Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Wannan wata wasa ce dangin dara. Sau da dama akan yi caca da ita. Wato a sanya kuɗi kan cewa duk wanda ya yi nasara a wasar, to zai mallake kuɗin. Wani lokaci akan sanya wani bu daban da ba kuɗi ba, kamar tufafi da makamantansu. Maza manya ne suka fi gudanar da wannan wasa. Sai dai akan samu wasu lokuta da yara ke yi, musamman waɗanda suka gani daga manya. Mutane biyu ne suke gudanar da ita, sai dai za su iya fin yawan haka yayin da aka yi taron dangi.
Wuri Da Lokacin Wasa
i.
Akan
gudar da wannan wasa a filayen caca, da keɓaɓɓun wurare cikin kasuwanni. Yara sukan yi a
gindin inuwowin bishiyoyi a cikin unguwanni.
ii.
Ana
gudanar da wannan wasa da hantsi ko rana ko ma da yamma. Sai dai ba a faye yin
ta da dare ba.
Kayan Aiki
i.
Ƙodagon goruba ko taura ko ƙwallon
mangwaro ko duwatsu ko makamantansu.
Yadda Ake Wasa
Akan
zana gidajen dara kimanin talatin da shida (36) ko a yi ‘yan gurabu yawan
wannan adadi. Akan yi gidajen daran shiɗa a tsaye, shida kuma a kwance, jere da
juna reras. Daga nan kowa daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa zai zaɓi nau’in ‘ya’yan da
zai yi amfani da su (ko dai tsinke ko dutse ko ƙwallon mangwaro ko
na taura ko ƙwadagon goruba da makamantansu). Kowa zai ɗauki ‘ya’ya goma
sha biyu ya zuba su ta hanyar jerewa a layuka biyu na farko da ke gabansa. A
wani lokaci akan yi taron dangi, wato mutane biyu ko sama da haka su kasance
suna tafiya a tare. Wato su yi shawara kafin ɗayansu ya yi tafiya. Wani lokaci
kuma za a samu wani mutum da ba ya cikin wasa amma yana sanya baki a wasan. A
irin haka, abokin wasan wanda ake sa wa baki zai iya ƙin
yarda, musamman idan wasar ba ta buqatar wani ya sa baki.
Daga
nan mai tafiyar farko zai fara tafiya ta hanyar tura ɗa zuwa gidan da ke
gaba da shi. Za su ci gaba da tafiya karɓa-karɓa. Akan tura ɗa zuwa gidan gaba ko baya ko gefe.
Yayin da ‘ya’ya biyu na ‘yan wasa daban-daban suka mannu da juna, mai tafiya
zai cinye wannan ɗa da ke jikin ɗansa (idan akwai
gidan da zai iya sauka a bayan ɗan). Idan kuwa mai wasa ya kai ga shiga ɗaya daga cikin
gidaje biyu da ke kusurwa a gaban abokin karawarsa, to ya shiga Sarki. Saboda
haka, za a naɗa shi Sarki ta
hanyar ƙara ɗa ɗaya a kan wannan ɗa da ya shiga Sarki da shi. Sarki yana da ikon
yin doguwar tafiya. Saboda haka zai iya
cin ɗa da ke nesa da
shi. Amma Sarki ba zai iya cin wani Sarkin daga nesa ba. Ɗa
kuwa ba zai iya cin Sarki ba, ko da suna kusa da juna, sai dai idan ya rage ɗa ɗaya ne kacal ga mai
wasa.
Wasu
lokuta mai wasa kan ambaci: “girjim” daidai lokacin da ya ɗaga ɗa daga wani gida
zuwa wani gida, musamman domin zolaya. Hakan na faruwa yayin da ya sunsuni/shinshini
ƙamshin
nasara kan abokin karawarsa, wato domin zolaya. Yayin da aka cinye ‘ya’ya mai
wasa ko aka kulle shi gaba ɗaya, to an kore shi ke nan daga wasan a wannan turmin.
Wasu Daga Cikin Dokokin Wasa
Duk
da akan samu bambance-bambancen dokokin wasar daga wuri zuwa wuri, an yi ƙoƙarin
kalato wasau daga cikinsu kamar haka:
i.
Sanya
baki a wasar da ba ta sa baki laifi ne.
ii.
Idan
ɗan wasa ya samu
damar ci, sai bai ci ba a wasar da take tsakar ci, to za a ɗauke wannan ɗan da ya ƙi
ci da shi.
iii.
Yayin
da mai wasa ya dace ya ɗauki akalar wasan
da ke ci sai ya yi wata tafiya daban, to damar lokacin was an/kakar was an
wannan lokaci ta huce/wuce.
iv.
Duk
wanda aka shiga ɗaya daga cikin
kusurwowin gabansa biyu, dole ya naɗa wa abokin wasansa Sarki.
v.
Sarki
yana fawar doguwar tafiya.
vi.
Ɗa ba ya iya cin Sarki sai ya kasance shi kaɗai ne ya saura a gidan
mai wasa.
vii.
Sarki
zai iya cin ɗa daga nesa.
viii.
Sarki
ba zai iya cin Sarki daga nesa ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.