Ticker

6/recent/ticker-posts

Cutar Sefa Gaskiya Ce: Tabbas Cuta Ce Mai Matuƙar Illa Ga Dabbobi Da Mutane

Cutar sefa tana jawo mutuwar dabbobi da mutane. Nau’in dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haƊa da; Shanu, Tumaki, Awaki, RaƘumai, Aladu da Dawaki.

ALAMOMIN CUTAR SEFA A DABBOBI

• Mutuwa lokaci guda

• Tabo mai kama da Ƙurji

•Zazzaɓi mai zafi

• Rashin kuzari

• Zawayi mai ɗauke da jini

• Fitar jini daga kafofin jiki kamar su kunne, ido, hanci, baki, da duburar dabba

Jinin da ya fito daga jikin dabbar da take ɗauke da cutar sefa ba ya bushewa.

ALAMOMIN CUTAR SEFA A MUTANE

• Tabo maikama da cizon ƙwaro

• Murɗa

• Amai

• Ciwon ciki/damƙar ciki

• Zawayi mai ɗauke da jini

• Tari da jini

Wahalar nunfashi da sauransu

ABIN DA AKE BUƘATA MUTUM YA AIWATAR IDAN YANA ZARGIN DABBA TANA ƊAUKE DA CUTAR SEFA

Ƙaurace wa dabba wanda ba ta da lafiya ko dabbar da ba a san me ya kashe ta ba

• Hanzartawa wajen sanar da rashin lafiyar dabba ko mutuwarta wa likitan dabbobi ko asibitin dabbobi

• Kada a ci dabbar da ba a san me ya kashe ta ba.

• Duk dabbar da ta mutu ya kasance an binne ta bisa ƙa’ida yadda shari’a ta tanadar.

• Rigakafi wa dabbobi domin hana yaɗuwar cutar

Cutar Sefa Gaskiya Ce; Tabbas Cuta Ce Mai Matuƙar Illa Ga Dabbobi Da Mutane

Post a Comment

0 Comments