"Tattalin ibada da zumunci
Ya yi masallacin addini,
Ga ladan na ta kiran sallah
Kai nai kaɗai aka tsinkaya
Ka san abin da wuyar koyo
Bisa hasumiya ta masallaci
....
Ban zo ni ba na ji ana ta hwaɗa
Ya yi masallacin da ba awa
Sai ko Masar ko Birnin Sin
Da wurin wanka da na alwalla
Duk ya gina ga masallaci
Wada sunka kwatanta muka ji shi
An ce akwai bargo na Gabas
Mai gyara ƙafa ga masallaci"
An ce wannan shi ne tsohon masallacin Katsina wanda Sarkin Katsina Mahamman Dikko ya gina, wanda kuma makaɗa Salihu Jankidi Rawayya ki waƙe a waɗannan ɗiyan waƙa na sama.
0 Comments
Post your comment or ask a question.