannan dalilai wato kare hakki da kwatar yanci, kare addini, hana
gu6ata harshe, bunkasa al'ada, sayarwa duniya gargajiyar al'uma, karewa yanki
hakkinta da dai makamantansu.
Sai dai anan Arewa da yawayawan kafofin aikin jarida ana
kafa su don kusan abu biyu ko uku. Ga su kamar haka: Na farko kare mutumcin kai
da samun kafa ta maida martani ga ‘yan hamayya ko ‘yan adawa da duk wani wanda
aka dauka makiyi ne.
Na biyu saboda kasuwanci, neman kudi ko jari hujja. Muddun
kudi za su samu daga gudanar da harkar sadarwa da isar da sako to duk wani abu
na tsare martabar al'uma ko shiyya ko bangare baya cikin lissafi sai dai ko ya
zama dan karere ko ya yi rakiyar nufi.
Sannan na uku saboda ya zama mabudin shiga kofofin duk inda
mai kafar yada labaran zai iya shiga don nemawa kansa a karon farko wata dama
daga masu mulki, manyan ‘yan kasuwa, masu fada aji cikin al'umar kasar ko
yankin kai ko ma duniya.
Shi ya sa za ka ga da yawa kafofin sadarwarmu a Arewacin
Najeriya irin wannan cin mutumci, tozarta mutanenmu, danne hakkinmu a majalisa,
rajin kare hakkin bil Adama, tauyewa ‘yan shiyyar damarmakinsu a wajen daukar
aiki, rabata daidai a dukiyar Kasa da dai sauransu duk ba su dame su ba.
Baya da wannan in an bi ta 6arawo to abi ta mabi sahu. Akwai
‘yan Arewa da dama a Soshal Midiya in kuka duba shin kishin al'umarmu yana daga
cikin abinda yake damunsu ko akidarsu ko manufar kasancewarsu a kafofin sada
zumanta?
A hakikanin gaskiya da dama a cikinmu nemawa al'umarmu hakkinta
ba ya daga cikin aniyarmu na hawa soshal midiya. Abin da mafi yawancinmu suka
sa a gaba shi ne nishadi, barkwanci, sharholiya, soki burutsu, bambadanci,
tumasanci da dai ire-irensu.
Ba za ka ga wani abu da ya shafi kwatarwa jama'armu kasonsu
ko yaye musu kunci ko yakar rashin adalcin da ake nuna musu ‘yan dandali
intanet sun yi rubutu ko dogon bayani ko bidiyo ko shiyarin ko sharhi ko fashin
baki ko tambihi da makamantansu akai ba.
Duk wanda yake da ja ya je yayi bincike a TikTok, Fesbuk,
Instagiram, Tuwita, Waz'Af da sauransu ya ga mene ne ‘yan Arewa suka maida
hankalinsu kai kama daga kallo, dora kwanten wato kirkira, saukewa daga shafuka
za ku ga wAllaahi shiririta ce.
To yanzu a hakan shi ne sauran mutan duniya za su dauka mun
damu da kanmu, rayuwarmu, ci gabanmu da nemawa kanmu kima da daraja? Ku taya ni
dubawa don Allaah. Wannan na daga cikin dalilan da yasa kowama yake ganin damar
duk wani mutumin Arewa ba a bakin komai yake ba.
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.