Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Yari Ɗan Bagge
A garin Sububu yake, sunansa Isaka kuma manomi ne sosai
musamman na hatsi, ana ce masa yari ne saboda idan ana aikin gayya shi ke kai
ruwa yana ba masu noma, duk mai yin hakan ana ce masa yari.
G/Waƙa : Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Ku yi
noma da gaskiya,
‘Y/Amshi:
Don Allah ku hwanshi[1]
kanku.
: Riƙa da
gaskiya, noma ba,
: Kashi ya kai ba.Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Ku
yi noma ku baz zama,
‘Y/Amshi: Don Allah ku hwanshi kan
ku.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Yari
irin Amina na Maigujiya,
: Na sha daɗi.
‘Y/Amshi: Gyado mai kashin marake,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari Ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Don Ɗan Bagge nit taho,(x2)
‘Y/Amshi:
Don Ɗan Bagge Za ni wasa.
Jagora:
Bancin ka ɗan Bagge,(x2)
‘Y/Amshi:
Raggo baya shan duman ga .
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari Ɗan Bagge,
: Noma ba ya saka rama.
Jagora : Ba
tun yau ba nij ji labarin,
: Ka tara hatci.
‘Y/Amshi:
Ka tsere ma shakitinbau[2].
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Ku
yi noma da gaskiya,
‘Y/Amshi:
Don Allah mu hwanshi kanmu,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Ku
yi noma ku baz zama,
‘Y/Amshi:
Don Allah mu hwanshi kammu.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya saka rama.
Jagora: In
dai ‘yab Buhari[3]
ce,
‘Y/Amshi:
Kowa ba bari takai ba.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari Ɗan Bagge,
: Noma ba yasa ka rama.
Jagora:
Yunwa ‘yar Buhari ce,
‘Y/Amshi: Kowa ba bari takai ba.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Yunwa ta taho da gorori[4],
: Ta iske maza,duk ƙaton,
: Da taƙ ƙuma ga wuya sai,
: Ya shantala,
‘Y/Amshi:
Sai ya hurce Kwantagora.
: Riƙa da
gaskiya.
: Noman ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Sannan ta waiwayo,
‘Y/Amshi:
Ta ga ƙaton da bai ɗaga ba,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: In tak ƙumai bugu,
‘Y/Amshi: Sai
ya kai gabas ga Barno.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Kuma sai ta waiwayo,
‘Y/Amshi: Ta ga ƙaton ta ba ɗaga ba,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : In
taƙ ƙirai[5]
bugu,
‘Y/Amshi: Wajjen Yamma za ya dosa.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Ga
hwa gudun muna ta yi,
‘Y/Amshi: Amma ba a yi Arewa.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Han
na Arewa sun biyo hanya,
: Sun ɓata ƙasa,
‘Y/Amshi:
Sai shayi sukai na gaske,
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Ni
dai ban san na gaske ba.
‘Y/Amshi:
Sai na sa dawo ga baki.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba.
: Yaro ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Ko wacce na gaske ne,
‘Y/Amshi: In dai ba dawo ba ƙyale.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Kwacce mai koko ta sayar,
‘Y/Amshi: Ta bam mai nagaske zanne,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Masu
biredi sun sayar,
‘ Y/Amshi:
Sun bar mai nagaske zanne.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Kuma an taho da tsaba[6],
: Na iske an sayat,
‘Y/Amshi:
Dud dai mai na gaske na nan,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Hashimu ya taho da rogo,
: Na iske ya shigat,
‘Y/Amshi:
Dud dai mai na gaske na nan.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Ko
‘Yattama da adda haki,
: Na ga ta sayar,
‘Y/Amshi:
Ta bam mai na gaske zanne,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora: Malan abdu ya sayar,
‘Y/Amshi:
Yabar mai na gaske zamne.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Ku ji mai yamri[7]
ta sayar,
‘Y/Amshi: Ta bar mai na gaske zamne,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya saka rama.
Jagora:
Kuma Dela uwat tuwo,
: Kuma mun iske ta sayas,
‘Y/Amshi: Ta bam mai gaske zamne,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Hassi ta Amali ta bugo hwanke[8],
: Na ga ta sayas,
‘Y/Amshi: Ta bar mai na gaske zamne,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya saka rama,
Jagora:
To ƙarya ba na gaske ne ba, x2
‘Y/Amshi: : To ƙarya ba na
gaske ne ba,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Shi ya ce na gaske ne,
‘Y/Amshi: : Kuma dai ya ƙi sha ya ƙoshi,
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Rani wanga ya yi rani,(x2)
: Ya sa maza lage,
: Tahiya wagga ta yi nisa,
: Ta sa maza gaba,
: Yunwa wagga ta yi yunwa,
: Ta bada arkane[9],
: Ga mata da ‘yan ɗiya,
: Ka ji ƙatonta ya
yi lalata, ya bata wuri,
‘Y/Amshi: Ya tsere yana ta kainai.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka ka rama.
Jagora:
In dai macce hat tana da ɗiya,
‘Y/Amshi: Ta hi maigida,
: Sai in ranta bai gashe[10]
ba,
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
In ranta yai baƙi,
‘Y/Amshi: Ko yaƙi tana
iyawa,
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
Yunwa ta ci Adarawa[11],
: Sun yo ga Gobirawa,
: Sun iske Zamfarawa,
: Sun zan mutun guda,
Y/Amshi:
Kowa ba ka jin ba’a tai.
Jagora:
Sada ina ba’a[12]
takai,
‘Y/Amshi: Ƙato bai ci yar raga ba.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama,
Jagora:
Garba ina batun ba’a,
‘Y/Amshi: Ƙato bai ci ya raga ba,
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora:
In ɗan dandi[13]
tay yi mai daɗi,
: Ba ya son gida,
: Amma ko da ta yi mai ƙono,
: Sai ya lissahwa,
‘Y/Amshi: Ka ji ya ce gida ni kai,
: An ce baba na kira na.
: Riƙa da
gaskiya,
: Noma ba kashi
yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa
ka rama.
Jagora : Yunwa ta game da ‘yan ƙyare,
: Za su unguwa, tac ce ina nuhwa,
: Sun ce za mu unguwa,
: Tac ce bari in baku shawara,
: Ku yi wajen gida ku nemi,
: Abincin da ku ka ci,
: In ko kun ƙi shawarata,
: Wahala ta na gaba,
: Sai kun kwana ba abinci,
: Kun tashi ba-,
: Kun ci tuwon da
ba miya,
: Sannan sai
gudansu,
: Yan noce,yay yi
lissahi[14],
‘Y/Amshi: Yac ce gida nikai,
: Ko aikin marece
in tai.
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi
yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa
ka rama.
[1] Fansa.
[2] Raggo: wanda ba
ya iya aikin noma.
[3] Yunwa.
[4] Abin bugu
[5] Buga masa da ƙarfi.
[6] Dawa.
[7] Dawo wanda aka kirɓa ba a sa ruwa ba, aka sa man
shanu ana sayarwa. Fulani suke yinsa.
[8] Fanke
[9] Wahala
[10] Ɓacin rai mai tsanani
[11] Mutanen Adar.
[12] Zolaya
[13] Yawon bariki
[14] Tunani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.