"Shehun gidan Hassan ɗan Mu'azu, Katakoron Matawalle " inji Makaɗa Sa'idu Faru a cikin Waƙar sa ta Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu Malami murabus, Mai Amshi ' Muzakkarin Sarki ɗan Abdu, abun biya Shehu na Ali'. A gefen hagu na wannan hoton Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu ne(ya yi Sarauta daga shekarar 1931 zuwa rasuwar sa a shekarar 1938) tare da Wazirin sa Malam Abbas (ya yi Wazirin Sakkwato daga shekarar 1925 zuwa shekarar 1948) a gefen dama. Allah ya kyauta makwanci, amin.
***
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu ne sanadiyar a ƙirƙiri Bikin Kamun Kifi na Argungu dake Jihar Kebbi ta yau.
Ya kai wata ziyara ce ta yayyafawa gaba/rashin jituwa tsakanin Masarautar Sakkwato da Masarautar Kabi dake Argungu da ta samo asali tun daga yaƙe - yaƙen da aka yi tsakanin masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya da Kabawan Muhammadu Kanta.
Kafin wannan ziyara tasa da yakai a shekarar 1934 a lokacin mulkin Sarkin Kabi Muhammadu Sama(1920-34) Masarautar Sakkwato ta nemi sulhuntawa da Masarautar Kabi ta Argungu har sau huɗu a baya amma abun ya ci tura sai dai a wannan karo da Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu ya kai wannan ziyarar a shekarar 1934 ne lamarin ya samu karɓuwa ga Kabawa har Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu na lokacin, Muhammadu Sama ya shirya masa gagarumin tarbo/biki na nuna al'adun Kabawa a wani gurbi dake Kogin Argungu wanda ake kiran Matan Fada. Daga wannan bikin ne na 1934 aka mayar da hidimar zuwa kasaitaccen bikin da ake gudanarwa a kowace shekara a wannan wuri ya zuwa yau.
0 Comments
Post your comment or ask a question.