Ticker

6/recent/ticker-posts

ALLAH MAI TAIMAKON MUTUM BABU SANINAI

AMSHI

Allah mai taimakon mutum babu saninai.

AMSHI

Ya tabaraka maisheni yamma inbaje koli na.

AMSHI

Mai sama Allah maisheni yamma inbaje kolina.

AMSHI

Allah maisheni yamma inbaje koli na.

AMSHI

Kuntugi, Molo kuntugi harda su goge, tuna molo kuntugi har da su goge, mai kotso da masu taushi sun hangan mai molo yaganeni ya aje gunkinsa.

AMSHI

Sannu garnakakin maza, mijin bilki na yalwa mammalo mai waka kanen idi dodo na yalwa.

AMSHI

Ya tabaraka ke agazar mutum babu saninsa.

AMSHI

Da sai ankokowa akan kwana da mace yanzu da wani bai kada tashi sai ankamamai.

AMSHI

Kaga andafa kifi gidanmu kan aka mikaman, yanzu kan kihi ni nike taci ba karhwa ba.

AMSHI

Masu kuntugi sunkace dani lawai dogon zance, nace um um bahakan bane dogon zance, irin dogon zance lawai inya dauki wanga saiya sauya shi.

AMSHI

Nayi tsalle, nakara tsalle na 6arje gumina ya tabaraka mai sheni yamma in6arje gumi na.

AMSHI

Ya tabaraka ke taimakon mutum babu sani nai,Jallah inyayi nuhin shi babu wani mai juya mai.

AMSHI

Duna na bilki mammalo Shatan yalwa, yan solo sunganeni sun aje solonsu, yan kwafta sunganeni sun aje kwafta, Masu molo ma sungane ni sun aje molo, kai masu goge insun gane ni sai lale lale.

Rubutawa:

@DANKARSHE✍🏽

Hussaini dogo
Sarkin Yaki

Post a Comment

0 Comments