Duk namijin da ya tsotsi nonon matarsa har ruwa ya fito yasha wannan ruwan nonon, ko tana shayarwa ko ba ta shayarwa tananan a matsayin matarsa.
A indai aure yake haramta a tsakani shi ne,
idan mace ɗaya ta shayar da shi yana jariri a lokacin daba ya buƙatar wani
abinci sai nono,ba ya iya cin komai sai nono, to idan ya zama matar data shayar
da shi ita ce ta shayar da matarsa, to anan aure ya haramta a tsakaninsu.
Amma mutuƙar ya girma yana cin abinci, yana
yin komai da kansa, yana yawo a gari, to anan duk nonon matar da yasha a wannan
hali '‘yarta ta halatta ya aure ta, amma indai yana jariri ne ta shayar dashi,
to anan ne take haramta a gareshi.
Don haka duk wanda yake kan fahimtar cewa ai
idan miji yasha ruwan nonon matarsa babu aure a tsakaninsu, wannan ba gaskiya
ba ne.
ALLAH TA'ALAH kasa mudace.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu
baki ɗayanmu Ameen.
ZAN IYA SHAN NONON MATATA
TAMBAYA (182)❓
Assalamualaikum Warahmatullahi wabarakatuhu brk da Rana malam ya qokari
Allah ya kara nisan kwana dan Allah tambaya ta itace idan mace na shayar da
yaro shin ya halata mijinta ya sha nonota Amma idan nono ya wadatu yaron ngd
Amma dan Allah kar ace nayi rashin kaunya
AMSA❗
Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu
A cikin neman ilimi ai Kunya a gefe ake adanata, Kin manta da Abinda
Nana Aisha (Radiyallahu anha) take cewa: "Madallah da matan Madina wadanda
kunya bata Hana su tambaya akan addininsu"
(Sahihul Bukhari)
An tambayi Committee Fataawa al-Lajnah ad-Da'imah a gameda hukuncin
Miki ya Sha Nonon matar sa, suka ce:
"Ya halatta miji ya ji dadin jikin Matarsa saidai inda yake
Haramun shine saduwa ta dubura, da Kuma lokacin da take jinin al'adah da jinin
haihuwa ko yayin Ihrami (Hajji ko Umrah) har sai ta fita daga Ihramin gaba
daya"
(Shaykh ‘Abd al-‘Aziz ibn Baz, Shaykh ‘Abd-Allah ibn Qa’ud, Fatawa
al-Lajnah al-Daimah, 19/351, 352)
"Haka kuma ya halatta miji ya tsotsi Nonon matarsa Kuma ko da
yasha Nonon to hakan bazai sa ya zama
mahram ba"
(Shaykh ‘Abd al-‘Aziz ibn Baz, Shaykh ‘Abd al-Razzaq ‘Afifi, Shaykh
‘Abd-Allah al-Ghadyyan, Shaykh ‘Abd-Allah ibn Qa’ud)
Shaykh Muhammad ibn Salih al-‘Uthaymin yace: "Idan babba ya Sha
Nonon hakan bazai sa ya zama Mahram ba saboda wannan hukuncin yana faruwane a
shekaru 5 ko Kuma shekaru 2 na farko kafin a yaye jariri. A qarqashin haka baza
ayi la'akarida mijin da yasha Nonon Matarsa a matsayin Dan ta ba"
(Fatawa Islamiyyah, 3/338)
A taqaice jamhurun malamai sunce ya halatta miji ya sha Nonon matarsa
duk da dai ba'a so hakan ba la'akarida ai Nonon mace abincin jaririn ta ne
bawai na Mijinta ba
A shawarce me zai hana yaje ya siyo Yoghurt ya sha ya qoshi, yabarwa
jaririn abin shan sa, kinga anan kowa ya sha rabon sa kenan. A gani na hakan
shine yafi adalci
Lactic acid (Nono) na Jarirai ne, Yoghurt Kuma na manya ne. Duk da dai
shan sa ba Haramun bane amman kowanne abu da muhallinsa. Ajiye qwarya a
gurbinta shine yafi dacewa
Muna muku tallar sabuwar makaranta Online mai suna: "MU'AMALAR
AURATAYYA A MUSULUNCI". Wanda yake da ra'ayin shiga yayi magana ta Private
hukumar makaranta zata turo masa tsare - tsare da dokokin shiga
(WhatsApp: 07035387476)
Wallahu taala aalam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.