Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarar Baki

  Suna hanyar dawowa daga taron iyaye da makaranta ta tsara sai 'ya ta ce wa uwarta mama duk ƙawayena cewa suka rinƙa yi mamana tana da kyau sosai. Ta yi wuf ta tari bakinta ta ce ba yanzu za ki bada labari ba. Ki bari sai mun je gaban babanki.

Bayan sun iso gida, cikin murmushi ta ce da ƴarta faɗa wa babanki abun da ƙawayenki suka faɗa miki.

Yarinya ta ce: "cewa suka yi mamana tana da kyau sosai saidai kash tanada manyan kunnuwa kamar gurasa, kuma kwalliyanta irin naa mutanen ƙauye ne. Ga ta gajeriya, jagira da jan baki da ta sa kamar wata aljana". 

Tarar Baki

Post a Comment

0 Comments