Bismillahir-Rahmanir-Rahim
1. Ya zuljalali karimu Allah rahimi,
Sarkin da yai yi duhun dare yai safiya.
2. Tsira aminci kai ta yi gun É—an Ami-
Natu rabbu É—ai nan a faÉ—in Duniya.
3. Sanyo da alayensa har Asahabu ma,
Har Auliya’u kasa ciki baki É—aya.
4. Baiti na yo domin na yo wani tsokaci,
Kan Intanet hasken da ke game Duniya.
5. Baiwar Hakimu a Duniya yau mun gani
Baiwar da kowa ya gani ba turjiya.
6. Da can dukkan saƙo idan har za mu kai,
Sai mun wuce sanyin dare da na safiya.
7. Kwana saman hanya waÉ—ansu su shekara,
Kafin a kai saƙo zuwa can Indiya.
8. Amma a yau a cikin daƙiƙa an gama,
Ka tura saƙo ko ina nan Duniya.
9. Allah Ta’ala godiya mun yi maka,
Da nufinka ne saƙon ya je Somaliya.
10. Mai son sanin dukkan muhimman lammura,
Wannan na yau ko ko na tun kafin jiya.
11. Tafi intanet ka sam bayani fat É—aya.
Dukkan abin nema akwai ba tankiya.
12. Mai kyau da mai muni ka duba duk akwai,
Na cikin gida Najeriya Afriƙiya.
13. Duk kasuwanci in kana so za ka yi,
Kai intanet tuni ya bazu duk Duniya.
14. Haka na karatu ma akwai shi tuli-tuli,
Harka ta Boko harda ma Islamiya.
15. Wa’azi na dukkan malamai lalle akwai,
Na ƙasar waje har ma gida Najeriya.
16. Digiri É—aya ko ko uku in har ka so,
Ka samu shaida can cikin game Duniya.
17. Dukkan ƙasa mai son ta tattala arziƙi,
Domin ta zamto kan gaba nan Duniya.
18. Sai ta kula da fagen na harkar intamet.
Ta ba shi dukkan nin kulawa kun jiya.
19. Gogul cikinta akwai kuÉ—i in kun biÉ—a,
Haka nan a fasbok na sani ba tankiya.
20. Yutub canal buÉ—e ka nemo mabbiya,
Ka sam kuÉ—in riga dama ‘yar tagiya.
21. IG tiwita dak ciki in ka iya,
Balle su tiktok ma fagen sharholiya.
22. ÆŠauka ka yaÉ—a Duniyar ga ta zam gani,
Tuni ka zamo wani mai kuÉ—i a dare É—aya.
23. Haka tambaɗa sharri da ƙirƙire duk akwai,
Wasu can su cashe can waÉ—ansu ashariya.
24. Ka kula da ‘Yan É—audu fa har ma karuwai,
‘Yan madigo ‘Yan luÉ—u har da masha giya.
25. Birjik akwai su su na ta yawo ko ina,
Yawo suke halinsu sak na Wahainiya.
26. In zamani ya zo da yayi sai mu bi-
Mai kyan ciki sam babu mu ba zilliya.
27. Mu bi zamani daidai da addini kawai,
Kar yaw wuce mu ko muna masa zamiya.
28. Ni dai tuni na fito gari na bi zamani,
Dan yaÉ—a kairi ‘yan uwa kui bibiya.
29. Mota ta shaiÉ—an taka birki kar ka bi,
Domin hakan zai sa ka taɓe Duniya.
30. Saƙon Aminu ka zanka ji ka bi zamani,
Don zamani aka ce Abokin Taffiya.
TAMMAT
Daga alƙalamin
Aminu Sani Uba
(Abu Isah Asshanƙidi)
08162293321
aminusaniuba229@gmail.com
16/satumba/2023
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.