Ticker

6/recent/ticker-posts

Mamin Jatau

6.80 Mamin Jatau 

Wannan wasa ne da ake aiwatarwa tsakanin mutane biyu zuwa sama da haka. Mutane biyu ne suke gudanar da wasan a lokaci guda. Saboda haka, idan ya kasance yara da yawa ne suka taru domin wasan, za su riƙa yi ta bibbiyu. Yayin da ɗaya ta faɗi, sai wata ta karɓe ta.

6.80.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Wannan wasa ba shi da takamaiman lokacin da ake gudanar da shi. Akan yi wasan a dandali ko makarantun boko ko kuma wuraren da yara ke taruwa.

ii. Babu wani takamaiman lokacin da ake gudanar da wannan wasa. Akan yi shi da hantsi ko da yamma ko ma da dare.

6.80.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya su fuskanci juna. Daga nan za su riƙa tafa hannuwansu cikin salo-salo. Yayin da suka tafa da juna, sai kuma su yi tafi (wato yarinya za ta yi tafi sannan ta kai hannu su tafa da ‘yaruwarta). Salon tafin da yara ke yi sun bambanta daga wuri zuwa wuri. Yara kan yi waƙa yayin da suke gudanar da wannan wasa. Ga waƙar kamar haka:

Mamin jatau mi,

Tashin wulbairo,

Bairo-bairo mi,

Ai liki-liki laila,

Wulbari laila,

Tashina laila,

Tashin makaranta laila.

 

Is ma e gud e gud e gud ala conturol,

Mamanta‘yar banza,

Ta sace min nera.

 

Babata ta ce,

In ta je mak-mak-mak,

In ta je Makka,

Za ta sayo yoyo,

Za ta sayo min,

Ɗankwalin dis-dis-dis,

Ɗankwalin disko.

6.80.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara, sannan yana samar da nishaɗi gare su. Baya ga haka, wasan na koyar da ƙwarewa wurin amfani da hannu ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments