Ticker

6/recent/ticker-posts

6.2 Allah Mun Tuba - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 133)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

6.2 Allah Mun Tuba

Wannan ma waƙar roƙon ruwa ce. Akan rera ta ne yayin da aka samu fari ko rashin saukar ruwan sama da wuri. Yara maza da mata da manyan mata da tsofaffi duk suna rera wannan waƙa. Ga yadda waƙar take kamar haka:

Bayarwa: Allah mun tuba,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Ya Allah ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Gero a dawa ya bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Masara a dawa ta bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Maiwa a dawa ta bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Wake a dawa ya bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Allah ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Allah mun tuba,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Ba mu sake zagin ɗan kowa,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Ba mu sake dukan ɗan kowa,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Ba mu cin amanar ɗan kowa,

Amshi: Allah mun tuba.

 

Bayarwa: Allah mun tuba,

Amshi: Allah mun tuba.

Haƙiƙa wannan waƙa tana ɗauke da wani muhimmin saƙo. Wannan kuwa shi ne ra’ayin Bahaushe kan cewa, munanan halayya da ɗabi’u na kawo fitintinu tsakanin al’umma. Daga cikin irin waɗannan fitintinu ko jarabawowi akwai rashin ruwan sama. Saboda haka ne a cikin waƙar ake kawo zancen tuba daga wasu miyagun halaye kamar su zage-zage, da cin zali (duka) da kuma cin amana. Sannan waƙar na ɗauke da jerin sunayen amfanin gona, kamar yadda akan same su a gonar Bahaushe. Wannan ya kasance tamkar wani kundin killace sunayen amfanin gonar Bahaushe. Kuma makaranta ce ga yara wurin koyar waɗannan kalmomi.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments