Ticker

6/recent/ticker-posts

Rarara Da Rusau... Kantoma!

Idan mai bibiyar adabi da alaƙarsa da siyasa ya biye wa Rarara ba abin da zai faru gare shi sai ya ƙare da tamɓele bisa godabe!

A wannan sahar ta soshiyal midiya, yawancin ayyukan adabi da ke rayuwa da tafiya bisa tsari ba kamar na Dauda Kahutu Rarara. Ba kuma wani abu ke sa shi samun wannan tagomashi ba sai naƙaltar abubuwa da suka haɗa da!

1. Baiwar tsara da fitar da waƙa cikin ƙankanen lokaci.
2. Zaɓar kari mai jan hankali da nusarwa.
3. Bin ƙa'idojin waƙar baka da rubutatta, haɗe a waje guda.
4. Naƙaltar fasahar labartawa da bayyanawa a cikin zubin waƙa.
5. Iya hotantawa da zayyanawa da adon harshe irin na birni da na ƙauye 

Shi ya sa ko ba ka ra'ayin dambarwar siyasarsa ko aƙidarsa ko yadda yake gudanar da lamurransa, a matsayin mutum mai nazari, za a ƙare ne da faɗa irin ta Malam da ya ji zaƙin kiɗa da murya a waƙa, yana cewa, ba dai a ce ba daɗi ba.....!

Malumfashi Ibrahim

Post a Comment

0 Comments