Fajaruddeen (Kashi na 10)

    Fatiha ce zaune kamar kullim a gurin zamamta iska na kaɗawa GSP ne dasu kasantuwar wancan satin malamin baizo ba yasata shantakewa a gurin tanata kallon hanya atunaninta ko idaninta zasu hango mata yayanta Deeni tafe dan yanzu in ba ta ganshi ba sunyi hira ba ta jin daɗi ita kanta har mamakin irin shaƙuwar da tai da shi tayi take.

     Wani ɗan ajinsu ne ya zo wucewa ya ce a'a fatiha halan baki san malam ya zo ba ta ce wallahi fa ya ce yama ɗan jima ta miƙe na gode tai ajinsu dan tana cikin ɗaliban da ko kaɗan basa san missing ɗin class.

     Tun daga farkon matattakal takejin muryar malamin kamar tasan ta sedai ta kasa tunano ko a ina ne tasan muryar ilai kuwa tana zuwa bakin ajin taga yayanta Deeni gabanta ya faɗi aranta ta ce na shiga uku ashe malami ne ba student ba ta daure tabi bayan student ɗin dake ƙoƙarin shiga.

     Dakatar dasu yai yana faɗin yanzu ake zuwa aji sukai tsuru tsuru kufita kuban waje ta ce towo ashe dai shi ma ya iya faɗa yana kallon ta kamar ya ce su dawo ya basar kawai dan ko kaɗan baya san karya tsarinsa.

     Koda ya fito fatiha ya kira dan ko kaɗan baiji daɗin korar su dayai ba karo na farko da yaji babu daɗi dan ya hana ɗalibansa makararru shiga aji saidai shi mutunne mai san tsaiwa kan bakansa hakan ya sa yaka sa barinsu shiga inzaki tafi gida ki zo department ɗinmu ina san magana dake ta ce to ya kashe wayarsa.

     Kai tsaye daga masallacin agric sociology ta nufa kasantuwar basu da nisa sosai ya sa ba ta jima ba ta ƙara sa ba ta kirashi ba wasu Yan mata da tagani tai gunsu sallama tai masu a wulaƙance suka amsa wataƙil kodan sunga ba wata shigar kirki taiba atamfar jikinta ma duk ta koɗe kai baka ce ‘yar jami'a ceba.

     ba ta damu da yadda suka amsa mata ba ta ce dan Allah inatambayar office ɗin malam fajar ɗaya daga cikinsu ta kwatanta ma tai mata godiya tai inda aka kwatanta mata.

     Kamar ko yaushe Farida ce zaune cikin motarta tana ɗan duba wadu takardu yayin da lokaci lokaci takan ɗaga ido ta kalli office ɗin malam fajar ko zataga fitowarsa dan hakan yazame mata jiki kullin sai taga tafiyarsa take iya tafiya itama tun ma'u na mata faɗa harta dena.

     Gabanta ne ya faɗi ganin mace na kwankwasa ƙofar ba ta jimaba aka buɗe ta shige duda daga inda take tana iya hango anbar ƙofar abuɗe saidai hankalinta ya kasa kwantawa kishi duk ya rufeta to wai ita wannan wace a'ina take ita dai tasan bama a Faculty ɗinsu take ba bare ta ce a department ɗin sociology take yadda ta fuskanta sun saba sosai dan in ba ta manta ba ita tagani rannan ran hutu ya ƙaryata ran hutu.

     Sai da Fatiha ta jira ya ɗan kammala wasu abubuwa kamin su fito hakan ya sa suka ɗan jima kamin su fito haushi duk ya cika farida.

     Fatiha ce ta fara fitowa kamin ya fito ya rufe ƙofar suka jera sukai gun motarsa suna ɗan taɓa hira suna shiga motar yaja suka bar Faculty ɗin yan mata masu sansa haushi duk ya cika su duk zatonsu budurwarsa ce musanman ganin yadda yake ta annashuwa wasunsu ma zasu iya cewa yau shi ne karo na farko da suka taɓa ganin fuskarsa a sake da annuri.

     Suna tafe a mota suna hira nan fatiha ta ce yah Deen ashe daman kai malam ne baka taɓa faɗan ba wallahi duk zatona kana MS ɗinka ne yai murmushi ba tare da ba ta amsar tambayar ta ya fara mata faɗan latti tahau ba shi haƙuri tana faɗin wallahi banyi zaton za ka zoba ganin malam GSP basa san zuwa yai murmushi shi ke nan na haƙura ya sa hannu ya ɗauko handout ya miƙa mata ta amsa ga karun yaunan sauran a kuma makara tahau godiya.

     Ya ce ai nai mamaki da kika makara keda na sanki kamin lokaci ya cika kin shiga aji kamar ta ce ai jiranka na tsaya yi ta basar ta ce wallahi tunani ne yai gaba dani ya ce kin gani ko shi ya sa hanaki wannan tunanin karfa ki je tunanin nan ya mai da mun da ƙanwa daƙiƙiya tai murmushin jin daɗin kalamansa ba tare da ta ce komai ba.

     Da kujerar motar ta ɗan kishin giɗa kalamansa na mata dawo mata tana jin daɗi shiru ne yaɗan ratsa kamin ya ce fatiha ahankula ta ɗago ta kalle shi ba tare da ta ce na'am ba ya ce kindai ƙiyimun kwatancen gidanku ko gabanta ya yanke ya faɗi bai damu da rashin amsarta ba ya ce kinsan me yau dole kimin kwatance ko kuma ki bari in kaiki in gani da kaina.

    Tai shiru bakice komai ba kwatancen ne ko kuwa kaiwar ce ya faɗa idanunsa na kallon titi tunani tai inta kwatanta masa tabbas in ya zo ba lallai ya gane ba garin tambaya kuma tasan zai iya jiyo abin da zai iya sa ya fita sabgarta itakam ayanzu ba ta san abin da zai rabata da shi ina jinki nan ta kwatanta masa ta ce muje yaji daɗi dan bezaton za ta ce yakaitan ba.

     Seda taga sun kusa unguwar ne tunin karta jefa babansu ya zo yakawo mata hankalinta ya tashi saida ba damar ta ce ya ajiye ta dan kwarjini yake mata musaman ma dai yau ɗinnan ta rasa me yasa.

     Har ƙofar gida ya kaita tai tai ya tsaya yaƙi ya ce zai yi wani abu kedai ki shirya ganina dan kuwa duk randa kikai fashi zaki ganni tai dariya ashe bazan ganka ba dan ba batun fashi yai dariya za mu gani ai tai masa godiya yaja motarsa ta tafi ta jima tana kallon inda yabi ranta cike da tunanin anya kuwa batai kuskure ba kawo shi gidansu tasan fa hakan na nufin rabuwarsu indai ya gano ko ita wace.

     Shi kuwa kai tsaye daga nan gidan su Faiza ya wuce saida ya shiga Jifato na ƙofar nasarawa ya mata siyayya kamin ya wuce kamar ya koma gida ya kuma shiryawa saidai tunawa da yai da yadda sukai da ummamsa ya sa ya fasa dan bayasam yaje ta ce yaje ya ce mata a'a ranta ya kuma ɓaci.

     Ya jima a ƙofar gidan kamar ya kirata awaya dan duk yanada numbobin ɗalibansa na makarantar dare yadai fasa yahau baza ido ko zai hango yaro ya tura.

     Bashir ne ya parker motarsa bayan ta fajar ganin zai shiga gidan ya sa fajar saurin masa sallama Bashir ya amsa yana miƙa masa hannu sukai musabaha fajar ya ce dan Allah faiza za ka turomin inka shiga gaban Bashir ya faɗi kamar ya ce bazai baza'a turotan ba ya daure ya ce ok to inji wa.

     Ace mata inji Fajarudden gabam Bashir ya faɗi dan ya jima da riƙe wannan sunan a kwakwalwar sa ok kawai ya iya cewa kamin ya shiga gidan zuciyar sa na tafarfasa ji yake kamar ya koma ya mammake fajar kasa shiga gidan yai rasa abinyi yai yayin da a ɓangaren fajar yake ta saƙa da warwarar abin da zai ce mata.....

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

     Daƙyar ya daure ya shiga ciki suka gaisa da umman su Fa'izan kafin ya ce umma ina kuwa mutuniyar ta nuna masa bayan ɗaki inda Fa'izan take ɗan shuke shuke tana can tana fama da sana'ar tata bai ce komai ba ya wuce bayan ɗakin umma ta bi shi da kallo dan ba haka ta saba ganinsa ba.

     Dakyar ya iya riƙe fushinsa ya ƙaƙaro murmushi lokacin da ya ƙarasa inda take tana ganinsa ta faɗaɗa murmushinta a'a yah kaine da yanma haka yai murmushi bari kawai ina zaune na ji ina san ganin yar ƙanwata nace bari kawai in zo ta ce ashe duk ɗaya muke nima tun da na tashi naketa tunaninka ya ce ba wani nan ta ce wallahi murmushi yai gami da cewa.

     Albishirinki ta ce goro ya ce da zan shigo nafa haɗu da mutumin ya ce in turo ki ta ɗan kalle shi da alamun rashin fahinta wake nan ta tambaya malaminku man malam fajar yah bafa na san zaulaya kasani shiyasa ai bana zaulayarki kinsani da gaske nake yana ƙofar gida ta miƙe shi ne yah baka faɗan ba na san yana can yanata jirana Allah ya sa ma bai tafi ba.

     Yadda jikinta ke rawa ya sa shi jin tausayin kansa na san maso wani shi ke nan jeki ki dawo se amin hukunci tai tsakar gida ta faɗawa ummanta tai waje.

     A ƙofar gida ta ganshi jikin motarsa ta sameshi ta masa iso zuwa cikin farfajiya ƙanwar ta ce ta kawo masa ruwa nan suka gaisa inda shiru ya biyo baya.

     Fajar ne ya katse shirun da faɗin na san kina mamakin ganina ko ta girgiza kai alamar a'a ya ce saboda me tai murmushi ai ba yau ka taɓa zuwa ba kwanaki ma ai kazo kan registration ɗina na jamb oh hakane bazakiyi mamaki ba kam.

     In tambaye ki mana ina ji ta faɗa yanzu ace ki samu miji ya ce aure yakeso ki yi karatun kyayi agidansa me zakice tai murmushi indai ya yadda ai aure baya hana karatu kamar yadda karatu be hana sure haka ka taɓa faɗa mana lokacin sallamar ummu'aimana hakane anman ba abun da nace zaki faɗanba ra'ayinki nake sanji ehto in mijin ya amince zan yi karatun ai babu komi watau dai kin yadda zaki iya aure kafin kammala sch tai murmushi eh.

     Ok to yanzu misali in cikin malaman makarantar dare suka ce suna san aurenki me zakiyi eh to zan amince sabida ina jin sunsan halina sosai nima aƙalla na fahinci wani cikin halinsu yai murmushi zaki iya zama gidan su mijinki matsayin gidan auren ki ai nanma gidanmu ne mezai hana ok shiru ya biyo baya.

     Ya jima yana jinjina abin da yake san faɗa kafin ya ce yanzu kinsan me ya kawoni ta ce eh cike da mamaki ya ce me ya kawoni tai murmushi nasam bazai wuce kan admission ba yai murmushi admission ai ba'a fara ba.

     Anyway ba shi ya kawoni Faiza ya kira sunanta cikin sanyayyar murya ta ɗago ta kalle shi ganin ita yake kallo ya sa ta saurin ƙasa da kai dan bazata iya jurar kallon kallo da shi ba muryarsa ta tsinkaya na faɗin Fa'iza zaki iya aurena a tsorace ta ɗago ta kalle shi har lokacin ita yake kallo yanayin fuskarsa ya nuna mata tabbacin abin da yake faɗe kuma mai maitawa yai zaki aureni cikin rawar murya take faɗin uhmm hmm murmushi yai ganin duk ta rikice ya san za'ai haka.

     Katse mata maganar yai da faɗin ni zan tafi in kin yanke shawara ki turon da saƙo ko wane anman in amsarki No ce bana buƙatar saƙonki I will consider ur silent as No sa'annan duk yadda amsarki ta kasance yes or no bana buƙatar tere re in lokaci yai kowa zaiji motarsa ya ƙarasa ya ɗauko abin da ya siyo mata bai jira cewarta ba yabar area ɗin.

     Inda yabi ta bi itama da kallo ji take kamar mafarkin da ta saba yine ace wai yau ita malam ya zo yana tambaya ko za ta aureshi inama inama zai iya ganin zuciyarta dan ya san amsarta yes ce.

     Jin shiru ya sa Bashir fitowa sai dai ita kaɗai ya gani a gurin azaune yaji daɗi aransa kenan ba wani abu mai mahimmanci bane ya kawo shi dan yaga alamun ya jima da tafiya har ya zauna batasan ya zauna ba yaɗan taɓo ta tai saurin kallonsa ƙanwata tunanin me kike haka yah wai ba mafarki nake ba.

     Yai murmushi idanki biyu itama murmushin tai haka idona biyu dan bana ganinka a mafarki me ya faru ne tai saurin gyara zama yah wai malam Deeni ne ya ce zai aureni atsorace ya ce aure kuma eh yah ke me kika ce masa kasa magana nai ya miƙe yai waje batare da ya ma koma ciki yaima umma sallama ba.

     Motarma kasa janta yai sai ɗan sahu ya hau yana zuwa gida ya shige toilet ya saki ruwa akansa ya jima ruwa na zuba akansa kafin ya daure ya dawo falo nan ya zube kan gado ransa na masa suya ga kukanma ya kasazuwa.

     Ita kuwa Fa'iza tun tafiyar malam take tsara wane irin saƙo za ta turawa malam saidai ta kasa tsaida matsaya kan wane iri ya kamata.

     Shikuwa Fajarudden koda ya koma gida ya faɗawa ummansa yadda sukai ta ji daɗin zuwan da yai aranta tana fatan Allah ya sa ta amince ɗin.

     Koda ya koma ɗakinsa tunanin maganganunsu da yarin yai yaitayi karo na farko da ya tsaya yai tunani akan yarinyar tabbas ya san tana da tarbiyya bai taɓa tsayawa ya mata kallon tsaf ba sai yau ya fahinci abubuwa da dama aransa game da ita yakuma tabbatar ma kansa she will a good wife materia anyway zan yi ƙoƙarin koyawa kaina san ta ko auren mu yayi daɗi tun da dai zama ne na har abada.

     Kwana biyun nan kullin cikin duba wayarsa yake ko zaiga saƙonta saidai shiru shi kansa baisan dalilin sa na damuwa da rashin saƙon ba is that because i don't want be rejected ya tambayi kansa har mamakin damuwarsa yake.

     Yau ne kwana na ukun tun safe yake duba wayarsa ko zaiga saƙonta saidai har lokacin kwanciya baccinsa babu message hakan ya sa kawai ya kashe wayarsa

     Ita kuwa faiza rasa mai za ta rubuta tai ta kira Bashir wayarsa akashe ta tura masa saƙo babu alamar ma saƙon yaje kundum bala tai wajen sha biyu ta tura masa night greeting ta kashe wayarta.

     Juyi kawai yake ya kasa ma baccin baisan dalilinsa na kunna waya ba Fatiha ya kira awaya ta jima tana ringing kan ta ɗaga da alamu daga bacci ta farka sun jima suna hira kafin suyi sallama kowa ya kashe.

     Yasaba da fatiha ya shaƙu da ita sosai yake samun comfort in yana tare da shi kansa ya san ya shaƙu da yarinyar yana jinta aransa ya damu sosai da damurta ya san shi mutunne me tausayin mutane sedai ya san yadda ya damu da fatiha daban yake da kowa, ko ayanzu ma da sukai waya sai yaji duk damuwarsa ta ragu hankalinsa ya kwanta da batun fatiha.

     Alamar saƙo da yaji ya sa shi ɗaukar wayarsa murmushi yai kawai ganin ba wani abu mai mahimmanci ta ce ba saidai aƙalla ya san message ɗinta means accepting him.

     Alwala yai ya zo danyin nafila nan ya roƙi Allah inda alkairi Allah ya tabbatar nace Amin ina nai gidanmu dan bacci ya fara ɗibata.

    Wasa wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin malam da faiza shi da kansa har mamakin yadda ya sake jiki suke soyayya yake ji yake kamar ba shi ba yayin da Faiza takejin tamkar tafi kowacce mace sa'a a soyayya.

     ***

    Abubuwa sunbi sun cakuɗewa farida ɓan gare guda inta duba soyayyar Fajarudden da bai san tanai ba da ta mamaye mata zuciya yadda har abin na ƙoƙarin taɓa karatunta dan tuni ya taɓa rayuwar farin cikin da ada take ciki yayin da awani ɓarin tausayin Fatahu ya mamaye ilahirin zuciyarta.

     Ance ko wacce rai na san mai kyauta ta ma za mu iya cewa hakan ya taka rawa wajen sassauta ƙiyayya da takaicin fatahu a zuciyar farida harma ya juya zuwa zallar tausayi shi kansa ya fuskanci akwai wanda take so sai dai yana ji a jikinsa farida tasa ce musanman yanzu da yadena ganin tsanar sa a idanunta face tsabar tausayi yanasa ran wataran zaiga tsabar sansa a idanun ta.

     Yanayin yadda ta rame shi kesa mahaifinta damuwa a kullin gani yake lefinsa ne ji yake kamar ya juya agogo ya dawo da abin da ya wuce dan gyara abubuwa da dama da yake ganin kuskure ya tafka arayuwarsa sai dai kash ya san lokaci baya dawowa in ya wuce.

     Umman Su farida kullin cikin ƙarfafa masa gwiwa take duda kuwa ita ma ɗin tana yin jarimta ne kawai dan kar ta ƙara masa damuwa.

     Yaransu har sun fahinci tabbas akwai da muwa a tattare da iyayan nasu sai dai sun ta allaƙa damuwar tasu da damuwar da jaririyar gidan ke ciki wato farida suna ganin tsabar san da suke mata ya sa damuwar ta suma ta sanya su damuwa.

     Hakan ya sa duk suka mai da hankalinsu gurin farantawa ƙanwar tasu dan suna da tabbacin in tana cikin farin ciki kowa ma zai zamo cikin farin ciki musamman Abbansu da damuwarsa tafi ta ummam tasu bayyana.

    ****

     Fatiha ce zaune suna hira da umman ta yaro ya shigo wai ana kiran Fatiha ta ce jeka ka ce waye bai jima ba ya dawo wai inji faruk ada azatonta yayanta ne Fajar jin wani ne yasata mai da hijabin data ɗauko ta ce ka je ka ce ba ta nan umma ta ce jeka ka ce tana zuwa ta dubi umma fuska da alamun da muwa anman umma..... ba ta bari ta ƙarasa ba ta ce ki je yana jira.

     Umma kinta san abin da zuwa na yake nufi eh na sani anman ba koyaushe ne zuwanki yake nufin abin da ke kike nufi ba ki je in mijin kine kome zaiji duk runtsi sai ya aure ki.

     Rai a tunkushe ta daure ta fita badan taso ba.

     Tsaye yake jikin motarsa sanye yake da shaddarsa ruwan zuma shiga ta hausawa yai, yai kyau sosai dan daman faruk mai kyaune ko wace irin shiga yai kyau take masa, ba fari bane kazalika ba baƙi bane masu kalar fatarsa hausawa ke kira da ruwan tarwaɗa bai da ƙiba kamar yadda bai cika tsayi ba sai dai bazaka taɓa kiransa da ramamme ba gashi da kwarjini hakan ya sanya koda Fatiha ta fito ya mata girma a ido ta kasa sauke kwandon rashin mutuncin da ta ɗebo da niyar juye masa ko ta huta da takai cin da yake shirin jefata.

     Ko kaɗan ba ta wani gane su ba dan ba tsayawa take ta wani kalle shi ba bare tasanma yana zuwa gun sana'ar ta harma yana mata ciniki.

     A hankula ta masa sallama shi ma ɗin a maƙoshi ya amsa kamin ya ce malama fatiha barka da yanma ta amsa a taƙaice barka dai baki gane ni ba ko ta ɗan kalle shi da alamu so take taga ko za ta ganeshi zai dai yadda ya zuba mata ido ya sa ɗauke nata idon gami da faɗin eh to ban waye da kaiba yai murmushi hakane bazaki gane ni ba koda yake ganeni ba shi mati a'alaba.

     Sunana Faruk Nasir mai Gold ta ɗago ta kalle shi dan mutane kaɗan ne a faɗin kano za ka anbaci Nasir mai Gold su gaza sanin sunan ci gaba yai da faɗin zan iya cewa nida ke ba yara bane tun da duk wanda ya shiga jami'a duk ƙanƙantar shekarunsa ana masa kallon me hankali da ya san rayuwa fiye da me shekarun da be karatu ba.

     Hakan ya sanya basai na tsaya kwane kwane ba zaki fahinci na san kinsan da babu abin da kesa namiji ya zo gurin ɗiya mace face neman soyayyar ta to agaskiya nima hakan ya kawoni nazone innemi izinin ki na koban dama in nemi izinin mahaifinki na zuwa gunki dan mu tahinci juna domin ina san family ɗinmu da naku ya zanto guda ta hanyar auratayya.

     Wato inaso nan bada jimawa ba nida ke mu zamto ma'aurata girgiza kai ta shiga yi aure fa kuma wai ni kasan ni kuwa wace yai ɗan murmushi karki damu na san komi akanki saida na bin cike na na tabbatar da ke ɗin me irin tarbiyyar ki nake so Sannan nazo karki damu da abin da ake faɗe ni banma yadda ba kuma kisa aranki bazan taɓa yadda ba ɗabi'unki shi ne mafi a'ala atattare dani all I want is for you to give me chance.

     Shiru tai kafin ta ce chance ta ɗan murmusa alamu murmushin takaici ne koda banda tabo arayuwata ba ni da burin auren me kuɗi na iya talauci na bare ina da tabon da nasam da talaka irina ma bazai auren ba bare me kuɗi dana san da cewar basa auren talaka sedai su ɓatawa yarinya rayuwa daga baya ta ji aurensa da ‘yar uwarsa me kuɗi tun da ko na san da haka kaga bazanwa rayuwata tabo biyu ba.

     Shi ya sa nace kiban dama so that i will prove you wrong ba duk me kuɗi ne yake yadda ke kike tinani pls kiban dama zan tabbatar miki da ko ina akwai na kwarai pls dan Allah kabar ni inji da abin da ke damuna karka kuma zuwa guri ko kana jin zan yadda da daɗin bakinka ko kana jin zan yadda cewar dan kai kayadda iyayanka zasu rufe ido ka auri irina fuuu tai cikin gidansu.

     Iska ya furzar mai zafi gami da naushin iska cike da takaici yaja motar sa yabar ƙofar gidan.

    Farida ce zaune abin duniya ya ishe ta ba komai ke damunta ba face malam Fajarudden da aka saka mata as project guider ɗin ta tun satin da ya wuce ta gani sai dai ta kasa zuwa ko kaɗan ba taso hakan ba dan tayi niyar cireshi aranta hakan ya sa duk abin da zai haɗata da shi ta gujeshi ajima dan ya zama dole ne.

     Ta dena zaman jiran se ta ganshi kwana biyu ta fara jin daɗin rayuwarta duda kuwa daurewa take na cireshi aranta sai dai tana jin kamar za ta iya musamman yadda ta mai da hankalinta fatahu sosai yake ɗebe mata kewa har ta fara jin Wataran za ta iya sansa sai dai haɗa da malam tana jin shi zai ɓata mata lissafi inda adane zatafi kowa farin ciki aƙalla za ta dinga ganin sa kullin sai dai banda yanzu.

     Ala dole ta daure taja ma'u zuwa office ɗin yana waya suka sameshi da Fa'iza suke waya dan yanzu kusan kullun suna manne a waya shigowar su ya sa ya ce I will call you back dear nayi baƙi basu san me ta wayar ta ce ba sundai ga yai murmushi gami da faɗin love u more ma'u tai saurin kallon Farida sai dai yau ta birgeta dan damuwarta ba ta nuna sosai a fuskar ta ba sedai sani ne ma'u batai ba sosai zuciyar farida ke tafasa ji take kamar ƙirjinta zai tsage zuciyar ta ta fito.

     Kallonsu yai bayan ya ajiye wayar lafiya dai ya faɗa ma'u ta ce daman...farida tai saurin cewa daman sir nazo ne kan project ɗina project kuma mene haɗi na da project ɗin ki karo na farko da ya fara ba ta haushi arayuwarta ko dan ta ganshi yana waya da wata ne oho.

     Daman kai aka sa matsayin guider ɗina oh shi ne sai yau zaki zo ina tun satim da ya wuce aka kafe wani haushin ya kuma kamata wato ya san da batun tsaɓar wulaƙanci ya ce bai sani ba satin da ya wuce ne banji daɗi ba shi ya sa banzo ba ya ɗan kalle ta makarantar ce baki zo ba ko kuwa office ɗin sch ɗin ce ban samu nazo ba murmushi yai da gaske bakizo ba anyway ina ji kinada twin sis ko ta kalle shi da mamaki eh dan dai ni naganki wato ma ya sanni har zai iya gane nazo sch kunya ce ta rufeta na ƙarya da tai yai murmushi fahintar hakan ki daina ƙarya kinji ko to kawai ta ce.

     Yawwa zaidai fi yanzu ni me kike san inmiki ranta ya kuna ɓaci mutumin nan ya cika rainin hankali watoma ita za ta faɗi me zai mata in hakame to tai zamanta a gida man tayo abinta.

     Kallonta yai oh mene na jin haushi basai kinzo kina mun kunbure kun bure ba I mean topics zan baki ki ɗauki guda da kike san rubutu akai ko kuwa ke zaki kawon in ɗauki wanda naga yamun ki yi rubutun akai sannan kisan yi in group ko kuwa kekaɗai kike san yi shiru tai tana tunani ya ce ki je inkin gama tunanin kyazo ki faɗan suka fice.

     Suna fita ma'u ta ce gaskiya na tausaya miki bari kawai inji farida ya cika murɗaɗɗen hali in aka haɗa ka da shi an haɗaka da tension farida tai tsaki ni kiban shawara ma'u ta ce ai kawai ki je ki nemo topics masu sauƙi ki kaima ya zaɓa in shi zai baki kinsan muguntarsa duk masu wuya zairubuto kuma dole ki zaɓa haka ne farida ta faɗa.

     Yana zaune yana ɗan dube dube ta shigo ya amsa sallamar ta a'a harkim yanke shawarar eh ta faɗa ok ba sauya ra'ayi koda yake inkinma sauya abin da zance ba tai shiru me kika yanke zan kawo topics in saika zaɓa and ni ɗaya zan yi ok ki nemo topics masu kyau dan bazan karɓi shiri rita ba ya miƙa mata takadda sunane ta gani na wanda zai guiding ɗin da alamu ita ce last zuwa ta cike ta miƙa masa.

     Complimentary card ɗinsa ya miƙa masa in za a kawo chapter se a kirani bana san kira mara anfani ok ta ce tai waje abakin ƙofa taci karo da Fatiha tana ƙoƙarin shiga sannu ta ce da ita yawwa farida ta amsa gami da binta da kallo tabbas da wannan yarinyar ɗazu yake waya tsabar rashin aji shi ne se ta biyo shi office bama shi ya bita ga.

     Guri ta samu ta zauna suka gaisa suka hau hira wanda duk na karatu ne agogo ya duba ina da class ko zaki jirani shiru tai da alamu tunani take ya ce malama ki jira kawai ya miƙo mata takardu ki shigar mun dasu na jima da makawa shigarwa ta gagara inkim gama da wuri ki kirani inzo in basu kayansu ok ta ce yai waje ta bi shi da kallo kafin ta ci mai da hankali kan takardun.

     Tare suka tafi kamar ko yaushe a old campus ya ajiye ta shi kuma yai gida ransa cike fal da tunanin me ya sa ya kasa faɗawa Fatihan game da aurensa ya rasa meke damunsa game da Fatihan sau da dama yakan jita aransa fiye da ma Fa'izan duda kuwa shida kansa ya tabbatar ya kuma yadda yana san Fa'izan sai dai ji yake kamar in ya faɗawa fatiha auren alaƙarsu za ta ja baya batare da ya cinma burinsa na ganin ya temaka wajen rage mata damuwar da kullin yake gani a fuskar ta ba.

     Sai dai baijin zataji daɗi in ya san suna tare yai aure anman ya kasa faɗa mata ya san hakan ma zai iya janyo alaƙarsu ta ja baya tun da zatai zaton be ɗauketa da mahimmanci ba.

     Shi kuwa Faruk abin duniya duk ya isheshi kusan baya sati bezo gidansu fatiha ba saidai baya nasarar samunta wataran kuwa akance tana zuwa in ummanta ta takura sai ta fito sai tai kamar ta fito tai shigewarta gidan yayan babanta setaji ance ya tafi ta koma gida.

     Hakan ya sa faruk yanke shawarar kawai zai samu mahaifin Fatihan ya nemi izini ada niya yai ya sa anema masa aurenta agida saidai kamis ya ce ya fara neman izinin zance insun saba ayi auren acewarsa wataƙil dam kai tsaye gunta ya zo shi ya sa take ganin cutar ta zai yi.

    💞Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Rubutawa

    Faɗima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.