Mu Yi Tunani...

    Ba don  rashin Æ™auna akai shara ba,
    Ba don abinci kawai akai tumbi ba.

    In munka duba duniya tai can gaba,
    Nisan da mai fan kanmu bai hango ba.

    Tafiya da yadda ka hangi saura ke cira,
    Ka bi zamani in zamani bai barka ba.

    Kyan zamani in bai wuce gonarmu ba,
    Ai binsa gunmu ba zai zamo wahala ba.

    Kowa da yadda ya ke shiga cin kasuwa,
    A mutum É—ari ra'ayin su bai zam É—ayya ba.

    Wani ya saya wani zai sayar wani ko kawai-
    Sata ya je don bai taɓin sana'a ba.

    Wani tsaf da shi wani babu ci wani shi kaÉ—ai-
    Ihu ya ke hajar sa don ba ta karɓu ba.

    Wani ko kawai kallo ya je da zubin ido,
    Gun wanda hannayensu ke taɓa riba.

    Mu ma hakan ya kamata mui tsantsar tsari,
    Mu tsare tsaro da cikin idonmu mu duba.

    Mu bi zamani mui lamuni a fasa da mu,
    Mu kasa mu kwasa tabbacin ba a barmu ba.

    Duba da yadda muke zuwa islamiya,
    Ba za ya sa mu mubar shiga harkar ba.

    Sai dai kawai mu guje wa tsa-tsa mai tsiro,
    Mu guje dukan sharrin da bai shafemu ba.

    Wani ya yi batsa yana ganin ya kai ƙura,
    To kai bi tarbiyya ba za ka wahalta ba.

    Wani ya yi zagi ya yi giba yai zuga,
    Wani ya tsaya kan gaskiya bai faÉ—i ba.

    Wani ya yi sokonci da ban-bandariya,
    Wani ko karatu yai hakan bai barshi ba.

    To kun ga ke nan duk abin da ka je da shi,
    Shi za ka yi lamarin ba zai canza ba.

    Allah ka sa mu kwatanta amfani da shi,
    Kan gaskiya da faÉ—inta ba bin gaibu ba.

    Sukari, mazarƙwaila na ke take da shi,
    Ringim a can na ka tashi ko ban faÉ—i ba.

    Maisugar Ringim (رسول الأدب)⁦✍️⁩⁦✍️⁩
    ringimmaisugar@gmail.com
    09123098967

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.