Ticker

6/recent/ticker-posts

Bari Kuka Sa’idu

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Bari Kuka Sa’idu

Yi shiru bari kuka Sa’idu,

Me kake wa kuka Sai’du?

 

Mai kuɗɗi Sa’idu,

Ku taho ku gane shi,

Ku yo ziyara.

 

Ɗan yaro ya buwaya,

Ɗan yaro sai dai a bi ka,

Amma ba ka bi su ba.

 

Ɗan Malammai Sa’idu,

Ɗan Alƙalai Sa’idu,

Gidanku an yi gadon karatu.

 

Ga kuma kuɗɗi barkatai,

Kuma ga shi kun gaji hanƙuri.

Kai yi shiru ɗan yaro Sa’idu,

Yi shiru bari kuka Sa’idu.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments