Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruwan Ƙauye - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Ruwan Ƙauye 

Masu Cafewa: Ruwan ƙauye,

 Ruwan ƙauye.

Mai Direwa: Jagwalgwale ne.

 

Masu Cafewa: A wanki kare a wanki doki,

Mai Direwa: A ɗauko ɗan mutum a jefa.

 

Masu Cafewa: Yarinya bak ki da yayu ne?

Mai Direwa: Yayuna sun fi ɗari goma.

 

Masu Cafewa: Iya lissafa mu ji labari,

Mai Direwa: Ramlatu,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Khalid,

Masu Cafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Halima,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Abdul,

Masu Cafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Ni ma na iya aikin bariki, bariki balle aikin Jos.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments