Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Baƙar Rama

Allah sarki bakar rama 

Ta yar Nasara mai yawa maniyi sannu da rana Tasalla!! 


Wadansu mutane suna fadin 

Bakar rama ko ba mutum ba ce 

Nace masu aa kubar fadi 

Bakar Rama Amma mutum take 


Wai sai suka ce min 

Haru Uji!! 

Bakar rama Indai mutum take 

Sai kai mana tadin bakar rama 

Sai ku matso zan gaya muku 

Na farko zancen Bakar rama 


Mai son yan nan bakar rama 

Ya kan shiga kogo kamar guza 

Kamar gansheka ya ja ciki 

Ta ce bata so ba zata ba 


Ya hau kan rimi!! 

Sai ya kere Rimi

Ya fadi da kirji Bakar Rama 

Tace bata so ba zata ba


Sai ya samu giginya 

Ya hau giginya da baya 

Bakar rama tace bata so ba zata ba ......


In ya hada wannan 

Ya zauna 

Ya yi mata kukan wata bakawai 

Da kwana hamsin!!! 

Sai ta ce ba ta so ba za ta va 

Allah sarki bakar rama 


Allah ya jikan Uji mai dandan!!


Credit: Fatuhu Mustapha 17/08/16

Post a Comment

0 Comments