Ticker

6/recent/ticker-posts

Nijeriya Ƙasarmu Ta Gado

  1_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da ake ƙiran miji da baby jariri kuma a ƙira shi daddy 🙄


2_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da biki dole sai ranar Asabar ko ranar Lahadi 🙄


3_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da take bawa wasu ƙasashe tallafin wutar lantarki yayinda ita kuma ta kasa tsayar da wutar a ƙasarta 🙄


4_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da makullan mota da wayar iPhone ba a saka su a aljihu saboda burga 🙄


5_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da cikin sauƙi da kwanciyar Hankali ake tara dubunnan Naira domin zaman makokinka amma ba za a taba baka jari ba lokacin da kake a raye 🙄


6_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da kana buɗe firji maimakon ka ga tarin ababen sha da na tanɗe tande saidai ka ga tarin zogale da yakuwa 🙄


7_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da za ka siyo kare sannan ka sanya masa suna tiger 🙄


8_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da mai aure za ka ji yana faɗin budurwarsa na cin amanarsa 🙄


9_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da ƴan damfara suke da gobe mai kyau fiye da wanda ya kammala karatu 🙄


10_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da masu aski suke manna hoton askin da ba zasu iya irinsa ba 🙄


11_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da magani ɗaya yake warkar da cututtuka sama da hamsin🙄


12_ Barka da zuwa Nigeria ƙasar da matasa suke rina gashinsu zuwa fari tsoffi kuma su rina nasu zuwa baƙi 🙄

NIGERIA KASARMU TA GADO

Post a Comment

0 Comments