Ticker

6/recent/ticker-posts

Waye Ya Tura ni?

Wani Sarki ne ya sa gasa akan duk wanda ya shiga babbab Rafin garin yayi wanka, to zai auri 'Yar Sarki, ko a ba shi billion ɗaya, ko rabin garin. Wanda cikin rafin nnan akwai kadoji, dorinar ruwa da sharks da dai sauransu. 

Ranar gasar, ana tsaye jikum-jikum an rasa wanda zai fada, kawai sai aka ji taaaaannnjjjjjaaaaammmmm,

Ana dubawa sai aka ga Ɗan Fulani Yana bunjum-bunjum a rafi. Yana fitowa aka yi ihuuuuu!!!!. Sai ya tafi kai tsaye gurin sarki. Sai sarki yace "me kake so?, 'ya ta?" , Ɗan Fullo ya ce "a'a", Sarki yace "Biliyan ɗaya?" Ɗan Fullo yace "a'a", Sarki yace "ko rabin gari?" 

Ɗan Fullo yace "a'a", Sarki yace "toh me kake so?" Sai Ɗan Fullo yace "so na ke a nuna min uban da ya tura ni!!" 😂😂😂 

Ashe Wai tura shi aka yi...😂😂😂Post a Comment

0 Comments