Wannan wani ɗan Waƙa ne daga cikin Waƙar da Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ya yi wa Marigayi Mai girma Uban Ƙasar /Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammadu Asha wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1960 zuwa rasuwar shi a shekarar 2004. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Wannan Waƙar ta na cikin Waƙoƙinsa da ya yi wa Marigayi Mai Girma Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammadu Asha a farko farkon hawan mulkinsa a cikin 1960s, saboda maganganun da ke cikin ta suna nuna a lokacin Siyasar Jamhuriya ta biyu ta zafi sosai musamman tsakanin mabiya/magoya bayan Jam'iyyar NPC mai mulkin Lardin Arewa/Tarayyar Nijeriya da babbar abokiyar adawarta a Lardin Arewa ta NEPU/NEHU.
Kasancewar Jam'iyyar NPC /Salama ana ganin ta masu iko /mulki da manyan mutane musamman masu arziki ko attajirai ce kasancewar ta ƙumshe da Jagororin irin su Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello GCON KBE. A bangaren NEPU /NEHU /Sawaba kuma tafi zama ɗauke da Malamai/Almajirai na Addinin Musulunci da musamman masu ra'ayin Ɗarik'ar Tijjaniya ko Ƙadiriya ganin cewa Jagoranta Malam Aminu Kano na da wannan ra'ayin da kuma 'yan bokon dake faɗa ko yaƙi da Sarauta da Sarakuna.
Kasancewar Ƙaura Namoda cibiya ce ta ilmi tun lokacin Jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya (domin masu Jihadin sun yi zaman Ribaɗi anan) sai kuma aka samu zaman Ɗarik'ar Tijjaniya da Ƙadiriya sosai a wannan gari duba da yadda manya-manyan Malamai da Almajiran da suka dinga baro garuruwan su zuwa Ƙaura Namoda da zama, cikin su kuwa har da wani shahararren malami daga Birnin Magaji da ake kira Malam Muhammadu Na Birnin Magaji wanda ya samar da wata babbar Zawuyya da ta haifar da Halifofi biyu bayan rasuwarsa, watau Halifa Malam Sani na Malam Babba da mai bi masa, Halifa Malam Mai Suna (Atiku) na Malam Babba. Akwai Zawuyyar Malam Shehun Ƙaya da ya fito daga Ƙasar Maradun da kuma Zawuyyar Ƙadiriya dake Shiyar/Unguwar Kambarawa Ƙaura Namoda.
Haɗuwar waɗan nan jagorori na addini da na mulki ya sanya an yi ta samun tashin tashina na rikicin siyasar da ya sanya Masarauta da masu sarauta sun yi ta ƙoƙarin kariyar kansu daga hushin gwamnatin NPC ta hanyar ƙoƙarin murk'ushe irin wannan adawar ta 'yayan Jam'iyyar NEPU /NEHU na yankin wadda saboda adawa ta cikin gidan sarauta har da wasu 'yayan Sarki ko masu alaƙa da sarautar ke mara mata baya.
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.